Sashe 18
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
, mami ta sauke numfashi ,gbdy ta gama karantar maryam tana mugu mugun son adamcy ,ta kuma san muddin ya gano hk zaa qara samun matsala ne ." "Nima baa son raina bane dan burina bai wuce na ganku tare cikin koshin lafiya da farinciki ba amman shi adamcy din ne zuma ne sai ancisa da wuta "haka zamuyi hakuri dashi muyita masa addua allah ya sausauta zuciyarsa ta fad'a tana sake kwantar da kanta a cinyar mami shiru parlour'n yayi baa jin motsin komai sai na saukar numfashinsu dana ac dake aiki sai kusan shabiyu mami ta mike tana jaddada mata tayi qoqarin ta shawo kansa yazo anjima bata hakuri ."ta qarasa mgnr tana dariyar tsokana ." "Dan allah mami ki rufa min asiri ina ni ina tarar aradu wannan ai sai ke "mami tayi murmushi tare da yi mata sallama ta shiga mota suka baro gidan, mami kam da direbanta ya d'aukota bai wuce koina daita ba sai hanyar gida tana zaune abayan mota tana tunani abubuwa dayawa abinda yafi komai daga mata hankali soyayyar adamcy din data ga ya samu kyakkyawan mazauni a zuciyar maryam da kuma qiyayyar adamcy gareta tasan baqaramin wahala da qalubali zata sha a hannunsa ba dole tana bukatar taimakonta ,dan dole kuma tasa ido arayuwar gidansu idan ba haka ba maryam bazataji dadin rayuwar aurenta ba ." Tana cikin wannan tunanin wayarta ya fara ringing it was nana hauwa'u sai data sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta dauka tana cewa "auta ya kike ya gida da fatan kuna lafiya ? to ya zaman naku yake ? "To shikenan ayita hakuri wata rana sai labari okay zan kirata in sha allahu ,yanzu ma ina Kan hanyar komawa gida ne daga wajen marym nike "eh to lafiya dai ba lafiya ba "mami ta fad'i haka cike da raunin murya baangaren nana hauwa'u tace "lafiya mami me ya faru daga tarewa jiya jiya km ?. "Kinsan halin yayanki ai "me yayi mami? "wai akai masa amarya yaki kwana a gidan wallahi jiya kwana nayi cikin damuwa da tashin hankali amman nima yau nayi masa hauka dan na nuna masa ba tsoronsa nike ji ba mari uku nayi masa masu kyau ,wallahi kuwa nasan da zarar ya sauko zai shiga hankalinsa ya dawo ban hakuri ,ku barni dashi duk zan sauke masa abinda Ke damunsa in sha allahu bazan bar duniya ba sai ya canza rayuwa ai ko da mutane suke ganin Kmr yafi karfina, ba karfina yafi ba zan haifi d a ne nazo ina jin tsoronsa? kawai dai ina lallabashi ne sbd bana son takurawa rayuwarsa mota na tafiya suna hira da auta har ta kawo gida." Wayarsa ce ta fara ringing sai data katse bayan ya gama shan kamshinta ya ciro yana dubawa Hannunsa daya yasa ya rike qugunsa dashi yana takawa zuwa bakin window din dakin ya bude yana kallon haraban gidan inda masu tsaronsa ke safa da marwa magana yayi wanda bai wuce ta minti uku ba ya katse ya soma cire kayan jikinsa ya fad'a bayi dan wani irin zafi jikinsa ya d'auka ga sarar da kanshi yake masa zama yayi acikin bathtub ruwa na sauka a sansar jikinsa " ita kuwa maryam ta shiga d'akinta cike da faduwar gaba ta zauna abakin gadonta tana tunani ta dauki lokaci zaune tana tunani hali irin na mijinta har sai data duba taga lokacin sallar azahar tayi ta mike ahankali ta shig bathroom ta dauro alwala ta fito ta gabatar da sallah bayan ta kammala ta koma ta zauna a inda ta tashi ta tsurawa tv dakin ido sai dai sam batayi shaawar kunnawa ba bare ta d ebe mata kewa tayi shiru tana tunanin ya kama taci wani abu dan tun abinci jiya ne acikinta dan haka ta fara tunanin fitowa ta samawar cikin wani abu ." Ahankali ata yake saukowa sanye da wasu kaya , jikinsa na fidda kamshi mai sanyi dadi ya ajiye wayarsa akan center table ya samu waje ya zauna ya d'auki remut ya kunna tv ya qara karfin ac ya daura kafafunsa akan table yana duban tv ,ahankali maryam ta fito daga dakinta cikin sanda kamshin turarensa ya bugi hancinta sam batayi tunanin yana parlour'n ba tafi tunanin ko yana dakin yana shirin fita ya bar gidan ne, dan haka ta cigaba da saukowa tana saukowa tana sake jin kusancinta da kamshin turarensa mai sanyi da bugar da zuciya ta lumshe idanunta tana cigaba da daura kafafunta akan step ai tana gama saukowa kawai taga mutun zaune tmkr wanda aka dasa ." Tsananin tsoron data tsinci kanta ciki sauran kad'an ta saki fitsari a inda take tsaye ,nunayen ajiyar zuciya da numfashi ta sauke alokacin daya ta sanyawa jikinta jarumta kana ta soma tafiya cikin sanyin jiki zata shiga kitchen, a natse ya d'ago idanunshi ya zuba mata oly eye's dinsa masu firgitar da mutun dole taja ta tsaya sakamakon idanunshi da taji suna yawo a gbdy ilahirin jikinta ta hade yatsun hannunta waje daya ta dago kanta zuwa Kan kujerar da yake zaune taga yayi mugun hade fuska tmkr zaki yana kallonta a kaskance ." " zata iya cewa tunda tasanshi arayuwarta bata ta'ba ganin yanayinsa haka ba alama yayi mata da ido ta koma amman ta dauke kanta tayi kmr bata fahimcesa ba har tayi taku biyu taji Kmr ya mike ai da mugun gudu tayi Kan step, bata tsaya akoina ba sai a dakinta har da rufe kofar ta tsaya tana haki da maida numfashi "bayan ta samu natsuwa kwalla ta zubo mata "bata san tana tsananin tsoronsa ba sai yanzu yaya adam baya sona gashi ni kuma ina sonshi ta fad'a a fili cike da sanyin jiki ta zauna jugun tare da dafe kuncinta ." kusan awa daya taji motsin fitar motocinsa ta sauko da sauri sai dai hawaye ne ya zubo daga idanunta Sakamakon ganin ya rufe kitchen din duk inda ta kalla acikin parlour'n babu wani abu da zata iya sakawa cikinta dole taja jikinta ta dawo daki bayi ta shiga ta dauro alwala ta gabatar da sallar laasar ta kwanta lamo a saman abun sallah yunwa na nukur kusanta sai tayi kamar ta kira mami akawo mata abinci sai tayiwa kanta fad'a ta maida wayar ta ajiye ." wasa wasa awanni suka dinga wucewa duhu ya fara sako kai lokacin magariba yayi a daddafe ta tashi tayi sallahr magariba ta dawo ta kwanta a haka ishai tayi wanda zuwa wannan lokacin ta fara raina kanta tuni hawaye ya fara fareti akan kuncinta tasan mugunta da kuma hukuntata yasa yayi haka tana daga kwance amman jiri take gani saboda tsananin yunwa tuni idanunta suka canza kala saboda kukan yunwa da take bata san yunwa bata da hakuri ba sai yau hatta test din miyon bakinta ya canza ." Ata kuwa tunda ya fita yana wajen wani abokin kasuwancinsa daya sauka a kasar yau din nan sun jima suna tautaunawa akan kasuwanci shi kanshi banda coffee babu abinda yasanyawa cikinsa karfe bakwai daidai a haraban family house dinsu tayi masa, yana qoqarin fitowa daga mota yaga direban mami na fitowa daga gidanta hannuwansa duka rike da wasu hadaddun kuloli aransa yace shegiyar yarinya sarkin rashi hakuri har ta kira akawo mata abincin ,ai da baki kira ba yau haka zaki kwana da yunwa nonsense girl kawai . massalaci dake cikin esate din ya shiga yayi sallah bai fito ba har sai daaka idar da sallah ishai ya zauna yana azkar yana nadamar abinda ya fadawa mahaifiyarsa wanda yayi haka ne cikin zafin zuciya gashi yanzu yana dayasani ."ahankali ya dinga jin rashin kyautatawar da yayi mata , nan da nan kyakkyawar zuciyarsa ta dinga umartanshi da yaje ya bawa mahaifiyarsa hakuri ya nemi tafiyarta yayinda bakar zuciyarsa ke gargadinsa har ma da bashi karfin zuciyar nisanta kanshi daita . wayarsa dake ringing ya katse masa tunanin da yake ya ciro yana duba wayar sunan ammar ya gani ya dauka yana cewa "yaakayi ammar ?eh mun gama magana dashi yanzu haka ina family hausa ,ok bani minti biyar yanzu zaka ganin a gaugauce ya fito ." Kai tsaye rufar da yake zama da bakinsa ya nufa inda ya iske ammar yana ganinsa ya washe baki yana cewa ango !ango !! angaishe da ango kasha kamshi" "A ina kenan na sha ? A wajen ama... "kaga dan Allah malam ka barni naji da abinda ke damuna dan ni babu wani kamshi dana sha kuma bana saka rai zan sha shi har abada ". kai dai anyi mai cutar kanshi kai muguntar ma har da kanka zakayi wa ?"har kuwa karshen rayuwata zan cigaba da zama haka ban sha wannan kamshin ba ya fad'a yana zama acikin daya daga cikin kujerun dake ajiye agurin ."ai ni an gama da rayuwata an cuceni wallahi amman I think kawai zan samu wata in aura dan bazan iya rayuwar aure da wannan yarinyar ba dan sam sam attitude dinta is something else..." ya fadawa ammar yana jan dogon tsaki . "hmmm amman da kayi hakuri ka d'an sake daita kad'an kagani ko tafiyarku zatai daidai "no it can be possible ammar "okay idan haka ne na hadaka da wata sabuwar mai bautar qasa dake karkashin kamfaninmu yarinyar tana da kirki sosai , koni bancin bani da wata matsala da salima dana shiga sawun masu nemar aurenta dan yarinyar akwai natsuwa da kirki ga kamun kai shuru ata yayi without saying a word."Ko baka sonta ?.."ammar ya tambayesa, ahankali yace " ammar I don't really know tunda banganta ba amman bani da zabi tunda na rasa princess zan iya manage da wata "ya qarasa mgnr yana duban fuskar ammar" to kayi hakuri da mrym din kawai madadin ka qara da wata tunda itama wacce zaka aura din ba sonta zakayi ba manage ne ai kaga gara kawai ka dinga rage zafi da mrym kawai zai fi ga tarin ladan aure gana biyayyar mahaifiya" over my dead body ni fa I can't let the woman I hate touch my fingers balle hannuna har azo ga jikina gaskiya ammar bazan ta'ba Iyawa ba ." Bama zan barta ta ta ba ni ba bare ni na kai kaina dan rage zafi tayi zamanta haka nima nayi rayuwata haka amman batun rage