Sashe 36
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dawo kenan bazan koma wannan gidan mai kama da makabarta ba sai na kwana biyu .nana hauwa u ta zungurinta kan tayi shiru amma ina maryam bata fuskantarta ba mami ta miqe tsam ta basu waje dan tasan dole zasu tautauna a tsakaninsu . mami na fita nana hauwa u ta zubawa maryam duka a cinya wallahi ki rufa min asiri baki isa ki kwana a gidan nan ba yadda na dauko ki haka zan maidake gidanki wajen da nana hauwa u ta daketa take sosawa tana dariya tace wallahi babu inda zani kamar zaki iya bayan kina tsananin sonshi ? kai nana hauwa u ban da sharri wa ya fad a miki son 'ya'yan take?inji zabiba ta fad a tana murmushi nana hauwa u tace ai ni tuni na san da wannan ga tanan kuma idan ta isa ta karyata ,sister ban da sharri fa auren daaka samu na amince da kyar zaki zo kice ina son shi nana hauwa u ta sake qara mata wani dukan maryam tace babu komai wallahi koda da zafi ni banji zafin ba, dan bakya laifi ko kin kashe dan masu gida wani dan masu gida ? yayanki ! dariya suka bushe da ita gabad aya su Aunty zabiba tace "Kefa sabon iskancin mai lasisi kikaje kika koyo a gidan yaya barta dole tayi iskanci da alamun taga gadon baccinsa shima yaya naga ya canza kwana biyu da alamun ya angwance inji cewar zabiba wallahi ku daina fad ar haka kar sautsayi ya shigo dashi mu shiga uku ku dai shiga uku amman mu ai yayensa ne dole ya daga mana kafa dariya maryam ta saki har da tafa hannu wannan kanin naku ai mami kawai yake d agawa kafa hira suke sosai yayinda maakatan gidan suka cika gabansu da kayan marmarin da abinci da abun sha aunty khadija ta dubi auta da alamun kin samu lafiya alhamdulillah Aunty khadija rayuwar aure is not easy amman haka zamuyita hakuri har allah ya kawo mana sauki Ameen kefa maryam yaya zaman naku da uban shegu ?uhm ta numfashi to da sauki zance amman ni matsalata mai girma ce kuma ban san ranar da zan fita ciki ba ta qarasa maganar kamar zatayi kuka . Gabad aya suka zuba mata ido cike da tausayawa ita fa siater matsalarta mai sauki ce ba kamar ni ba da ko muryata baya son ji baya cin abincina kona girka sai dai masu gadin gida suci bani da kwanciyar hankali matukar yana gida , sister kuwa nuzla ce matsalarta amman ni zanyi maganinta ki rabu daita huce haushi take akan hisham shi kuma rashin ganewa ne idan ba haka ba ko sauraranta ma yayi inji cewar aunty khadija allah ya kyauta daga nan Suka cigaba da hirar matsalolin rayuwa wani suyi dariya wani suyi jimami cikin haka aunty abida ta shigo daman ita tana yawon shigowa ko dan taji halin da ata yake ciki a wajen mami diyana da rukkaya suka shigo su kuma nana hauwa u ce ta kirasu kusan duk yammatan gidan suka shigo aka sake bud e habin hira banda nuzla har karfe shida ta buga suna tare ana hira . Ahankali motocin ata suka shigo haraban estate dinsu sakamakon kiransa da mami tayi suna gama daidaita tsayuwar motocin ya fito kamar ance ya kalli kofar gidan baba babba hisham ya gani tsaye tare da nuzla ya zuba mata ido kamar zai mata numfashi . shiru yayi yana mamakin karfin halinsa ko bai ji kunyar kowa ba ai ya duba mami bare tsakaninsa dashi ahankali nuzla ta kalli inda yake kallo d aya tayi masa ta d auke idanunta tana jin farinciki dan yanzu bata jinsa aranta haka ne ma yasa take son dandanawa jininsa wahala kuma har ga allah tana son ta auri hisham yanzu dan hishsm miji ne bancin yana kawo mata uzurinsa akan mahaifiyarsa da yanzu ta dade da kasamcewa a gidansa . daya daga cikin masu tsaron bakin get din ya dagawa hannu ya taho da sauri ya tsaya a gabansa cike da girmamawa daman hisham na zuwa wajen nuzla ne ?Eh !ranka ya dade kusan kullum yana zuwa shiru yayi kafin daga bisani yace okay zaka iya tafiya ya juya ya koma bakin aikinsa shi kuma ya nufi kofar gidan mami yana kiran mb ,yayan mami suna shirin mikewa su kama gabansu har nana hauwa u dan ita maryam mami tace ta zauna ATA zai zo sai su wuce tare suka ga mutun ya shigo kamar wanda aka jehoshi yana huci gabad aya suka mike tsaye suna kallonsa . bai ce masu komai ba ya samu waje ya zauna akan kujera yayinda kannensa suka gaishesa amman yaki magana ya soma waya da yaya Ibrahim . Hankalin mami ya tashi ta qaraso garesa ta dafa shi tana tambayarsa lafiya adamcy naga ka shigo wani iri ?still shiru yayi yaki magana ganin haka aunty shahida ,aunty khadija da zabiba har da nana hauwa u sukai ma mami sallama zasu wuce muryarsa a kausashe ya soma magana cikin tsananin fushi auta kar naga kin fita daga gidan nan kin dawo gida kenan . gabad aya suka dawo cikin tsananin tashin hankali suna dubansa akan wani dalili kenan adamcy ?aunty shahida ta tambayesa yayi shiru yana huci tamkar zaki ka barta ta koma gidanta tayi zaman aure tunda suna zaune lafiya da mijinta inji wa yace miki haka ?ya fad a a zafafe yana fesar da hucin numfashi zaku iya wucewa amman ita babu inda zata mami kam shiru tayi ta kasa magana mami kice wani abu mana kinyi shiru kina kallonsa aunty khadija ta fad a tana dubanta zaku iya wucewa zanyi magana dashi Suna shirin fita mb ya shigo dole tasa suka tsaya kallo d aya yayiwa abokinsa ya fahimci akwai damuwa ya qaraso kusa dashi ya zauna yana cewa yaakayi friend ! kace nazo yanzu yana qoqarin bud e bakinsa yaya Ibrahim ya shigo ya fesar da numfashi sannan ya soma mgn mb daka shigo yanzu kaga hisham tare da nuzla ko baka gani ba ? na gansu amman. dakata mb an tabbatar min kullum yake zuwa wajenta kuma nasan yana yin hakan ne saboda ne .juya can ka kalli auta da kyau haka aka kai masa ita ?yau zaa yita ta qare gidan nan laifin mai tayi masu ?idan laifi ne ,ni ne nan nayi saboda naki amincewa da soyayyar nuzla kuma nasan shine sila da dalilin son a kuntatawa auta tunda ni babu abinda zaa iya min ,dan haka yau zan kashe wannan aure . mami ta sauke numfashi sannan ta mike ta bar wajen. dan tasan halin d anta wani irin murdaden mutun ne mai wuyar shaani uwansa ma numfasawa sukayi domin wannan karon fad an gasky yake da son kwatarwa kanwarsa yanci amman sunyi mamaki wannan shine karo na biyu da ya nuna kulawarsa akan nana hauwa u amman duk da haka bazasu bari ya kashe mata aure ba . maryam ta kallesa taga yadda hankalinsa ya tashi akan yaruwarsa ya manta irin azabar da yake gana mata ,ya manta cewar itama diyar wani ce yake quntata mata hawaye ya cika idanunta tausayin kanta ya kamata ta kalli nana hauwa u taga itama hawaye take ta kalli ata cikin sa a idanunsu ya tsarke cikin juna tayi kamar zata girgiza masa kai amman wata katuwar hararar daya zabga mata mai had e da kallon banza yasa ta d auke idanunta akanshi ,tana mai share hawayenta da hannu ta qaraso kusa daita nana hauwa u ta riko hannunta zuwa gefe sister kinji hukunci yayanki dan allah karki yarda ya kashe miki aure saboda ya hisham mutumin kirki ne nuzla ce matsalarki . bani da zabi sister bazan iya ce masa a a ba duk abinda yake son ya zarta akaina na amince ni mai biyayya ce a garesa ,maryam ta rungumeta ajikinta bakya son yaya hisham ne ? to bazan ce bana jinsa araina ba , amman idan yayana yace na koma gidansa zanyi idan yace a a babu inda zani wallahi sister kina son mijinki ta fad a tana zare jikinta a nata ta tsura mata ido tana kallonta hawaye ne kawai yake fita daga cikin idanunta qirjinta har wani sama da kasa yake ta riko hannunta tana cewa shi bai rike nashi auren ba zai kashe auren wasu muje ki fad awa mami kina son mijinki nana hauwa u taki binta ta zare hannunta ta rakube gefe tana share hawayenta dole tasa maryam ta dawo ta tsaya kusa daita tana share mata hawaye . mb ya kira layin hisham cikin kankanin lokaci sai gashi ya shigo yayi mamakin ganin mutane cike ya tsaya yana kallonsu d aya bayan d aya sai dai bai ga matarsa acikinsu ba , wani mugun kallo ata yayi masa sannan ya qaraso gabansa ya tsaya tare da jin kai ya zuba hannuwansa duka cikin aljihunsa baka son auta shiyasa ka zabi ka dinga quntata mata ta wannan hanyar ko ?hisham yayi shiru yana mai sunkuyar da kanshi kasa dan jin kunya kasani nasani kowa yasani ban bada goyon bayan auren nan ba dan har yanzu bana son aurenku daita cool down ata mb ya fad a yana dafashi ya buge masa hannu yana qoqarin cukumar wuyan hisham yaya ibrahim ya shiga tsakaninsu dan girman allah ka matsa babu inda zani ka samu waje ka zauna ayi magana ta natsuwa idan har kaga na zauna to ya miko min takardar sakinta dan bazata qara zaman aure daahi ba har abada ya saketa yaje ya auri wacce yake so . Mmn sudais MAR'ADAMS *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 12 Jin abinda ATA ya fad'a yasa maryam duk ta rud'e sai zufa take fitarwa hankalinta yayi matukar tashi gbdy ta nemi natsuwarta ta rasa domin tasan halinsa tunda ya furta zai raba auren lallai zai aikata hakan "ta fashe da wani irin kuka mai karfi , haka ma nana hauwa'u kuka