Sashe 64
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fito ya shig kitchen duk sai daya duba cabinet din kitchen din nan ma bai ga wani abun kirki da zaa had awa mutun breakfast mai kyau dashi ba dan haka jiki a sanyaye ya fito yana kwallawa maryam kira yayinda mami tana nan zaune tana kallon tv tana cigaba da kora ruwan tea da sauri maryam ta sauko tana dubansa gabanta na wani irin bugawa da karfi muryarta a raunane tace yaya gani ? meye haka ?me ya faru kuma ?itama tayi karfin halin tambayarsa har ya d aga hannunsa ko me ya tuna ya sauke ya dafe goshinsa a fusace ya cire hannunsa ya d an saci kallon mami ita kuma ta zuba masa idanu tana ji da ganin abinda zai faru maryam taja baya tana jin yadda zuciyarta ke rawa meye wancan agaban mami ?ya sake wulla mata tmbya tayi shiru tana dubansa a tsorace ya zira hannunsa daya cikin aljihunsa yana sake yin magana a tsawace meye haka ina magana kina jina ?abinci ne ! what ?!ya furta a tsawace . ta sake ja baya kar ya wanka mata mari dan a yanayin da yake kallonta babu sausauci amman zaki iya bawa mahaifiyarki irin wannan breakfast din ? gabanta yayi wani irin mugun fad uwa ya tsura mata ido hakan ya bala i bata tsoro gbdy ya sake canza mata ya fara taku zuwa inda take tsaye tana yar kyarma tana baya baya yana biyota har sai data kurewa bango wallahi ba da gangan nayi ba babu komai a store ne komai ya qare iya abinda muke dashi na bawa mami . afusace ya d aga hannu zai wanka mata mari cikin wani irin masifaffen tsawa yaji sautin muryar mami wallahi idan ka ta bata ban yafe maka ba . cak ya tsaida hannunsa tamkar an dasashi zuciyarsa na tafasa cike da zafin zuciya ya sauke hannusa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya juyo ya soma taku cike da bacin rai ya qaraso ya zauna kusa daita kamar mai neman gafara ya fara kame kame umm umm ummm nace ba kace me ? shiru yayi yana kallon mami yayinda maryam tayi sauri ta haye sama tana wai wayensu ina jinka adamcy ? Kiyi hakuri sweetheart banji dadin yadda naga kina breakfast haka ba bana zama a gida bansan babu komai a gidan nan ba sannan wannan yarinyar bata fad a min babu komai ba ya qarashe maganar kamar zai yi kuka. mami ta kallesa sosai ta gano halin damuwar daya shiga adalilin breakfast dinta, daman kuma tayi hakan ne dan ya gani numfashi ya sauke yana sosa keyarsa yana cigaba da kallon mami ahankali mami ta tabe baki to ka bata damar da zata fuskanceka bare ta fad a maka babu komai acikin gidan nan ?amman ! sai kuma yayi shiru yana runtse idanunshi . amman me adamcy ?kai kanka kasan baka da wata kalmar da zaka fad a min na yarda a matsayinka na magidanci baka bawa matarka wannan damar ba sam matarka bata da cikakken iko acikin gidan nan yadda kake nuna baka qaunar jamaa da yanuwanka haka kake nunawa matar aurenka ,kai kanka kawai kasani baka damu da damuwar kowa ba dan haka karka rainawa kanka hankali ka nemi daurawa yar mutane laifi ta qarashe maganar cikin fad a saboda halin adamcy baqaramin damunta yake ba ,shi mutun ne wanda babu ruwansa da damuwar jama a sai dai kanshi da aikinsa ya kamo hannun mami ya soma rarrashinta sweetheart Kiyi hakuri kema Kinsan yanayin aiki ne sai ahankali ,ni kaina bana samun time din kaina kamar yadda kika sani amman at least data fad a min zan sa a kawo komai ta bishi da wani mummunar kallo wai yaushe ka bawa maryam wannan damar yarinyar nan haka take rayuwa cikin qunci acikin gidan nan ga rashin so ga yunwa dame zataji ? allah sarki maryam baiwar allah allah dai ya qara miki hakuri amman na cuceki na hadaki da damuwa ,na hadaki da mutun mara kirki ,na hadaki da mutun mara zumunci wanda ko yan uwansa baya so bare wata aba maryam wallahi adamcy baka da tausayi da amana nayi danasanin hada auren nan allah dai ya gyara maka wannan bakar zuciyar taka . Kuka yaci karfin mami . jikin ATA yayi mugun sanyi babu abinda ya tsana kamar hawayen mahaifiyarsa da bai da kamarta jin kukanta yake har cikin zuciyarsa ya sake matsowa kusa daita yasa kanshi akan cinyarta yana jin yadda zuciyarsa yake tafasa yana jin kukanta yana ganin laifinsa amman yafi ganin laifinta domin kuwa itace sanadin da yasa ya kasa sauke nauyin da allah ya daura masa sannan ya kasa mata biyayya ta matsawa rayuwarsa dayawa akan maryam ,shi kanshi baya jin dadin abubuwan dake faruwa ,jin kukanta yake aransa yana jin kamar yayi kuka . ahankali yayi amfani da karfin zuciya irin tashi ya fara bata hakuri da rarrashinta sweetheart Kiyi hakuri nasan bana miki yadda kike so Kiyi min addua wallahi a shirye nake da na canza in zama mai faranta miki ,kuma wallahi ina son yan uwana sweetheart wani dadi ne ya ziyarci zuciyar mami dan abinda tafi bukata kenan ta dade tana adduar ya canja . ya qara gyara kanshi akan cinyar sweetheart dinsa sweetheart ki yafe min ko zan samu sausaucin abinda nake ji araina kada zuciyata ta buga sweetheart ,damuwa tayi min yawa wallahi ni kadai nasan halin da zuciyata take ciki a haka kamar lafiyayyen mutun ne amman sam ba haka bane mutun ne mai dauke da mummunar ciwo a qirjinsa da zaki barni haka babu nauyin kowa akaina zanfi ji dadin rayuwata sai dai zuciyata taji da damuwa daya amman yanzu damuwa tayi min yawa na rasa ya zanyi da rayuwata wallahi zan gwamaci mutuwa sweetheart akan rayuwar da nake . mami tayi saurin saka hannu ta rufe masa bakinsa bata son taji batun zai mutu idan ya mutu tayi yaya ai ita babban burinta ta mutu ta barshi a duniya, tana shafa kanshi tana jin sonshi har acikin bargon zuciyarta ki yafe min sweetheart adamcy baka min laifin komai ba ban ta ba rikeka araina ba kullum addau nake maka d ana sai dai abu daya nake s kamo. ina son ka sausautawa maryam ka zauan da mace mafi cancanta ,maryam ta cancanta kowani nmj idan ya sameta zaka ji dadin rayuwa daita mace ta gari ya dago kanshi yana kallonta ya saka hannu shi ya rike kunnuwansa bazan iya ba sweetheart but I promise you in sha allahu zan kawo miki matar da zan aura in sha allahu zan faranta miki zakiyi farinciki da zabina amman batun wannan yarinyar fa gsky sweetheart sai dai kiyi hakuri .he ending the talk with a smile . mami tayi shiru tana dubansa sam adamcy baya ganin girmanta baya tausaya mata duk son da yake ikirarin yana mata abaki ne bai kai har zuciyarsa ba . shiru kawai tayi tana jin babu dadi ko kadan acikin ranta tana son zubar da hawaye amman data tuna irin matsifar da hakan zai jefa rayuwarsa da alamuransa sai ta fasa sai dai yadda zuciyarta take tukuki ta tabbatarwa kanta tana cikin tsannain damuwa akanshi, idan batayi gaugauwan kawar da hakan aranta ba shima wani bala i ne ga rayuwarsa runtse ido tayi zuciyarta na shirya mata yadda zata kawo qarshen komai Sweetheart me kike tunani haka ? muryar ATA ne ta katse mata tunani , harara ta maka masa tana cewa ina ruwanka da abinda nake tunani ?wayarsa ya ciro ya kira daya daga cikin yaransa ya bashi umarnin a shigo da komai na kayan abinci enough . Cikin kankanin lokaci aka dinga shigo da kayan abinci sai daaka cika store tab da kayan abinci babu abinda babu na amafani haka ma fridge tun a ranar komai ya sauyawa maryam sunci mai kyau ita da mami su sha mai kyua, sai abinda suka ga dama suka girka kuma basuyi wa ATA tayi ba shima bai damu ba tsabgogin gabansa kawai yake yi sai da yamma ne ya dan saci kallon mami yace sweetheart ko zan samu irin coffee da kike min ?zaka samu mana amman a wajen matarka ba tun da yaji ta fadi haka bai sake cewa um ba bare um um, ya cigaba da danna wayarsa maryam najin haka ta matso kusa da mami tace mami dan allah Kiyi masa mana wani kallo mami tayi mata na rashin zuciya irin nata ,mutun bai damu da kai ba amman kai kabi ka damu kanka akanshi please mami ai kema kin iya kije kiyi masa ta rage murya sosai tace idan nayi bazai sha ba amman muje muyi masa tare zai sha mami ta tsura mata ido kawai tana kallonta cike da tausayawa tare suka shiga kitchen din sukayi sai dai koda ta fito parlour bata gansa ba a d akinsa ta sameshi zaune akan kujera yana amsa kira taja qaramin table din glass din dake tsakar dakin ta dora tray din akai ta tsiyaya masa acikin a cup tace gashi ! ba tare daya kalleta ba ya dauka ya fara sha dan a bukace yake . ta juya ta bar dakin tana rufo masa kofa kwanan mami uku a gidan wanda hakan ya haifar da sukuni da kwanciyar hankali ga maryam har mamakin kanta tayi yadda yanayin jikinta ya canza, domin mami nayi mata duk wani abinda zai kwantar mata da hankali tare da kawar mata da damuwarta da zarar taganta cikin damuwa sai tayi duk abinda zata kawar da damuwar sannan hankalinta zai kwanta sosai take kula da cin abincinta mussaman ta dinga had a mata fruit masu gyara skin da qara ni ima ajiki most especially yankakkiyar ayaba da soyayyiyar gyada da kankana da madarar ruwa a had a waje daya wannan kam kullum sai mami ta had a mata ta bata ,wannan had in mai dadi yana aiki abu biyu ne ajikin nmj ko mace yana gyara skin sannan yana qara ni ima ajikin mutun. zaman mami a gidan ya dan kawo sauyi domin duk abinda ATA zai yi na rashin mutunci tana taka masa burki da fushinta domin dai idan ba fushinta ya gani ba baya kin abinda yayi niyya kuma yanzu babu laifi yana cin abincin