Sashe 68
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wata irin murya kamar tana tare dashi ya dade zaune har goshin asuba sannan ya zare hannunsa cikin na mami ya fito ya nufi d'akinsa kamar ya d'an kwanta ya huta dan wani irin sara kanshi ke masa amman yasan ko ya kwanta bazai ta'ba iya runtsawa ba saboda halin da mahaifiyarsa take ciki ." kai tsaye hanyar bathroom ya nufa ya tura kofar ahankali ya shiga domin tsarkake jikinsa bayan ya zare jallabiyarsa wanka tsarki ya soma alokacin da ruwa ya fara sauka ajikinsa zuciyarsa ta fara hasko masa komai daya faru a awanin da suka gabata "sweet heart kinga irin matar da kika za'bawa rayuwata ko ?" Kin aura min mazinaciya ,kin aura min macen data gama zubar da mutuncinta a waje Ko adadin maza nawa ne suka kusanceta ?yayiwa kanshi tamabayr yana furta kalmar subhallah acikin zuciyarsa "a gaskiya sweetheart baki kyauta min ba ,shiyasa raina yaki amsarta zuciyata taki sonta, babu shakka wannan dabi'ar ce yasa zuciyata ta qasa amsarta amatsayin mamata "nan da nan zuciyarsa ta fara tafarfasa yana jin tuttukin bakinciki sakama kon yadda yaji maryam akan gado "sweetheart kin sadaukar da rayuwarki akan mazinaciya batare da kinsani ba wani zazzafan numfashin ya fesar kana ya cigaba da wanka da wannan tunanin yayi wankan tsarki Ya gama ya d'auro alwala ya fito ya sauya wani jallabiaya mamadin ya kwanta ko ya zauna sai kawai ya tsinci zuciyarsa da s n gabatar da nafila "gara ya koma zuwa ga ubanginsa ko zai fita daga cikin maseefun da yake ciki na tsawon shekaru Cike da tashin hankali maryam ta shiga d'akinta ta samu waje ta zauna tana duban mami "wani irin soyayya mami take mata haka ?ta furta a saman lip's dinta tasan mami na matuqar qaunarta amman bata ta'ba tunanin zata aikata haka akanta ba ,kanta ta kifa a daidai hannun mami hawayenta na zuba "allah sarki mami kina s na da yawa ,kina son cigabana ta kowani hanya kina nan kina shirya min yadda zanji dadi a gidan d'anki ni kuma mahaifiyata tana nan tana shirya yadda zan cutar da d'anki domin kuwa da magungunan da sukai masa sunyi tasiri sai abinda tace masa zai yi amman duk runtse duk wuya bazata ta'ba barin yaya adam ya juya wa mami baya ba idan sukai nasara akanshi sake kwantar da kanta tayi tana tunanin irin kallon da ATA yake mata wanda ke d'auke da tambayoyi kuma tasan duk akan yadda ya sameta ne ."hakika maryam kinyi gaugau wa arayuwarki "ko a wani matsayi yaya adam zai dauketa fatanta allah yasa yau n cikin zai shiga dan kuwa idan ya shiga kafin yau akwai kutirin bala'i a gidan ." sosai tayi zurfi cikin tunani qarar wayarta ce ya dawo da ita daga tunanin da take ta yunkura ta mike da kyar ta d'aga tana duba screen din wayarta sunan mahaifiyarta ce ta kalli agogon wayarta tana mamaki kiran me take mata adaidai wannna lokacin ? kamar bazata d'auka ba sai kuma ta kara wayar a kunneta ta shige bayinta tana magana qasa qasa ."ummah lafiya ?okay to shikenan amman karki aiko da komai s i mami ta wuce bayan ata ya idar da nafila ya zauna yana addua tare da neman zabin allah arayuwarsa ,wannan shine karo na farko da yayi wannna tunanin da kuma addua wa mahafiyarsa yana zaune har aka kira sallah asuba ya mike yayi alwala ya fita zuwa masallaci ya gabatar da sallah sannan ya dawo bai shiga d'akinsa ba ,ya shiga d'akin maryam domin duba mami wanda alokacin itama mrym tayi sallah tana kwnace abayan mami tsaki yaja tare da jan qafarta d'aya ." firgigib ta bud'e idanunta ta mike zaune tana shafa idanunta bai tsaya wata wata ba yaja hannunta hanyar waje yayi daita ,maryam wanda keta rokonsa ya barta a kusa da mami amman bai kulata ba yana kaiwa waje yayi fillinging daita ta zube qasa tana dubansa "yayinda shi kuma yake jifanta da wani mummunar kallo,"bai ce mata komai ba dan idan ma ya nuna mata yaji ciwon rashin samunta a cikakkiyar budurwa zata iya cewa kishinta yake wanda shi kuma har ga allah ba kishinta yake ba, kawai yadda ta munafurci mahaifiyarsa ta nuna mata cewar ita din mutuniyar kirkice yafi damunsa "kiji abinda zan fad'a miki kar na sake ganinki a kusa da mahaifiyata domin ita din mutun ce mai tsarki "hannuwanta duka ta d'aura bisa kanta tana kiran "wayyo allah na shiga uku dan ko bai fito fili yayi mata dalla dalla ba ta fahimcesa fiyye da haka "shiiiiii ! karki kuskura ki tasa min uwa daga bacci idan ba haka ba wallahi kinji na ranste sai na d'agawa uwarki da ubanki hankali kin dai san halina, Kinsan abinda zan iya yi dan haka stay a way from my mum ."yana gama fad'ar haka ya juya ya koma d'akin ya zauna kusa da mami yana kallon yadda take sauke numfashi normal ba kmar d'azu ba ." Maryam kam komawa tayi Kan step ta zauna ta raku'be jikinta waje d'aya tana tunani yadda zatayi "wani hanya zanbi ni maryam ya fahimci shine mutum na farko da ya fara sanina ya mace ?"babu wata hanya tunda rashin hakurinki ya janyo kika mallaka masa kanki baya cikin haiyacinsa zuciyarta ta bata amsa da haka amman kuma ai kina da sheida ?tabbas kina dashi sister itace sheidata ta d an ji natsuwa kad an amman duk da hk hankalinta ba a kwance yake ba .a hankali ta mike tsaye ta fara tafiya kamar mara laka ajiki jikinta ba qaramin sanyi yayi ba ganin irin kallon zargin da yake mata duk yadda taso taji haushinsa ko kuma taga laifinsa zuciyarta ta kasa kar'bansa amatsayin mai laifi ko wanda zataji haushi sai ma taga kamar ya fita gaskiya kuma kowaye dole irin kallon da zai mata kenan . idanunta taga suna ganin duhu akan kujera mai zaman mutun uku ta zube ta kwanta tana runtse idanunta ." Karfe takwas saura maryam ta farka ta sauke idanunta akan agogo bata sake yunkurin komawa bacci ba ta tsaya ta gyara ko'ina tare da shiga kitchen da yin abincin da zasu yi breakfast dashi sai dai har lokacin zuciyarta cikin dar dar take ta kasa jin sukuni dan hango katoton matsala wa rayuwarta take . Karfe goma gabdayansu ya'yan mami suka harllara a gidan kuma a dakin maryam .maryam din ce kad'ai bata cikinsu tana parlour n qasa cikin jimami yayinda ATA ke gabana mami yana magana cikin tsananin damuwa "dan allah sweetheart ki bari na fitar dake zuwa kasar ndia a duba min lafiyarki murmushi iya baki mami tayi tana cewa "adamcy kenan baka son na mutu ko ?mami tayi masa tambayar idanunta na kanshi "wallahi banaso sweetheart!"Yayi maganar kamar zai yi kuka kallonsa kawai mami take without saying a word to him sai dai wani irin tausayinsa ne ya mamayeta da sauran yanuwansa tabbas ta yarda kuma ta amince d'anta na mutuqar qaunarta damuwar dake yawo cikin rayuwarsa ne ya hanashi yi mata biyayya runtse idanunta tayi sai ga hawaye sharr yana sauka akan quncinta ". hannunta ya riko gam cikin nashi yana cewa "why sweetheart?me yasa zaki zubar da hawayenki "ki daina kuka please idan wani abu kike so ki fad'a min am ready do anything for you sweetheart idan kuma tafiyar ne bazakiyi ba wallahi na hakura bazan takura miki ba amman dai bana son na rasaki, dan a yanzu idan kika mutu ba iya yan'uwana ba hatta mutane gari ma sai sun min gori akan rayuwata aunty shahida ta kallesa tasan sarai daita yake maganarsa ."an waye gari wai yar'uwata ce da kanta tamin gori sweetheart a karon farko naji na tsani kaina duk da nasan tayi min n akan abinda nake miki ,nasan na sakaki cikin damuwa sweetheart ki yafe min lafifukan da nayi miki abaya da wanda zanyi a gaba nasan kina sona da wannna yarinyar ne yasa kema kike takura min amman dan allah ki yafe min tsanar da nake fad'a miki inawa yarinyar a gabanki nasan tana sakaki cikin tsananin damuwa "wallahi sweetheart na sha fad'a miki Kiyi min addua ko allah zai saka min soyayyarta acikin zuciyata amman har yanzu shiru babu wata alama ta qaunarta "ya qarashe maganar muryarsa na rawa mami ta kallesa idanunta cike da ruwan hawaye tace "tabbas yawon fadar tsanar da kakewa maryam tana bata min rai amamn adamcy na yafe maka duniya da lahira burina allah ya had a hankulanku waje d'aya ." aya bayan daya yan'uwansa suka baro d akin zuwa parlour suka had'u gabadayansu suna hira har da maryam nan aunty shahida take basu labarin abinda ya faru "kai auntynmu dan allah da gaske ?wallahi ga maryam ku tambayeta "gaskiya auntynmu kin gama da yayanmu "inji cewar zabiba maryam ta mike tana mai jin tsananin farinciki yadda yan' uwanta kuma dangin mijinta suke matuqar qaunarta aunty khadija tace "ai gara da,aka gama dashi baki ga yayi laushi ba duk ya canza kala kamar bashi ba ,yaro sai shegen taurin kai da fadin ran tsiya ai ni wallahi mami tayi min daidai ai da mun san d'an wannan shirin film din zai dawo dashi haiyacinsa da tunin an dade da wuce gurin aunty khadija ta qarasa maganar tana miqawa zabiba hannu suka tafa Allah dai yasa buqata ta biya." nana hauwa'u tayi murmushi tare da mikewa tana cewa in sha allahu ta biya sai fatan alkhairi ta shiga kitchen inda maryam take qoqarin gama tuwon shinkafa da miyar agushi . tun daga falo kamshin miyar ke shiga hancin nana hauwa'u har sai da yasa yawunta tsinkewa "matar yaya wannan kamshi haka kamar zaa tafi gasar abinci "kai sister yau kuma tsiya zaki min "? ke mu bar wannan maganar yaya had uwarku da yaya ta kasance daren jiya ?"nan da nan yanayin maryam ya sauya idanunta suka canza kala alamun zatai kuka "babu wani jin dadi sister yayanki wani kallo yake min wanda bazan iya fitowa na bayyana shi ba .nana hauwa'u ta dafa kafad anta "karki wani daga hankalinki ko sarewa "me yasa zaki fad'i hka wallahi sister a matukar tsorace nake "ba gani ba meye abun tsoro ?nana hauwa ta fad'a cike da kulawa maryam bata san sanda ta rungumeta ajikinta ba tana share hawayenta