Sashe 91
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
adamcy ? me yasa zaka bata kasuwancinmu maganar gsky muddin haka zaa cigaba da tafiyar da kamfanin gara kowa ya watse a rufe kamfani kowa ya kama gabansa "okay wannan shine daman shirina ai a rufe kowa ya kama gabansa "Ibrahim da fahad suka kallesa a rude suna mai mamakin jin abinda ya fad'a " yes haka nake so "okay saboda kasan kana da wasu compaines masu zaman kanka shiyasa kake son a rufe wannan ?"yayi kyau yayi kyau gara daka fad'a mana muka sani ."ai daman mugunta ne acikin cikin wannan mugun mai girman kan , kai ne dai ka kasa ganewa kake daukarsa amatsayin mutumin kirki ai ga irinta nan zai janyo kowa ya rasa saboda tsabar bakinciki irin nasa da dai a rufe gara a siyar a bawa kowa hakinsa "inji cewar fahad . Dan allah fahad ka samu natsuwa kai ma Ibrahim ka natsu kar wannan abu ya zama damuwa " karki damu mami wani abu bane ai bazamu biye masa ba zanyi komai domin naga business din ya tsaya da kafafunsa "ko kuma a siyar ba nifa gara a siyar dashi inji cewar fahad "wannan kuma karya ka fad'a dan matsawar ina raye babu wanda ya isa ya siyar da AGC "mu zuba mu da kai dan halak ka fasa yadda kake ji da taurin kai muma muna ji dashi a qarshe zan maka gargadi ka rage wannan zakewar da jijji da kai idan ba haka ba wallahi zaka rasa rayuwarka a banza kuma babu abinda zaayi "yana gama fad'ar haka ya juya fuuuuu ya fice har zai bi bayansa mami ta sha gabansa da sauri tare da ware hannuwanta karka kuskura kabi bayansa ,kana jin mutun yana ikirarin zai kasheka ya kashe banza shine zaka bi bayansa sweetheart ki barni babu abinda zai iya yi wallahi bazan barka ba idan kai baka son rayuwarka ni ina da buqatar ka a raye ,oya koma can ka tsaya ko ka wuce d akinka, tsayawa ya kasa furta komai yana cin ransa . yaya Ibrahim yace" idan har baka bari an sauko da komai ba ina tabbatar maka gobe goben nan zan bar aiki a kamfanin ."so what idan ka bar aiki ? ya kallosa a fusace yana huci ,ka sani ni kasuwancina ba kamar na kowa bane kuma nasan kan business dina kuma babu wanda ya isa acikinku ya janye daga hukuncina "enough adam ya fad'a a tsawa ce shima tmkr zai maresa shima AD yayi kusa dashi sosai yana zaro masa idanuwanshi da suka gama canza kala tsabar bacin rai "ka sausauta muryarka akaina Ibrahim " idan ba haka ba me zakayi ? "Zan... zan canza maka kamani yanzu ya fad'a yana huci kamar zaki .shima sai da mami ta shiga tsakaninsu "wallahi adam ka raina ne kana magana dani kamr bakasan tazzrar dake tsakaninmu ba, kai duk abinda yazo bakinka kake fad'awa mutane da wadan da suka girme maka da saaninka "adam ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa yana hura masa hancin "dan allah ku daina fad'a akan dan wannan matsalar duk ku kwantar da hankalinku komai zai daidaita kai adamcy wuce d'aki . naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana furzar da iska acikinsa sannan yayi wani juyi ya hau step da sauri sauri yake taka step yana cewa "babu wanda ya isa ya canza tsarina shi kuma wancan d'an iskan zai gane kurensa har ni zai yiwa barazana da mutuwa ? bayansa suka bi da kallo har da suka daina hangosa sannan yaya Ibrahim ya kalli mami "dan allah mami kiyi masa magana nasan ke kadai zaki fad'a masa yaji mutane bila adadin ne suka dogara da wannan kamfanin me yasa zai yi qari ? ban san me yasa zuciyar adam bata da tausayi ba wallahi idan bai sauke raayinsa ba akan wannan matsalar am sorry to say mami zamu samu babbar matsala dashi ." Mami ta riko hannusa ta qarasa dashi kan kujera ta zaunar dashi taje ta dibo ruwa mai sanyi a glas cup ta dawo ta mika masa " sha ruwa Ibrahim ka samu natsuwa " bai yi mata mutsu ba dan yana bukatar ruwan ya karba ya sha kadan ya mika mata cup yana sauke numfashi "kayi hakuri kaji ibrahim ka bar komai a hannuna kamar yadda kace maganata kawai yake ji ,zai ji da izinin allah duk yadda kuke so zaayi ya sauke numfashi yana cewa "na gode sosai mami allah saka miki da alkhairi dan allah kiyi kokari ki sauko da adam nasan yayi haka ne da wata manufa amman ya duba mutane dake amfana da ma'aikatan ba wadan da suka bata masa rai ba in sha allahu zai ji kuma zaka ga canji " allah yasa ya fad'a tare da mikewa rusunawa yayi mata sallama ." tsaye yake a d'akinsa yana faman zariya yana cika yana batsewa "har ni fahad zai wa barazana da mutuwa ?daga yanzu bazan cigaba da daukar wulakancinsu ba a hankali yake magana yana balbale botiran gaban rigarsa ya cilla rigar a saman gado ya saki numfashi da karfi tare da kwance agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yayi taku biyu ya ajiye a inda ya saba ajiyewa.jkinsa na tsuma ya tsura wa mirrow idanunshi yana kallon kansa gabadaya sai yake jin rashin dadin abinda yayi sam sam bai kyauta ba kuma ya tabbatar da maganar Ibrahim gaskiya ne mutanen da zasu shiga damuwa idan mummunar abu ya samu da kanfani suna dayawa amman bazai ta'ba daga wa kowa kafa ba ya furta a fili yana jan tsaki ya juyo ya fad'a kan katifa " Mami ta hada abinci a qaramin tire kamar yadda ta saba dan abinci idan ba daga hannunta bane baya ci saboda tsoro abinda zai cutar da rayuwarsa a natse ta nufi kofar parlour'nsa ta wuce bedroom dinsa ta shiga yana kwance flat akan gado ya daura hannuwansa duka faffadan qirjinsa ." Ta ajiye tiren abincin akan wani qaramin table wanda daman dan cin abinci aka tanadeshi ya mike a hankali daga kwanciyar da yayi ya zauna ya hade hannunwansa wuri daya bata tace masa komai ba kamar yadda shima bai ce mata komai ba ta dauki plet da spoon din abinci data shigo dashi ta kai bakinsa ahankali ya dinga amsa yana ci har sai data fahimci ya koshi ta ajiye sauran ta sakar masa murmushin farinciki tare da kamo hannunsa cikin nata kafin tayi magana ya motsa labbansa ahankali "na gode sosai sweetheart allah ya bar min ke "ameen adamcy nah kai ma allah ya bar min kai bata nemi tayi masa mgn akan lamarinsa dasu Ibrahim ba ta barshi har ya dan sauko hira ta soma janshi ."Ahankali ahankali ya dinga biye mata suka shiga hira ta tsakanin uwa da d'a a qarshe ta shigo masa da maganar . ka zama mai hakuri da yanuwanka adamcy dan baka da kamarsu sannan ka zama mai tausayi domin kai ma kana buqatar tausayawar ubangijinka , akwai mutanen da kamfaninku suke ci suke sha suke komai na rayuwarsu ka duba allah da ire iren su ka sauko da komai sai kayi tawassali da aikin alkhairin da kayi ka roki Allah wata buqata kaga yadda Allah bazai maka ba babu abinda nake buqata sweetheart kamar mafarkina ina tsananin son kasancewa daita ya fad a acikin ransa. mami ta dade tare dashi har sai data ga bacci na qoqarin daukarsa sannan ta barshi ta shafa sumar kansa. tana tsananin son danta bata qaunar abinda zai kawo masa damuwa arayuwarsa yanzu shiyasa ma tayi qoqarin danne damuwarta akan matsalarsa da maryam tunda yace bai so ta hakura har abada Allah ya raya abinda zasu samu blanket ta janyo ta lullube masa rabin jikinsa ta fito daga dakin ." bacci mai dadi ata yake yana rungume da hannunwansa cikin baccinsa ya fara mafarkinsa wanda a qalla ya kusan wata uku bai yi ba koma yace fiyye da haka ,yarinyar daya saba gani ita ya gani sai dai wannan karon cikin mawuyacin hali ya ganta acikin wani kungurmin daji gashin kanta duk ya hargitse ya zubo gadon bayanta tana gudu tana ihun kiran sunansa da iyakacin karfinta cikin haka wasu mutune guda uku maza suka biyota tana gudu suna binta har sai dai ta bace masu amman ita bata daina gudu acikin dajin ba juya ne ya soma dibanta kanta ya soma juyawa tana kokarin zubewa kasa sai gashi ya qaraso gareta ya tarota da hannuwansa duka sukai zube kasa tare ." lumtsatsun idanunshi ya tsura mata yana kallonta yana kiranta da sunan da yake kiranta dashi dan tuni numfashinta ya dauke ganin halin da take ciki yasa hankalinsa yayi mugun tashi ya kamo hannunta yana murza tafin hannunta cikin sauri amman still bata tashi ba hakan yasa ya hade bakinsu waje d aya ya fara tsotsa yana sake hade hannuwansu ya cigaba da murzawa ." Yana shan bakinta hankalinsa na tashi dan jijiyarsa tuni ya tashi, ahankali numfashi ta ya dawo ta soma bude idanunta har ta budesu akanshi still bakinsu na hade ya kasa cire bakinsa cikin nata ,hannuta ta kai ta shafa gashin dake kwance a fuskarsa wanda hakan yasa ya zare bakinsa a nata yana dubanta .ahankali idanunshi suka sauka akan tudun brest dinta nan take yaji shaawarta ta kamashi ya rungumeta ajikinsa tsam ajikinsa yana shafa bayanta naunayen ajiyar zuciya ya sauke Jin yadda jikinta ya dauki zafi gbdy jikinta yayi sanyi ya sake "su waye wadan nan mutanen dake binki ?shiru tayi babu amsa "me kika yi masu suke binki ?shima shiru tayi masa ya zareta ajikinsa ya tsura mata ido ina ne gidanku ?sai lokacin ta motsa jikinta ta nuna masa wani doguwar hanya ya mike daita rungume ajikinsa da hannunta ta dinga nuna masa hanya har suka qaraso wani gida mai get kai tsaye suka shiga da gudu yaga wata mata tayo kansu tana kuka , tasa hannu ta karbeta a hannunsa ta kwantar daita ajikinta yana qoqarin bude bakinsa yaji "allahu akbar !! Kiran sallahr daaka kwalla daga masalacin gidansu ne ya farkar dashi agigice ya mike ya zauna a tsakiyar gadonsa gbdy zufa ne ke tsiyaya ajikinsa gabansa sai faman bugawa yake ,jijiyarsa yaji ya harba da sauri yabi jikinsa da kallo yadda gabansa ya tashi sosai gbdy ruwan shaawa ya