← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 105

Sashe 11

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

qirjinta tare da fashewa da kuka ,ahankali ta durkusa kasa ta cusa kanta cikin qafafunta tana kuka tare da kankame jikinta ,sai da tayi kuka mai isarta sannan ta mike ta shiga bayi wanka tai ta fito ta bude wordrobe dinta shiru tayi tana kallo babu abinda babu hatta kayayyakinta na gida an kawo mata ta saka kayan bacci wondo dogo da riga mai long sleeve butter colour touch of brown ta saka hijab sannan tayi sallar shaf'i da witiri tayi addua akan Allah ya zaba mata abinda yafi zama alkhairi a tsakaninta da yaya hisham ." sai data rufe kofarta da key ta kashe fitilun dak'in tayi shirin kwanciya bacci , koda ya dawo ya tarar har tai bacci yana murda kofar d'akin yajita gam nan da nan yaji ranshi ya 'baci meye abun kulle kofa tsaki yaja ya juya ya shige d'akinsa ." Washe gari tana farkawa daga bacci tai sallah sannan ta fito ta wuce kitchen, had'adden breakfast ta had'a masu naji da gani bayan ta kammala sannan ta d'auka ta kai dining, d'akinta ta koma tai wanka ta shirya cikin doguwar rigar abaya bak'a mai ratsin ja tai rolling kanta da mayafin abaya sannan ta saka takalmi silifas ja , ta feshe ilahirin jikinta da turare tayi kyau sosai abunka ga farar mace ta d'auki phone d'inta ta fito zuwa falo ." tana fitowa shi kuma yana fitowa daga d'akinsa sanye da jallabiyya brown , cikin sakin fuska ta masa barka da kwana ,wani kallo yayi mata mai hade da harara sannan yaki amsa tsabar bakinciki "meye jiya zaki wani rufe daki ?tayi shiru "me kike tunani akaina ?"still dai shiru tayi masa tare da sunkuyar da kanta kasa "ko gidan nan naki ko kuma da kudin wani naki aka gina shi ?shiru tayi tana nazarin maganarsa ,a wannan shirun datayi ta fahimci inda maganarsa ta dosa yana son ta'bo yayanta ne abinda bazata d'aukar masa ba kenan muddin baya son zaman tashin hankali daita ya tsaya iya kanta kar ya ta'bo mata wani nata ita dai zata jure komai akanta amman akansu bazata iya ba ." Numfashi ta sauke tace "ga breakfast can akan dining idan ka tashi ci ".ta fada haka n dan kawo qarshen maganar sai dai bata kai ga k'arasa rufe bakinta ba yayi saurin cewa "to baa ci ina miki magana kina min maganar wani abinci d'an yunwa kika dauki ne ko me ?" yadda yayi maganar sai da ya gigitata "na fahimci haushin nuzla kike ji a zuciyarki "idan har fahimtata gsky ne wallahi kiyi maza ki cire a zuciyarki daman munafurci ne yasa kikace kin amince idan zan aureta na aureta well idan na tashi aurenta ba amincewarki nake nema ba ." A natse ta durkushe a gabansa tana kuka "karka min mummunar fahimta bazan iya bacci ba matsawar na bar kofar a bude tunda kofar shigowa falo a bude take amman kayi hakuri bazan sake ba maganar nuzla kuma wallahi babu ruwana ko mata goma zaka aura byn ita kana dama "saboda ga dan iska ba ?"ka rufa min asiri ba abinda nake nufi ba kenan yaja tsaki ya juya a fusace shifa ba lalla'ba yake son tayi ba so yake ta biye masa daga nan komai yazo qarshe ." nana hauwa'u ta mike da sauri ta rungumeshi ta baya tana rera masa kuka mai cike da jan hankali "yaya hisham dan Allah ka bari na samu natsuwa a gidan nan idan kuma har baza ka bani wannan kwanciyar hankalin ba kana iya sakina Kmr yadda nace ,sosai ta shige jikinsa tana goga masa dukiyar fulaninta sannan ta cigaba da magana "nasan baka sona amman ni ban ta'ba jin tsanarka ba zan iya mutuwa akanka yaya hisham dan allah me nayi maka da ka tsaneni haka ?"dan allah kayi hakuri ka dain a tsana haka bana bukatar komai bana son kuma daga gareka ni dai mu zauna lafiya cikin sheshekar kuka ta qarasa mgnr." Sosai ta rud'a yaya hisham jikinsa sai rawa yake ya juyo ahankali tana jikinsa ta sake narkewa a qirjinsa "kada ka canza yaya hisham kowa yabonka yake yi akan nayi saar samun mijin da babu kamarsa gurin kyakkwar halayya kana da kirki bazaka ta'ba barin nayi bakinciki ko kuka ba , samunka amatsayin miji ba qaramin nasara nayi ba amman why kake son canza halinka?runtse idanunshi yayi tabbas haka n shi kanshi yasan ya canza amman duk ita ce silar komai da bata amince da aurensa ba dole iyayensu su hakura ." kuka take sosai har da shesheka tausayinta ya kamashi ya soma jin kamar ya bata hakuri ta daina kuka amman ya kasa magana, dago kanta tayi taga ita yake kallo ta matso da fuskarta kusa da nashi ido cikin ido suke kallon juna suna shakar numfashin juna, gbdy wani iri suka dinga ji ajikinsu ya bude baki zai fara magana ta matso da lip's dinta kan nashi tana kallonsa tana motsa lip's dinta akan nashi "am sorry yaya hisham I don't mean to hurt you bansan rufe kofar zai 'bata maka rai ba da ban rufe ba "ta fad'a tana kamo lip's dinsa ta shiga tsosa cikin salo kamar ta samu sweet ,cikin son qara rusa shi ta kamo harshensa tana mai wani irin sha tana goga masa qirjinta ." wani nishi yaya hisham ya saki cikin fitar hankali da mamaki ya zare bakinsa yana j baya tare da cewa "meye haka ?ya fad'a Kmr bai ji dadin abinda tayi ba sunkuyar da kanta kasa tayi tana mai jin wata irin kunya "kayi hakuri" lumshe idanunshi yayi yana jin wani sanyi na bin jikinsa "muje kaci abinci dan allah ba dan ni ba" bai ce uffan ba suka wuce dining a tare itace tai saving nasa sannan ta zauna ta d'auki spoon ta kai bakinsa "bude bakinka na baka da kaina mamakin abubuwanta yake wani lokacin ta nuna masa Kmr tana son shi wani lokacin kuma sa'banin hk most especially idan tace ya auri nuzla ita kuma ya saketa ko ya qara wasu matan ma a bayan nuzla yasan ba so bane kawai biyayya takewa mahaifiyarsa " Tana bashi abinci shi kuma sai kallonta yake wani irin bak'inciki yake jin yana taso masa da takaicin bai wani ci sosai ba ya tashi ya wuce, tabi bayansa da kallo har sai da ya bace mata sannan ta daina kallonsa tana jin fad'a uwar gaba ta d'auki wayarta ta soma chart din maryam ."tana zaune ya fito cikin shirin fita aiki tayi masa adawo lafiya ya amsa ta hanyar taga mata hannu ,yana fita ta sauke numfashi ta kira maryam domin taji muryarta dan chart dinta ya nuna mata tana cikin damuwa ". "kiyi hakuri dai sister har sanda ubangiji zai kawo mana mafuta ta alheri ,In sha Allah zaku daidaita da yayana, ni dai fatana kullun kenan ubangiji ya daidai taku damu gabadaya ."wallahi babu wani gara ni sister nima hakuri nike yaya hisham ya canza sosai fiyye da tunaninki ,duk babu wannan fara'ar da wasan daya saba mana Ke wallahi tsoro ma yake bani ga damuwa ta qaru daman ba wani samun kanshi nike ba bare yanzu ga farincikinsa ta dawo jiya fa na tare a gidan nan amman ina ji kuma ina gani nuzla ta kirasa kuma ya tashi yaje ,t ya zanyi sister bai dameni ba dan na auresa ne tsakanina da allah kuma nuzla yaruwata ce da nake so da qauna "ahankali suka cigaba da tautauna akan abinda ya shafi matsalarsu ." a round 6pm bayan sun tashi daga aiki ya kamo hanyar gida saboda yau agajiye yake sosai yana buk'atar hutu ba zai iya zuwa gidan mumy ba ko wajen nuzla."yana isowa yayi horn gateman ya bud'e masa ya shigo yayi parking sannan ya fito tana zaune parlour'n sanye da wasu kaya ba wanda ya barta dasu ba ,tana ganinsa ta mike da sauri ta rungume shi ajikinta sannu da zuwa "yauwa !" ya fad'a atakaice yana qoqarin zareta ajikinsa dan bazai iya misalta yanayin da yaji ajikinsa ba ." zata amshi jakar hannusa ya hana ya shige d'akinsa d'akin tabi shi alokacin ya ajiye jakar hannunsa ta shigo ta tsaya gabansa zata kai hannuta jikinsa ya rike yana cewa "out pls "Kai tsaye fita tayi ranta a b'ace tamkar wacca akayiwa mutuwa, tana shiga dakinta kiran maryam ne ya shigo wayarta ahankali ta dauka kuka ta fashe mata dashi tana furta "sister zuciyarta ta fara min zafi ". duk hankalin mrym ya tashi tana tmbyrta "sister mun jefa rayuwarmu cikin qangin rayuwa kuka take sosai maryam na rarrashinta ." ******* Mami ta kira ya'yanta mata kan tana neman su a washegarin ranar suka kamo hanya suka zo nan mami tayi masu bayanin abinda yasa ta kirasu batare da bata lokaci ba suka amince aunty khadija tace "ai idan bai yarda ba mami ki bud'e masa wuta ,uhm uhm !! aunty khadija kin fa san halinsa mu dai bi ahankali idan aka bishi ahankali zai iya amince wa "inji cewar zabiba "wannan zaa bi ahankali ai shikenan a kirasa " babu 'bata lokaci aunty shahida ta kirasa kasancewar weekend ce yana gida ya shigo cike da izza fuskar nan tashi a had'e tamkar ta zaki yana shan kamshi". " adamu !"aunty shahida ta kira sunansa tare da mikewa daga zaunen da take ta jawo hannusa ta zaunar dashi bisa kujera itama ta zauna akan kujerar data tashi , cikin wani irin yanayi mai cike da tashin hankali da tsoron abinda suke shirin fad'a masa ya kalli mahaifiyarsu kana ya juyo ya kalli aunty shahida ,yayinda gefen hangunsa aunty khadija ce wacce fuskarta tafi ta sauran hadewa sai zabiba ya zuba masu ido yana kallonsu da sauraronsu cikn yin kasa da murya aunty shahida ta soma magana "yaushe zaka tare a sabon gidanka musan ranar da maryam zata tare ?". Gabansa ne ya shiga fad'uwa cikin tashin hankali yace "me yasa kuke da damuwa ne ?ya fad'a tare da jan sayayyen numfashi ya gyara zamansa yayinda ganadayansu har mami kacokan suka maida hankalinsu kanshi duk hankalinsu a tashe yake kar ya shigo masu da wata matsala ."wani numfashi ya sake saukewa kana ya cigaba da motsa lip's dinsa "da gidana da nan duk daya ne a wajena dan haka
Chapter 11 · 0% Book details