← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 105

Sashe 19

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

zafi ma duk bai taso ba ATA sai hakuri fa kuma wallahi irin wannan auren ma ya fi dadi gashi da alamun mrym din ma tana sonka zakayi yadda kakeso daita har Allah yasa ka fara sonta ammar ya fada yana dariya, da sauri ATA ya daga Kai yana cewa "me yasa kace tana sona ?ai mace idan bata son mutun da wahala ta yarda a daura aure ka duba nuzla misali ce guduwa tayi har sai byn daaka daura auren hisham da nana hauwa'u ". wannan ba gskiya bane , nana hauwa'u ta auri hisham ne ba dan tana son shi ba hakazalika nima na auri yarinyar nan ba dan ina sonta ba "anya kuwa wata killa fa nana hauwa u tana son shi ta boye ne kawai dan bata damar samunsa a wannan lokacin dan hk kawai ka rike marym dinka kamar yadda hisham ya hakura da nana hauwa u ."I can't" ya fada atakaice, dariya ammar yayi yana cewa "Ka bani dariya,irin ku n da anyi mistake kun kusanci matan da baku so sai ciki."duk fa zaka gama cika bakin kiyayyar ne ka gama zaka zo ka nemi hakinka ". Allah ya tsareni da ganin wannan bakar ranar "kai dai sai idan babu rabo a tsananinka daita amma wallahi in da rabo komin kiyayyar dake tsakaninku sai kun jone anyi ciki " ammar ya fada masa hk cike da zolaya ."yanzu ya batun yarinyar da nayi maka maganarta yanzu zaka aureta na hadaku dan gsky idan dai da gaske aure zaka qara gara wannan yarinyar ? wallahi kawai sweetheart nake tunani nasan ma da wahala ta barni bayan ta matsa maka ka auri zabinta sai kuma ta hanakali qarawa gsky ta barka ka qara tunda kana so . Kai dai bari kawai ammar abinda nasani ko banyi acikin lokacin nan ba zanyi a gaba ko nan da shekara goma ne sai na qara aure "Gsky abun naka na gaske ne "kai dai ka tayani addua Allah ya bani wata mai kyau kamar irin mace da nike so da gudu ma kuwa zaka sameta dan wannna yarinyar da nake maka mgn akanta ta had u sosai ata ya girgiza kai "da wahala haduwarta ta burgeni nifa ina da test "okay kenan ya kamata ka hakura ka rungume matarka amman kuma wallahi maryama ta had u matar manya irinku ce ". "Maryama !"?ya furta sunan a tsanake yana duban ammar yana jin sunan na ta'ba ranshi wanda bai kamata yaji hkn akan kowa ba sai akan princess dinsa ,muryarsa a kasalance yace "sunansu daya da wannnan dolen dolalon yarinyar "wacce kuma haka ? wannan yarinyar daaka aura min mana yayi mgnr yana jan tsaki ammar yayi murmushi yace eh sunansu daya ko bazaka aureta bane sbd sunansu daya ?kai ban son iskanci ya kake wani tursasa ni kamar dole to bazaa aureta ba muyi abinda ya kawoka nan da nan yayi qoqarin canza mgn zuwa ta business dinsu. Ammar kuwa sai faman dariya yake wallahi ata kabani dariya wai dolen dolalo kai ata wallahi baka da kirki nifa ina jiye maka tsoron ruftawa karkazo kana rokonmu muje maka rarrashin dolen dolalo tace sam bata san da wannan ba wani tsaki yaja yana maka masa harara . bai sake cewa komai ba ya mike tsaye yana cewa ina ganin baka shiryawa kasuwanci ba ko kafin ammar yayi magana tuni ata ya soma taku ata tsaya mana dan allah ka dawo muyi mgn tsaki yaja ya shiga bayan mota dan tuni masu tsaranshi sun bude masa gidan baya . Mmn sudais MAR'ADAMS
Chapter 19 · 0% Book details