Sashe 11
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
M SHAKUR EPISODE Bude kofa yayi yafito daga dakin ya sauko kasa Daddy kadaine a falo yana bude wasu files yana signing ga glass a idanunsa Baffa yariga yatafi, anatse yace saida safe Dad dagokai Daddy yayi yakallesa yace kaima saida safe Alhaji Salim bude kofa yayi yafice batare daya kara wata magana ba Daddy yasake kadakai yadauki files yacigaba da signing dayake yi. Wayansa ne yafara ringing cirowa yayi daga aljihu Nanah ce, katsewa yayi yakirata back ringing daya ta daga tace Baby dan Allah ka kulani wlh kewanka nake baice komiba ahankali chan yace ya su Mama ? Ahankali tace fine tanachan falo kasan yan uwanta har sun soma zuwa daga Katsina, Baby sai maganin mata aketa bani tayi maganan tana rage murya, yace wat is that ? Yayi tambayan da zuciya daya, baya wani hira da ita itakuma babu abinda takeso kaman taga yana zance da ita, bala in mahaukacin son Major Salim take gani take she s the luckiest girl on earth, ga kudi, ga kyawu, ga gayu, ga ji dakai, ga aji ga ilimi, lankwasa murya tayi tace Baby kagani ko idan za ama mace aure an samata rana ana bata magunguna haka dake gyara jiki, suna cire ciwon sanyi, suna saukar da ni ima ajikin mace kuma zaisa miji yayi na am da ita zakaga idan an tashi bikin Ameerah da Lubna za a basu maganin mata yace I don t think Ammi tasan shi dan dariya Nanh tayi yau wlh yabata dariya wato namiji namiji ne, kasa daurewa tayi tace Baby wlh I love you so much, ina mugun mugun sonka! You are so innocent, I can t wait to officially zama matarka, I promise I m going to be the best wife to you wayan na kunnensa baice komiba yakai dakinsa yacire wayan a kunne yasa a speaker ya ijiye kan gado yana rage kayan jikinsa jin shiru tace zakazo ka ganni gobe? yabata amsa atakaice kafin ahankali yace s see within the week kaman zatai kuka tace okay anatse yace I have to shower, daganan zan shiga gym murya chan kasa tace zaka kirani kagama? Ahankali yace okay! Yasa hannu ya katse yawuce closet nasa ya ijiye kayan daya cire yadauki wani short na nike da singlet na nike black yasaka hand gloves yasa sneakers yafito yasauka kasa yabude wani daki gym ne yahau kan treadmill yafara gudu na bala i kaman a highest yasaka yakai kusan 20min sannan yasauka yayi press up yadaga karfe yadaga rope kafin yaje punching bag yasaka fighting gloves, one of his hubby is boxing he loves it a lot, yayi punching bag sosai kusan 2hours yabata sannan yagama yana zufa sosai yakalli agogo is 12:20 yafito yawuce sama, kaya yacire yafada bayi yayi wanka yafito he wants to smoke but bayayi agidansu kwata kwata out of respect for iyayensa kwanciya yayi agado alkawarin dayama Nanah yatuna hakan yasa yadauki wayan even though yana tunanin tayi bacci yakirata but harya katse bata daukaba hakan yasa ya katse wayan ya ijiye yayi shiru tareda lumshe idanu he s just seeing that little girl face data taimakeshi as usual dan babu ranan da baya gani yazo bacci, he s not sure takai 16yrs ma she will not pass 15yrs, this is 5yrs probably yanzu she s 20yrs haka, there s this guilt dayake feeling koma ina take yanzu aduniya itada iyayenta shiya sakasu in it, shi ya jazamusu, banda yaransa dayasa sukai bincike sama da kasa shi da kanshi saida yayi tattaki yaje garin yaje layin but gidansu is still burnt, even though that neighbor nasu ta sanar dashi ba a kona dasu ba but anma Babanta shegen duka sunje asibiti daganan ne basu kara dawowa ba he went to the hospital akacemai an basu bill but basu dawoba bakudi, his mind is not at ease baitaba samun abinda ya tsaya mai araiba sai this, murya chan kasa yace where are you!? Nurse Safeerah! Yayi maganan ahankali yadan fuzar da iska yajuya gefe yakai hannu yana kunna side lamp yana kashewa lost in thought. Yarinyar is the most brightest girl he s ever seen in his life, the kindest, she has the most precious heart, she saved his life, zuman data shafamai was wat saved his hand not hospital, yakasa manceta the way she genuinely cried for him sabida taganshi in pain no one has ever done that ko iyayensa though baisani ba maybe dan baitaba wani major ciwo bane, but this particular guy makes a huge space a zuciyansa, sabida her kindness, free spirit and care, he just wanna know she and her parents are fine! He wants to take care of her! Support her, and gives her whatever her heart desires, gashi duk ba asan daga ina sukeba, har school da aka cemai Babanta na koyarwa wani primary school haka yaje school dinma basu da information na background na Babanta cus is not standard school principal din dai tacemai yan Maiduguri ne, ahaka bacci yayi awon gaba dashi. Mama tashigo dakin ta tadata da kyar ta tashi zaune takalli Waleed dake bacci abinsa one thing about him baya tashi da wuri dan baya bacci dawuri itakuma bata samin enough bacci dan bata isa tayi bacci ba sai Waleed yayi duk kalan gajiyan jikinta yanzu ma da kyar ta tashi, bayinsu tawuce ta shiga brush tafara yi sannan tayo alwala tafito tasaka hijabi tayi sallan asuba, one thing is tunda suka dawo gidan nan batada karfi da ikon zama kayi azkar bayan salla saidai kayi a tsaye dan zasuje main flat girki da gyaran gida, mikewa tayi ta linke dadduma tana enchanting morning zikir nata tazo wajen gado tadan lullube Waleed sannan ta shafa fuskansa tana murmushi tamike tabude kofa tafito tabude kofa tafice, flat din tashigo duk suna bacci basa tashi sai around 9, 10, 11 wata rana har 12 ma ko 1 na rana, kitchen tawuce taga Mama awajen tafara hada abinci tace Mama kibarshi zanyi komi murmushi Mama tayi tace wuce kije ki koma bacci Waleed bai barki kinyi bacci dawuri ba murmushi tayi she has the best Mom wlh, Mama zata iya dauke duk wani wahalan duniya dan kawai ta huta, tazo wajen Maman tasa hannu ta karbi waken tace kosai za ? Murmushi Mama tayi tace eh da kunu, sai pepper soup na kayan ciki gashinan cikin pressure pot, tunda kin karbe girkin bari na gyaro gidan ni dasauri tace Mama duk zanyi w hararanta da Mama tayi yasa bata karasa maganan ba tadauki tsinstiya tafice itakuma tashiga aikin tana tunane tunane yanzu haka Baba na chan compound yana wanke cars, watering plant, gyaran grass and sweeping, tsayawa tayi gaban sink din takalli window gari yasoma haske takalli sama azuciyanta tace Ya Allah baka bacci, I know Mahaifina baida sana a yanzu baima da hanyar yin sana ar sabida idanunsa baya gani sosai ko gidan nan sabida he s familiar with the sorroudings ne saisa yake komi, Mama na is helpless woman da batai karatu ba, I m all they got Ya Allah! Look at our lives slaving for people da basa appreciating namu ko mana godiya they said this is our payment na ciyar da mu dasuke tadan fuzar da iska tace Ya Allah karka dawwamar damu ahaka! Ka yantar da iyayena, kabani source na taimakonsu, duk inda zanje IT Ya Allah kasa suna biya nasami wani kudi hawaye ne ya sauko idanunta takai bayan hannu ta goge tacigaba da aikin sosai, Mama tagama gyaran falon ta duka tana saka turare taji karan bude kofa dasauri tajuyo Momma ce sanye cikin wani bubu mai mayafi ga charbi a hannunta tanaja fuskanta ahade kaman wacce ke shirin dambe takalli Mama ta zubar, Mama tamata murmushi taduka cikeda girmamawa tace barka da saukowa Mama Kubra, ina kwana kiramin yarki Momma tafadi awulakance tashi Mama tayi tawuce kitchen tabude kofa tace kizo Safeerah ana kira hannunta ta goge tarage gas tabiyo Mama suka fito ganin Momma tawuce ta duka tace ina kwana Momma kallon banza Momma ta mata dasauri Safeerah tasauke kanta kasa, Momma ta tabe baki tace anyways jeki shirya 8 Shamsu zai kaiki inda zaki fara IT, kibar aikin Uwarki takarasa wani abu Safeerah taji a kirji ta daure ahankali kanta na kasa tace Momma zan iya gama komi before time aiki yama Mama yawa gakuma Wale Feerah! Mama takirata cikin kakkausan murya dayasa Safeerah tai shiru bata karasa maganan ba, Mama tadan gyara magana tace yaran yanzu basu iya magana ba wani shirme kike gaya haka Safeerah ? Kada kafa Momma tayi tana kallon Mama tace ke Amina nizaki gwadama makirci? Ohhh wato ke kin kasa gayamin a fuskana aiki yamiki yawa sai ki turomin yarki dasauri Safeerah tace Momma wlh bahak Hannu Momma tadaga mata sama sannan takalli Mama tace na ciyar da mijinki na ciyar dake, na ciyar da yarku na ciyar da jikanku, nine tufafinku, abin shanku, kunzgunku, abincin jikanku, nine makarantan diyarku private university, kin dauka ina kashe uban kudin nan zan bar masu aiki agidan nan ne? Menene amfaninku? Shu aibu kanina ne jini daya kuma, da babuni da ina zaku? Sabida na rufamuku asiri namuku rumfa da sutura eh shine zaki bama yarki sako aiki yamiki yawa? Ahankali Mama tace kiyakuri Mama Kubra kuskure ne kawai da shirmen yara yasa Safeera ibu! Shu aibu! Momma tashiga kiran Baba ranta abace kaman daman jira take daga tsakar gida ya amsa yashigo gidan da gudu hannuwansa duk kumfa yana tsiyaya anan falon Momma tamai wani kallon banza da takaici tace shashasha bakasan zaka goge hannu kafin kashigo min falo ba runtse idanu Safeerah tayi zuciyanta namata daci yanda ake zagin mata iyaye agabanta, Baba dasauri yashiga goge hannuwansa ariga yace yakuri Mama Kubra, gani kin kirani cikin fushi tace Matarka Aminatu tayomin aike da yarku yanzu take sanar dani wai aiki yama uwarta yawa dasauri Baba yace Subhanallahi wani irin magana ne haka nakeji Aminatu, Safeerah Mama zatai magana Momma ta dakamata tsawa tace lemme finish Mama tai shiru, Momma tace dan haka ka tattara matarka da yarka da jikanku kubarmin gidana yanzun nan faduwa gabansu yayi dasauri Safeerah takalleta tace Momma dan Allah kiyakuri Mama tace Mama Kubra dan Allah kiyi hakuri wlh aiki baimin yawa