Sashe 80
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
motan Salim yayi kofan yadaki cikin John sosai yakoma baya, saukowa yayi bai damu da ruwan da akeba yamaida kofan yarufe yayi folding hannunsa a kirji cikin kakkausan murya na marasa imani yace what are you doing in my house when I m not around? Dasauri John yace nothing Sir! Tundaga kafa Salim yake kallonsa ruwa fa ake dudda ba sosai ba but rain is still dropping and harya jikema that means immediately yafita yafito dan inda ya basa na kwana as boy nasa daya biyosa is directly opposite gidansu probably yaga fitansa yataho, wani kalan tafarfasa zuciyan Salim yashigayi zuciyansa yafara komawa baka kirin yamai wani uban ihu da saida kap estate din yadauka. I said what are you doing here Sargent! Awani irin firgice Safeerah dake bacci tafarka sabida muryan Salim dataji yana ihu dako ina ya amsa, kirjinta yawani kalan buga dudda tanajin azaba batasan sanda tawani jumping tasauko daga gado ba abayanta fake kasa tadauka tazura babu komi cikin jikinta tabude kofa tafito Fitowa sojoji dake base din sukayi dan anji muryan Salim they have no right to intervene cus Major ne yayi ihu saidai only wanda yafisa mukami ne zai iya shiga case din, yanda gaban John ke faduwa jiyayi kaman tashi takare today and the plan was not like this daka plan din was yashiga gidan Salim yazo ya gansu in compromising position abinda AJ yafada kenan. Kallon Salim yayi gabansa na bugawa sosai amman ya daure yace Sir Ma .Madam ce taki ..ki Madam ce takirani Sir! Chak kawai numfashin Salim ya tsaya everywhere kawai yazaman masa baki! Daidai Safeerah na zuwa wajen kofan taji ana Madam ce takirani, wani irin fizgo John Salim yayi yakama gaban rigansa ya matsesa yana kallon kwayan idanunsa da kyau sabida yagane karya yake ko gaskiya yake fadi cikin wata kalan muryan bala i dake cike da zuciya yace wace Madam? Sosai John ya tsorota cus Omoh he s not ready for death but juyawa dayayi yaga sojoji tako ina yasan baza a taba bari ya kashesa ba and duka dai duka he can handle that shi soja ne, hakan yasa yakalli Salim yace your Madam Sir, Ma am Safeerah called m wani irin daga John sama Salim yayi gabaki daya like sama yakama kafansa daya a hannusa kaman yarike ganye kawai yakawo yabugasa da mota saida glass na motan ya fashe kan John na shiga ciki jikake ratstsarrarrrrr! Safeerah tabude kofa da gudu kanta ba dankwali daga ita sai abayan ba bra ba pant just abaya, ta kalli wajen glass na motan yafashe glasses gabaki daya akan John da wuyansa da fuskansa, come and see blood jikin Safeerah yafara rawa bata taba ganin abu haka in her life ba, wlh akan idanunta taga yasake fizgo John din kawai yakama hannunsa yama hannun wani irin duka da bata taba gani ba jikake balllll! Hannun John ya karye yafara liloooo John yayi wani kalan azababben ihuuuuu Salim yayi ihuu kaman wanda baida hankali yace who did you say call you? Kaman daga sama dudda yana cikin azaba yanuna Safeerah da Salim bai gani ba yace gatanan she s here to open the door for me! She called me Sir I have evidence on my phone kaduba wayana! EPISODE 8 Kun gane irin tsoro yashigeka ganin ana dukan kisan kai agabanka, saikuma ahau wasu maganganu dakaji ana kiran sunanka da bama ka tantance exactly what is going on ba shine state da Safeerah ke ciki, jinin datagani jikin John na fitarwa da yanda Salim ya ballasa agaban idanunta yasa brain dinta yama kasa gane komi, Salim bai kalli Safeerah da John ke nunamai ba sai kawai yasaki John yasa hannu yadauki wayansa dake aljihu yaciro yashiga call log, sabon number daya sayama Safeerah da kansa yasamata a sabon iPhone daya sayanata yaga ta kira ita tai kiran ga call history na about 55seconds bai karasa one minutes ba, bawai yana tunanin wani abu bane ko zarginta bane no but how dare she takarbi number yaron aikinsa, how dare she call him, how dare she talks to another man sakin wayan John yayi akasa jikake rakasasaaaa! Ta fashe yajuyo kawai yaga Safeerah tsaye chak gaban kofa sanye da black gown ba hula ko dankwali akanta, Ya Allah, kan Salim kwancewa yayi idanunsa namai wani kalan black out bayaji baya gani kawai yawani taho kaman zaki Safeerah batasan sanda tasaki kofa tajuya dawani kalan gudu ba ina tama manta da ciwon da gabanta keyi tahau hawa bene amman takasa sauri sabida azaba, daidai tanakai karshen last stair case din Salim na isowa ya cimmata yawani fizgota baji ba gani jikake tasssssss! Yadaurama Safeerah mari dayasa kawai taga jiri kanta na juyawa dabadan ya fizgota ba wlh da sai ta zubi tai rolling a staircase dinnan tsabagen yanda marin ya isheta, jikin Salim is literally shaking, muscles dinsa were having spasm kaman an makala shocking ajiki yarike mata hannu gam yace are you trying to show duka soldiers din jikinki, get naked and step outside ki nuna musu, do it Safeerah Shu ibu Salim! Yayi Ihun da saida gidan ya amsa gabaki daya fitsari kawai yashiga bin jikin Safeerah, tafashe da kuka bana wasaba ta mugun mugun tsorata cus Salim looks kaman zai kasheta, hannunsa biyu yakai duka wuyanta yashake yace when did u collect number yarona why did you call him ? Jijjiyoyin wuya da kan Safeerah fitowa sukayi tana dukan hannunsa tana tari tana feeling kaman zare ranta ake tashiga juye juye suna wajen stairs bataga komi ba, idanunta ma suka fara juyawa tana dukan hannunsa sosai baya sakinta, da kyar tai dabaran kai hannayen nata fuskansa tana dukansa ina bamayaji, cikin wata irin zuciya yace you are mine Safeerah! Only mine! Idan you don t want me zan kasheki na kashe kaina! I will kill us! As long as ina raye nobody can have you! Ganin baya motsi yasa tasaka yatsunta a idanunsa hakan yasa yasaketa tahau tari tana grasping breath takallesa ganin yana kursa idanunsa biyu tashiga rarrafe tayi hanyar dakinsu daidai nan yabiyota yanajan belt na jikinsa ta tura kofan tarufe tasa key tafashe da kuka tana tari sosai yazo wajen kofa yashiga buga kofan sosai. Open the door! Open the door nace! Saina kasheki! Wayace kiyi magana da John jiya! You lied to me! How dare you take his number yanda Salim yake buga kofan ganin kofan yafara motsi kaman zai fado yada tadauki wayanta dake kan gado hannuwant na rawa tarasa mema zatai dashi wazata kira Mama takira amman har wayan ya katse Mama bata daukaba same with Baba shima bai dagaba Salim na buga kofan zai fado hannunta na rawa tai dialing number Ammi a ringing na biyu Ammi tadaga daidai Salim yasauke kofan nan har kasa saura kadan yafado kanta tai bayi da rarrafe tayi tura tana sa key tana ihu. Mamaaa, Mama zai kasheni, Innalillahi Wa Innailaihi Raji Salim na buga bayin Safeerah bamatasan Ammi tadauki wayanta sabida yanda take kallon kofan, Ammi magana take. Safeerah Safeerah shi kansa Daddy dake gefenta saida ya kalleta yace meya faru dasauri yacire wayan tasa a speaker yace innalillahi something is happening Alhaji ihun Safeerah sukaji tana Mama zan mutu zai kasheni, ga buga kofan abu sunajin muryan Salim na cewa tabude kofan dawani irin sauri Dady yashiga kiran wayan Salim amman ina baya dauka while Ammi na Safeera Safeerah ina bataji, Dady yashiga kiran KB ringing daya yadaga yace KB kana PH da Salim? Dasauri yace yes Dady but bama quarters daya Dasauri Dady yace something is happening KB tafi gidansa yi maza karya kashe yar mutane Dasauri yace toh sir Da gudu KB yafito daga quarters nasu next line ne nasu Salim kafinma yashiga yaga sojoji dasauri yayi ciki ganin John ga Medic an kira ana kokarin stopping bleeding yasa yace what happen gidan Salim kawai aka nuna kai tsaye yawuce yabude ciki yashiga daganan falo yakejin buga kofa dasauri yayi sama direct yawuce bedroom din yana kallon Salim dake buga kofan zai fado ahaukace ga kukan Safeerah abayi ga kofa da Salim yasauke yayi kansa yace Salim juyowa Salim yayi yakallesa idanun Salim kadai yagani saida gabansa yafadi yasan ba lafiya yace Salim wat is wrong with you ? Kansa Salim yayo yace who are you dazaka shigomin bedroom inda matana take? Dasauri KB yadaga hannu yace woh woh woh toh fito muyi magan duka Salim yakawomai KB ya kauce yace common Man, you need to calm down Salim, chill, I know I know, remember she s your Safeerah whatever it is you need to calm down let s solve it okay, Salim chill kansa Salim yayi yace I said what are you doing in my house ko kaima ta karbi number ka ne ? KB yamai wani kallo na looking confuse Salim yace I will kill you KB, Safeerah is mine! Mine alone nobody can have her banda ni aduniya, I will kill her and kill myself yoh hear me yasake kawoma Kabir duka ya kauce suna fitowa nan falon sama sai shima KB yakawomai duka like the fought kaman suna arena yanda suka sabayi a wrestling sannan cikeda dabara yadan ne Salim da kyar shima danya tabamai idanu ne sannan yazare handcuff yasamai yakamasa da kyar yayi second bedroom na wajen dashi da karfi da yaji yabude bathroom na wajen yasakin ma Salim ruwan sanyi sannan yafito ya kulle bayin kawai yaciro wayansa yana Koran Dad yawuce dakin yayi knocking anatse yace Safeerah open the door is Kabir Safeerah taki bude kofa sai kuka bata yarda Salim baya wajen ba, daukan wayan Dad yayi atsorace yace Kabir meke faruwa dakin yabi da kallo kafin ahankali yace Daddy zaka iya zuwa Ph da Mom Salim is not okay, bansan meyama wife nasa ba but ta kulle kanta a bathroom, while yajima driver sa ciwo sosai I m just praying John makes it salati sosai Dady da Mommy sukayi Dady yace meke faruwa meya hadasu? Anatse yace I have no idea Dad, kawai kuzo yanzu da kyar na sakasa a handcuff na sakasa a bayi na kulle ya jijjimin ciwo ma, you guys should come kawai yana maganan ya katse wayan yasake buga kofan yace Safeerah! Taki amsawa sai kuka datake sai