← Book details Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 93

Sashe 15

Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba, tasowa yayi daga kujeran ya zagayo yadan taho ta sauke kanta kasa gabanta na mahaukacin faduwa bai karaso inda takeba but hakanan taji gabanta na faduwa sosai yamata bala in kwarjinin ga wani irin kamshi dayake wanda tunda Allah ya yota bata tabajin turare mai kamshi irin nasaba dadin tsiya, zafi taji kawai tanaji zufa na keto mata kaman ba AC a office din, sai tadanja baya takoma jikin sofa na kujeran takifa kanta ahankali kan kafafunta ta rungume kanta kunya duk ya kamata da tsoro da fargaba ga zufa tanayi gently yaduka bayan takoma jikin sofa yakai hannunasa yadaga kujeran yakama kafan yazaro gyalen ahankali yajuyo yakalleta kadan sai kawai yataso batare daya kalletaba yamika mata veil din yace take dago da kanta tayi ahankali ganin baya kallonta yasa ta karba tamike da sauri tafice kaman ana ingizata ta maida kofa tarufe tai wani ijiyan zuciya tana zaro idanu sosai sannan tacigaba da tafiya bata tabajin faduwa gaba kaman na yau ba dawani irin tension zufa sosai tayi fa, and also tunda Allah ya halitto ta duniya bata taba ganin mutum daya mata kwar jini kaman wannan mutumin ba, to kodon shine mai this big company, his eyes, the ways he looks, talks, the way his body moves and everything just enforces authority, bene tashiga sauka harzuwa na daya tama rasa inane hanyan office nasu da kyar ta gano tabude kofa tashige babu wanda yamata magana kujera ta takoma tazauna tana shafa kirjinta sannan ta fuzar da iska natsuwa yadan soma shiganta kafin ta dauki files tacigaba da aikin, kuka cikinta yayi mai kara da sauri tadago kanta takalli gefenta ganin kowa na aikinsa yasa ta maida kanta gabanta tacigaba da aikin wondering karfe nawa ake tashi, wuraren 4 saura taga yan office din na hada kayansu dasauri takalli Madam Maimuna tace an tashi? Murmushi Madam Maimuna tamata tace yes an tashi, kema hada kayanki kitafi bani files din, kinyi seprating wanda kika shugar da wanda baki shigar ba? Ahankali tace tamika takaimata ta amsa sannan tadawo tadauki jakanta tayi kofa tana tunanin kudin mota ko biyar batada shi cash, fitowa reception tayi tabude kofa ahankali tafito daganan inda suke zuwa gatema tafiya ne hakanan tashiga tafiya abinta tana kallon ma aikata na shiga mota some machine suna tafiya abinsu kaman ta nemi lift but zuciyanta yaki aminta she s new she just starts today ficewa gate tayi tasa kafa ahanya hango POS umbrella joint a chan nesa yasa tashiga sauri ta tsallaka titi taje wajen jakanta ta sauke taciro kati first bank nata tamika tace dubu biyar zan cire mutumin yace 200 charges na cire a ciki zaro idanu tayi tace 200 charges a dubu biyar haba dan Allah naira dari ne fa ko a school mutumin yace anan 200 ne Hajiya idan bazaki cire ba sai kije school din kicire bala in bata mata rai maganan sa yayi so rude, batasan sanda tamikamai hannu ba tace eh gwara nacire a school tunda baka iya magana ba katin yamika mata ta fizge tawuce ranta ya mugun baci idanunta sunyi ciki wannan coffee da Cookie ne acikinta, tacigaba da tafiya, gashi bata sake ganin wani mai POS ba harta fito daga anguwan gabaki daya tafito express still bataga POS ba dan wajajen kampanin ba area mutane bane gaskiya tashiga tafiya wata bakar mota taga tawuceta tana slowing down sai akai parking tare da sauke glass kasa ahankali tazo zata wuce batare datama kalli cikin motan ba anatse akace Safeerah! Bala in faduwa gabanta yayi da batasan sanda tajuyo afirgice ba ta kallo motan cus he s the least person take expecting, hada idanu sukayi tasauke idanunta ta gudu aranta tace this man again kai tsaye yace shigo dago kanta tayi da sauri suka hada ido wani kallo yamata irin kallon da is not like he s giving her an option kallon command yamata. EPISODE 1 Har cikin ranta bataso ta shiga motan ba it feels so strange but koda wasa bazata iya cewa no yacika mata idanu dayawa, kawai tana wani kalan shakkan sa balle tace masa no, maida kanta kasa tayi tasa hannu tabude motan ahankali tashiga ta zauna atakure wani irin kamshi motan keyi dataji da ace za a ce takarasa duka aryuwanta acikin motan nan zata iya sabida yanda motan ke kamshi. Maida glasses na motan sama yayi cikin motan yayi duhu sai wani sanyi da motan ya dauka, bata taba ganin kalan interiors na mata haka in her life ba sai yau da kyar tadaure tahana kanta kalle kalle, yaja motan bada wani gudu ba, boyayyen ijiyan zuciya tasauke to yanzu address na gidansu zata ce ko mene ya akema Boss magana ma, takalmin sojoji tagani anan inda kafafunta suke soldier ne dagaske no wonder fuskansa babu wani rahama sosai kaman mugu. Your address dasauri tajuyo takallesa but idanunsa nakan hanya maida kanta kasa tayi ahankali gently tace basaina bata maka lokaci ba ka saukeni a next bus stop saina tafi your address Safeerah! Yayi maganan anatse yet he s sounding so dominative, dasauri takallesa wlh gabanta faduwa yake why? Especially da yakira sunanta dan kallonsa tayi titi yake kallo hakan yasa ta maida kanta kasa tace GRA first avenue block 5B tayi shiru tana wasa da yatsunta saikuma calmly tace thank you wani secret ijiyan zuciya yasauke motan yayi tsit kanta na kasa tana wasa da yatsunta wani kalan kuka cikinta yayi that is so loud dasauri ta tura jakan bayanta cikinta tana runtse idanunta cikeda wani kalan kunya abin was so embarrassing tadan dago kanta ta kallesa kadan ganin hankalinsa na kan tuki yasa tadan gyara zama tana hoping baiji kugin da cikinta yayi ba, parking taga yayi gaban wani hadadden restaurant batare daya kalleta yace excuse me stay in the car yabude motan yafita tabisa da kallo dasauri kawai ko is because he doesn t look like someone that can harm her ko ya cutar da rayuwanta ko yamata wani bad abu da tuni tagudu, almost 5mins yabata aciki yafito saiya zagayo ta kofanta bamata lurada shi ba kawai taji an bude kofan a firgice tajuyo hada ido sukayi tadauke kanta da sauri instead of yamika mata sai ya ijiye paper bags din agabanta akasa wajen da kafanta yake yace next time eat a cafeteria a company, I don t want my employees staying with hunger am I clear? Gyadamai kai tayi batare data kallesa ba ya maida kofan yarufe yazagayo yashiga mazaunin dreba ya kunna motan yaja, kasa taba abincin tayi and bala in yunwa takeji bai sake magana ba har suka shigo GRA, sukaje first Avenue din kaman tace yasauketa daga bakin street nasu but takasa, haka yashige tun kafin sukai ta hango Baba dake zaune kofar gida kan wata yar plastic chair yasaka wata shadda brown data kode sosai, ta kafadan har yasoma zama kaman milk milk, kansa da hula ga yar radio karama rike a hannunsa yaja antenna sama yana saurara, baya gani sosai, sometimes baya gani kwata kwata, he understands environment nasa yasan sound kuma, jin karan mota coming towards kofar gidansu yasa yarage volume na radio kunnuwansa nawani budewa jin ba motan gidansu bane yasa yamike tsaye dasauri ya ijiye radio a kujeran yadaga hannuwansa alamun motan ta tsaya yace wa ake nema? Parking Salim yayi ahankali batare dayamayi kwana kaman zai shiga gidan ba dawani irin sauri Safeerah tabude motan tafito bata dauki abincin ba tace Baba nine wani murmushi sosai Baba yayi yamiko mata hannunsa yace Mamana an dawo daga IT ya wajen? Kika tafi yau kina fushi da Babanki haka akeyi duk na damu saisa na zauna anan naga shigowan ki, an dena fushin ? Hannun Baba takama tamai wani cute murmushi tace nadena fushin kawai ni banso Salma na zaginka agabana ne Baba ka kwadeta babu abinda zai faru Baba yace waya kawoki? Motan waye anan ? Juyowa tayi da sauri adan rude Baba yasa hatta mance suna tare tarasa mezatace daidai Salim na fitowa daga motan rike da paper bags na abincinta, Baba yajuyo yana dan gyara kunnensa trying to read step na mai zuwa da kamshin yace waye Safeerah ? Cikin mutunci da girmamawa yace nine Abba, Salim ne dasauri Baba yace Salim? Wani Salim? Salim daga ina? Safeerah maza wuce gida wucewa tajuya zatayi karaf suka hada ido hakan yasa ta duka tadauki paper bag din ahankali, Baba yace wani Salim ne bawan Allah me kake nema wajen Safeerah ince badai cutar da ita zakayi ba ko? Koko fada ta nemo ? Dasauri Salim yace a Baba, narage mata hanya ne kawai, wajen aikin mu babu abin hawa dan ijiyan zuciya Baba yasauke yace owooo toh Alhamdulillah, nagode Allah maka Albarka, mantuwa nayi dayake Yayanta yakaita ban ganta kafin ta tafiba so ban bata kudin mota ba, nagode nagode gyadamai kai Salim yayi yay shiru yana kallon Baba he felt very very terrible and responsible for condition nasa saiya kasa motsi, ahankali Baba yace Salim tashi yayi daga duken dayake ahankali yabawa Baba hannu yace sai anjiman mu Baba Baba yayi murmushi yace mujima lpy, nagode Allah yayi Albarka BQ dinsu tawuce ga mamakinta saitaga furnitures na ciki na nan but kayan sawansu babu badai da gaske an maidasu wajen masu gadi ba, ko saisa taga Baba ma awaje har an sallami masu gadin? Wucewa tayi flat din tana bude kofa taga Waleed shi kadai yana wasa a falo ga remote a hannunsa duk sanda taga Waleed ahaka only means yan gidan basanan yana ganinta ya washe mata baki yataho da gudu itama haka tace oyoyooo Waleeeeee tawani daukeshi sama yace Ummyyyyy ayoyoooo fitowa Mama tayi tace an dawo yan IT ? Dariya Safeerah tayi tana sauke Waleed tace Mama nadawo ya kuke ? Mama tace baki ganmu ba lafiyanmu kalau, jeki wanka, muna gate yanzu kallon Mama tayi dasauri zatai magana Mama kawai tajuya takoma kitchen alamun batason maganan, shiru tayi saikuma ta kalli Waleed tace kawo remote din muje daki muci abinci ko bata yayi ta ijiye tadauki jakanta da paper bag din tafito tawuce gate tabude dakin tashiga falo ne da uwardaka sai bayi falon ga katifar Baba da Mama sai falo katifarta ga gwangwanayen abincin Waleed awajen ga kayanta a ghana masgo dan babu
Chapter 15 · 0% Book details