Sashe 41
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haka Allah yaso yafaru, yaushe Safeerah zata tare? Sauke kansa yayi kasa yace in 2weeks an ina zaka sata ko acire kayayyakin Nanah akai gidan Auwal ne? Dasauri ya kalleta da mamaki cus magananta just confirm Nana ta yarda zata auri Auwal, sai kawai yace they don t have to, nabarwa Auwal gidan, Safeerah zata zauna a barrack ne Aunt ahankali Anty Asabe tace what about akwatinta da sauransu ? Dan shiru yayi chan yace daman that is why nakira Layla I know Ammi bazata yi ba yakarasa maganan muryansa ba dadi, murmushi Anty Asabe tayi tace m here zan dade ba yanzu zan koma Kano ba, maybe ma sai bayan babban salla, zamuyi everything rannan da za a kawota afara kawota nan iyaye su samata albarka kallon Anty Asabe yayi zaiyi magana ta girgiza masa kai tace I know kayi planning kayi isolating nata from the family sabida ba a sonta due to circumstances na auren ku but you are wrong Son, duk wani abu that is worth your love, kadaga idanu ka kalla kaji sonsa shows abunan worth family love naka, idan har kai ka iya kaso Safeerah means kowa in this family have that tendency of loving her too but hakan only zai iya faruwa ne idan ka barta tashiga family, don t be afraid of kyara da babanka ko Ammi zasu mata, to be honest banama jin Ammi, Dadyn ka nakeji but is still okay, Dady ku can be messy but he is still a good man, let them see Safeerah for she they will accept her eventually tunda kariga ka aura, ina nan, she will come we will welcome her da yar karaman walima kafin sutafi da ita gidansu calmly yace nizan kawota banson kowa yamata rakiya gyadamai kai tayi tace kafara zuwa nan toh da ita before mubarku kutafi gidanku gyadamata kai yayi baice komiba, tace ka shirya kudinka gobe zaka bamu na akwati ni da Layla zamu hada komi gyadamata kai yayi, Aunt ta shafa kansa tace koda kayi kuskure I will always stand by you ballema bakayi ba, kardai ka kara biyewa babanka kaji, take care of Safeerah, baruwanka da Nana in anyway tashigo this family dudda nasan I don t even have to tell you this gyadamata kai yayi baice komiba but yasan she has her reasons for telling him this, ta yunkura tace bari natafi tashi tayi, ahankali yace thanks Aunt fita tayi yakira Auwal awaya sai gasa ya shigo daidai Layla na zuwa Salim ya kallesa sosai duk yayi zuruuu sai ahankali yace you can keep the house I wish you the best Auwal! Zama Auwla yayi kusada shi sai kawai yasa kansa a kafadansa yana sauke ijiyan zuciya, ahankali yace Yaya everything is going to be fine ko? Anatse Salim yace as long as ka tsaya tsayin daka akan family ka! Gyadamai kai yayi baice komiba chan yace can I sleep here today? Gyadamai kai yayi Auwal yamike yawuce sama shikuma yasha tea da Nanah ta ijiye masa tsaf yagama yawuce sama dakinsa yashiga cus yasan Auwal na second room din, wanka yafada yayi yafito yasa jallabiya shafa i da wuturi yayi sannan yatashi yacire kaya yahau gado yana tunane tunane iska ya fuzar yafara juyawa agado yakasa mance how he felt da yayi hugging Safeerah, zufa yafara he was soo in the mood wasa wasa har asuba bai iya ya runtsa ba. EPISODE 4 Wasa wasa Momma ta damu sosai rashin ganin kanninta da Mama agidan yau kwana nawa, gashi Salma tagaya mata wani mai mahaukacin kudi yazo da Urus yadaukesu dan taga motar, sai wane da wane ke tuka motan nan a Abuja, sannan tagaya mata Safeerah tazo ta kwashi kayansu, sosai abin yadameta ga aiki ya kachame agidan ba mai yi Salma ko indomie bata iya dafawa ba balle gyaran gado, banda taci gayu aje yawo babu abinda ta iya, shara nan batayi tace asma dudda bawai kura ne agidan nasu ba, hakanan jiya takira aka samo mata masu aiki da mai gadi. Zaune take akatafaren falon nata tareda wata mata haka dake kama da ita amman saidai ita batakai Momma kiba ba, sannan kayan jikinta ba masu tsada kaman na Momma bane, fuskanta duk yanuna bacinrai da rashin jin dadi, Momma dake kallonta tace in ciyar dasu in sha dasu kuma ban isa na sasu aiki ba idan na saka yarsu ta zageni cikin dan zafi matar tace ni fa Adda Kubra karki ci baki ba bahaka nace ba, kawai kin kaskantar da Shu ibu dayawa haba dan Allah, gashinan ai sun bar miki gidan saiki jika ki shanye sosai Momma ke kallonta tace ni kikema rashin kunya Zainabu? Natura miki kudin mota kizo tundaga Katsina kinamin rashin mutunci baki Zainabu tabude zatai magana dan ita ke bin Momma, Momma ta daga mata hannu alamun tai shiru, tace koma mecece ni Shu ibu yasan namasa rana aduniya, nakuma nuna masa ni yar uwa ce tunda harna taimakesa bayan yarda tasa an kusa kashesa, amman wai nine za a wayi gari nadaga waya nakirasa yaki daukan wayana, gwada kiransa nasan hala ya dauki naki i just want to know how he is zuciyan Zainabu ba dadi dan tasan ba karamin abu zaisa Malam yayi zuciya haka da yar uwansa ba ayanda yakeson zumunci kuma itama bai kirata ya sanar da ita komi ba, tasan sarai baiso yadameta da damuwarsa ce hakan yasa kawai tai dialing number Baba ringing daya yadaga anatse yace Adda Zainabu mun wuni lpy, ya mutan katsina ina Yasmeen dina ? Cikeda damuwa Zainabu tace Malam ina kaje ba a ganka ba? Ina Maman Safeerah? Ina Safeerah ina Waleed kuma? Wlh bansan meke faruwa ba sai yau haka nabi mota tundaga katsina nazo da safiyan nan, kana ina eh? Wlh nadamu sosai kana ina? Dan Allah kafadamin Malam kuna ina iyye ? Yasan yayarsa Zainabu tadamun kam anatse yace ina gidana Adda dayake wayan na speaker Momma ta gyara zama jin abinda yafadi cikeda mamaki, ahankali Zainabu tace gidanka Malam? Gidanka ? Gyadamata kai yayi yace kwarai yau nake shirin kiranki daman banji dadi bane, an mini aiki ne a idanu Alhamdulillah idanuna sun bude rass, saikuma na aurar da Safeerah to mijin data aura Salim shiya bamu gida, yakuma biya duka kudin asibiti na! Yarki zata tare nan da sati biyu Karaf a kunnen Salma dake saukowa daga sama, badai wannan hadadden guy daya dauki Baba bane Safeerah ta aura ba? Hope badai shi bane? Like hope badai shibane cus she picked interest in that man cus tana ganinshi she sees money, real money ba kalan nasu na gado dayakusan karewa ba. Wani irin murmushi Zainabu tayi na farin ciki sosai takalli Momma data hade fuska tamau tace Alhamdulillah Allah mungode maka, Malam Allah yabaka gida muhalli naka, kaga turomin address nazo na ganku Baba yace yanzu kuwa dan muna bukatan zama atattauna kan shirye shiryen biki ya katse wayan, Zainabu takalli Momma tace tunda yabar gidan ki ai shikenan komi yakare zakije ne ko bazaki je ba ? Wani mugun kallo tamata tace ai na yafe Shu ibu ya aurar da Safeerah ban sani ba, ai na yanke sa amatsayin dan uwa, kadai kije ko ajikinta tace eh zani, mu uku iyayenmu suka haifa, kina babba idan bazaki hada zumunci ba, ni zanyi zumunci daku daidai wayanta na ringing taga address ne tadauki wayan zata juya dasauri Salma tace zan biki Aunt hararanta Zainabu tayi tace ke din Salma? Sha zamanki tareda mamanki tana maganan tafice Momma tai tsaki tace shashasha ki dawo ki tattara ki koma inda kika fito Zainabu tace Alhamdulillah dan uwana nada gida tafice abinta, Salma ta taho tazauna kusada Momma tace Momma indai mutumin danaga yadauki Baba ne rannan mijinta wlh bazan yarda ba, kinga yanda yahadu kuwa da alamu yama fimu kudi, irin mazan nan dani suka dace ba da ita ba, a ina tama hadu dashi? Momma this people munafukai ne fa when did they know this kind of person anata boyemana bamu sani ba Momma kafa tashiga kadawa bakin ciki yama hanata magana. Saida Baba yayi magana a waya da security na gate akabar Zainabu ta shigo, Safeerah ne tafita waje dan tarota tana bala in son Zainabu, batada shi, she s divorced tana struggling a katsina da saida abinci, tasan datana dashi data taimakesu, bolt ya kawota daga nesa ta hango Safeerah parking tasa bolt din yayi tabasa kudi Safeerah tai wajenta da gudu batai wata wata ba ta rungumeta tace Ummi naaaa Zainabu tace laaaaa kaga yarinya wai ke bakisan kin girma ba yanzu harda da? Wannan kyau haka dakikeyi kinji kamshin dakike kuwa uwa na lasheki an fara gyaran jiki ne? Kin magana Safeerah tayi tacema mai bolt nawane kudinta yace 6k takirgo kudin tabasa Zainabu sai kallonta take, tace ina wannan tijararren yaron mara mutunci mai halin turawa yaki abincin mu sai nasu dariya Safeerah tayi bata amsa ba sabida kofa da Mama tabude tana rikeda Waleed dake murmushi yana kallonta tace ohhh wai fashewa zakayi Waleed da kiba? Aiko nazo kadingacin tuwo kenan dan kaniyanka turo mata baki Waleed yayi Mama tace sannu da zuwa sannu da zuwa shigowa ciki sukayi duk falo tana kallon gida tace Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulilah kaga ko Malam banasha gayamaka ba Allah baya bacci wlh, watarana sai labari yau ku dubi gidanku, ai Mama Kubra bataci sunan damuke kiranta dashi ba wai Mama, Allah wadaran naka ya lalace zama sukayi ana hira Safeerah tawuce kitchen takawo mata abinci lafiyaye tafito Zainabu ta kalli abincin saita kalli Mama tace kinga rayuwa ko? Murmushi kawai Mama tayi batace komiba sukahau hira, Baba da Mama na bata labarin yaron da komidai hakan yasa Safeerah tamike zatai sama Zainabu tace zonan takalli Mama tace kekuma kira mun shi dan shiru Safeerah tayi, Zainabu tace kiramin surukina nace gyadamata kai Safeerah tayi tace bari na dauko wayan tawuce sama zuwa dakinta tashiga tazauna tadauki wayan daya sayamata hakanan kirjinta yahau bugawa, dialing number nasa tayi takai wayan kunne, zaune yake abayan mota sanye da uniform, wasu sojoji na jansa wayansa ne yayi ringing screen na wayan ya kalla ganin line daya saya yayi saving da Major Safeerah na kiransa yasa yayi jimm yana kallon screen din baya