Sashe 63
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 19 Sosai mami ta dinga rarrashin maryam tana masu addua allah ya daidaita tsakaninku ,Allah ya saka tausayinki acikin zuciyar adamcy ,allah ya kawo zaman lafiya a tsakaninku har qarshen rayuwarku ahankali maryam Ke amsawa da Ameen mami ,sai abu na gaba maryam na fahimci kina sakaci da addua ,Ina son kinsan wani abu ba a nasara sai an rike Allah,idan ka rike Allah,Allah ta ala zai taimakeka ki jajurce da adduoi maryam ki rage wasu abubuwa ki maida lamarinki zuwa ga Allah maryam ta gyad a mata kai alamun taji ,tana nan kwance ajikin mami har ta fara gyangyad i alamun bacci .ahankali mami ta d an buga bayanta tana cewa maryam kwanta kiyi bacci da sannu allah zai kawo mana saukin wannan tashin hankali sannan ya kawo fahimtar juna a tsakaninki da mijinki . maryam ta tashi daga jikin mami tana shafa idanunta sannan ta zame ta kwanta zuciyarta cike da soyayyar mijinta mami ta mike itama ta samu gurin nan kusa da maryam ta kwanta sai dai ita sam bacci yaki d aukarta, kwakwaluwarta ne ya shiga cajin tunani dan dole tasan abun yi tun kafin adamcy ya kashe maryam da bakincikinsa dan zuwa yanzu hakurinta ya fara qarewa akanshi . Juyi kawai mami take akan katifa kafin ahankali ta taashi ta sauko daga saman katifa ta tsaya gaban maryam tana kallon fuskarta bacci take, sai dai kana kallonta zaka san a matuqar wahale take baccin dan kana kallon yadda take sauke numfashi da ajiyar zuciya da karfi . auke kwayar idanunta mami tayi ta fara zagaye d akin kafin ta fara zance zuci ita kad dan dole zulai kiyi wani abu akan zaman ya yanki to mai zanyi ?mai zanyi ? ta tambayi kanta har sau biyu tana cure hannuwanta waje d aya Kiyi qoqari adamcy ya kusanci maryam ko Allah zai basu rabo wata killa sanadiyyar hakan ya sauko ya sausauta mata ya rungume aurensu. tabbas haka zakiyi zuciyarta ta bata wannan shawarar to ta yaya zan masa magana ya fahimci abinda nake nufi ? ta sake jefawa kwakwaluwarta tambaya shiru tayi yayinda ta koma ta kwanta akan katifa tana sauke numfashi tana mai sake had e hannuwanta guri d aya kafin ahankali ta soma sakin wani irin murmushi sakamakon abinda zuciyarta ta shirya mata wanda zai kawo mata saukin al amuran ta, alokaci d aya ta sauke wani naunayen ajiyar zuciya dole dai kina bukatar shawarar shahida kafin ki aikata komai . Washegari da misalin karfe tara na safe maryam tana zaune akan kujerar sofa tana danna waya yayinda mami ke zaune akan salayya tana lazimi ATA ya shigo bakinsa d auke da sallama sallamarsa kawai maryam ta amsa batare da ta kallesa ba ta cigaba da daddanna wayarta shima ko kallonta bai yi ba ya cigaba da tsayuwa mami ta d an kallesa yana sanye da jallabiya yayi mata kyau sosai sai dai bata jin dadin ganin yadda ko yaushe fuskar nan tashi take a had ,sannan bata jin dadin ganin shi da maryam haka zaman su sam babu sha awa kana ganin yanayinsu kasan gabad aya zukatansu basa cikin walwala da jin dadi most especially adamcy wanda zaka fahimci baya son ko bisa kuskure ya kasance a duk inda maryam take .yayinda ita kuma tafi qaunar su kasance tare akoda yaushe ya rungumeta babu kyama ,mami na kallonsa ya juya cikin takun isa ya fita daga d akin ganin tana lazimi ,bayansa mrym tabi da kallo har ya fice gabad aya tasa hannu d aya ta dafe goshinta tana jin wani tuttukin bakinciki tana jin zafi da ciwon abinda yake mata na kyarma da rashin son kallonta inda take ,amman ita ta rasa dalilin da yasa zuciyarta kullum take sake macewa akanshi ,a kullum zata d aura kwayar idanunta akanshi to wallahi son shi da qaunarsa ne Ke sake huda zuciyarta da gangar jikinta zata so ta mallakesa kamar yadda mahaifiyarta take buri amman hakan taki samuwa kullum babu abinda take hangowa attare dashi sai zallar qiyayyarta sam komai nata baya burgesa ita kuwa kwarjininsa kesa bata iya d aukarwa kanta mataki ,bata iya tunkurarsa da komai tana matuqar jin tsoronsa aranta da sanyi jiki mami ta qaraso inda take zaune ta kai hannunta ta dafata, ta d ago tana duban mami da idanunta dake cike da ruwan hawaye mami tasa gefen hijab dinta ta goge mata hawayen da suka zubo mata batare da saninta ba wani wahallen ajiyar zuciya ta sauke tana kawar da fuskarta gefe maryam ! Mami ta kira sunanta ahankali maryam ta waigo inda mami take ta sake zuba mata idanunta tana kallonta fuskarta da tsananin damuwa ahankali ta sauke idanunta ki daina damun kanki akan adamcy idan ba haka ba zaki rasa lafiyarki idan hakan kuma ta kasance babu ruwansa hasalima bazai ta ba zama damuwarsa ba sai dai ta zama damuwarmu kiyi hakuri ki dinga kawar da damuwar nan aranki sannan ki dinga kaiwa allah kukanki ,nasani maryam kina hakurin zama da adamcy ne saboda Kina matuqar ganin girmana da mutuntani da kuma qaunar da Kike masa nima kuma haka ne acikin zuciyata maryam ina qaunarki ina qaunar ku kasance a inuwa d aya dashi . numfashi ta sauke da karfi tana kallon mami eh shine ma dalilin da yasa bakya son na rabaku maryam . Maryam ta tsurawa mami idanunta ko karya ne bakya sonsa ?zazzafan numfashi maryam ta sauke ta kasa cewa komai dan tasan gsky mami ta fad kina dai danne sonshi ne saboda rashin qaunar da yake nuna miki amman ni naji ajikina kina qaunar adamcy ,maryam taji dadin yadda mami ta fahimci hakan sai dai kuma zuciyarta tayi rauni wasu sabbin hawaye suka zubo mata mami ta sake share mata kuka bayayi miki kyau maryam hakan ya sake karya wa maryam gwaiwa ta fashe da wani kuka sosai . wallahi mami ban san lokacin da son shi ya shigeni ba nice silarsa maryam kuma nayi danasani had aku aure ,mami ta fad a da matsanancin tausayinta ,duk yadda mami take jin qaunar adamcy ji take tafita qaunarsa maryam ta tsananta kuka tana tuna tun lokacin data fara jin qaunar yaya Adam din acikin ranta rungumeta mami tayi tsam tana rarrashi alokacin wayar maryam ta soma ringing mami ta zare jikinta tana kallon maryam itama d agowa tayi ta kalli mami sannan ta kalli screen din wayarta bata dauka ba ta cigaba da goge hawayenta yayinda kiran ya cigaba da shigowa still maryam bata d aga ba . mami ta d an yi gyaran murya wake kiranki ne tun d azu ?ummah ce !ta bata amsa atakaice idanunta na cigaba da zubar da hawaye me yasa bazaki d auka ba kika sani ko kiran mai mahimanci ne ?shiru maryam tayi ta kasa cewa komai dan tasan kiran me take mata, ita kuma ta gaji da abubuwan mahaifi yarta ,kullum abu d aya kuma babu wani biyan buqata ki d auki kiranta kar rashin d aukar kiran yasa hankalinta ya tashi tayi tunanin ko wani abu ne .ahankali maryam ta gyad a mata kai tana cewa mami bari naje na dafa miki ruwan zafi to shikenan maryam amman ki hada min da abinci bamu da komai fa mami ,karki damu ki dafa min abinda kuke dashi . Mrym ta mike tsaye ta fito tana qoqarin d aukar kiran mahaifiyarta daya sake shigowa ta sauko kunnenta manne da waya umma dan allah ki daina kirana na tura miki sako mami tana gidan nan bana son taji komai amman me yasa zaki fad i haka ummah? kema Kinsan mami tana matuqar qaunata a umma nifa gsky na gaji kawai abarshi na hakura bazan iya ba dan duk abinda zaa zuba cikin abinci bazai ci ba tunda baya cin girkina ,shiru maryam tayi tana jin yadda mahaifiyarta ta balbaleta da bala i ta inda take shiga bata nan take fita ba. kiyi hakuri ummah ba wai bana ganin qoqarinki bane saboda mami idan ta fahimci akwai abinda muke shiryawa d anta zata ji babu dadi to shikenan gara ma wannan zamu iya sake gwadawa ko za a samu ya kwanta akai ,to shikenan amman dan allah ummah karki kirani kiyi chart dina muyi komai ta chart ta qarasa mgnr tare da shiga kitchen ta soma qoqarin d aurawa mami abinda zatayi breakfast dashi cikin kankani lokaci ta gama dafa ruwan zafi ta zuba cikin flaks sannan ta dafa shinkafa da miya ta fito tana qoqarin qarasawa dining mami ta sauko tana cewa sannu da aiki maryam ?murmushi ta saki tana cewa kai mami wani aiki kuma byn shinkafa da miya ce kawai na dafa miki. murmushi mami tayi tana cewa kawo min nan diyata ta qarasa inda kujeru suke ta zauna maryam ta biyo bayanta ta ajiye kular abinci akan center table maryam tace nasan idan kowa yaci abincina yace babu dadi mamina bazatace babu dadi ba ? ina sam bazan fad a haka ba zuba min na matsu banji dandanon abincin my daughter ba abincin dai mami sai dai kiyi hakuri babu komai aciki ta qarasa mgnr muryata a sanyaye karki damu maryam fara had a min shayi cike da kulawa maryam take hidima da mami yayinda mami ke nuna mata farincikinki a zahiri amman a bad ani bakinciki ne cunkushe acikin zuciyarta suna zaune ata ya fito yana taku a natse akan step sanye da kananan kaya jikinsa sai fitar da sihirtaccen kamshin turarensa yake ,ya qaraso parlour n qasa hannuwansa duka zube cikin aljihun wondonsa tun daga nesa ya hango mami zaune tana breakfast da ruwan tea zalla babu wani abun hadi danginsu soyayyen Kwai da bread ko arish da sauransu abinda yasan ba d abiarta bace, abun yayi matuqar bashi mamaki dan haka kai tsaye store ya shiga adaidai lokacin maryam ta mike ta nufi hanyar sama d auko chazar wayarta . yana shiga dube dube ya fara bai ga komai ba ya