Sashe 50
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ciromin number Salim Ahankali take bude idanunta dasuka mata nauyi sosai kafin takarasa bude idanun Mama tagani zaune wajen kanta tana shafa fuskanta tana mata magana da bataji saita lumshe idanu tasake budewa ahankali taji Mama tace Safeerah kin tashi! Yunkurowa tayi Mama takamata ta dagota zama tayi ahankali tanabin kowa na falon da kallo Mama, Zainabu sai Yasmeen ke zazzaune kusa da kujeran datake, Momma da Salma na zaune kan two sitter, Baba na zaune kan one sitter yana kallonta kafin idanunta su sauka akan Salim data gansa zaune yana sanye da exact giznan da Waleed yasaka kusada Baba bazaka tantance ga yanayinsa ba amman kallonta yake, sake lumshe idanu tayi ahankali tabudesu sai tawani tashi zumbur ta mike tsaye arude tace Waleed! Direct tayi wajen kofa zata wuce Mama takamata tace Feerah tsaya wait dakata zokiji zauna Mama tariketa wani irin kallon Mama take gabanta na faduwa muryanta bama yafita tace Mama ya .taf Tama kasa maganan Mama ta gyadamata kai tace yatafi da Waleed but I need you to calm down zamu karbo Waleed munje gidansu but basa nan ance sun dade da saida gidan more than a year now, but anakan bincike za a nemosu, dole za a gansa, yanzu abinda nakeso dake is kije gasu Yasmeen su tayaki ki shirya kibi mijinki kutafi gidanku! Wani kalan girgizama Mama kai take tace Mama babu inda zani batare da Waleed ba! Ni banson auren nafasa! Kubasa takardan gidansa Mama I am not doing again! Tafashe da kuka sosai tana dukawa Baba yataso yace kefa dadina dake shirme Mamana, wat are you saying, za aga Waleed, mijinki is on it, tashi kuje ku shirya kutafi cikin kuka sosai tace ni bazani ba Baba! Waleed kawai nakeso yadawo min dashi, idan nafasa auren nan zai bani d ana, Baba Waleed is the most important thing in my life, I can do anything for yarona, Mama kunsan bayason yaron azabtar da Waleed zaiyi, no wlh, ni nafasa auren yadawomin da d ana bazanje ko ina ba bana sons ke! Mama ta dakamata tsawa, haba ga mutum anan Safeerah ko kunya bataji, shi karan kansa Baba ransa yabaci, calmly yace Safeerah listen to me, Waleed zai dawo gareki kinji kidena maganganun nan, I know what you re feeling right now, tashi kuje yamata alamu da idanu kan Salim na nan tadena maganganu haka cin fuska ne, Safeerah fa bamata gane komi girgizama Baba kai tayi tace wlh da gaske nake nina fasa auren Baba, yakawo min Waleed zamu koma kano, zamu sami gida me araha mu kama, bari yariga yace bazai taba bari na kaimai yaro gidan wani ba, ni kuma Waleed kadai nakeso arayuwana, bazan iya zuwa wani wuri babu shi ba, so what is the point of auren nan? Ni ku kyaleni nafasa auren dama banso tuntuni nafas ke dalla chan wawiya yimin shiru! Baba yadaka mata tsawa da take yanke maganan ta hadiye ta, yace banda ke shashasha ce sabida yaron nan Abbati kike cewa kin fasa aure ke bazaki taba aure ba, waye Abbati da zakiyi making that decision sabida shi? Iyye? Mutumin dake neman kasheki? Ya hallaka ki? Ya hallaka,? Kinsan yanzun nan awanki nawa a sume? Are you in your right senses? Kina a sumen nan kinsan adadin wajajen damukaje ni da mijinki Salim? Idan baki tashi kinbi mijinki kunbar gidan nan ba zanyi fushin da ban tabayi dake ba Safeerah, don t toy with my love for you and patient wuce kibar nan kika kara maganan kin fasa auren Salim sai ranki yabaci, stand up nace! EPISODE 47 Mama Safeerah ta kalla tana wani irin kuka tana mikewa, Mama da ranta itama yagama baci tace "ina tare da Babanki dari bisa dari, da hankalinmu da tunanin mu bazamu taba bari ki bata rayuwanki sabida Abbati dayaso karban rayuwan taki ba! Maganan banza kike yarinya, yaron da dagake har Waleed zai hada ya hallaka kike magana haka akai, stand up and follow mijinki we will get Waleed back have faith in Allah, bani mayafinta Maman Yasmeen" mayafinta Zainabu ta dauko takawo tazo wajen Safeerah dake kuka itama tana warwarewa dan yafamata tarage murya tace "trust us daughter, trust mijinki, yanzu u are not thinking straight, but Salim is your best weapon na samo Waleed uhmm" yafamata gyalen Zainabu tayi tabata takalminta mai kyau na akwati Safeerah tasaka tana kuka sosai tana kallon Baba, Baba yakama hannunta saiya bude kofa Salma duk taji ba dadi hakama Momma cus sunsan ayanda Safeerah ke son Waleed babu inda zata yarda taje without yaron, but Baba ya tursasata, motan Salim Baba yabude yasata agaba yarufe yataho gaban motan daidai Salim na fitowa daga gidan, matsawa gefe Baba yayi yace "Bismillah Salim" tahowa wajen Salim yayi kansa akasa anatse Baba yace "Salim ina mai baka hakuri bisa kalaman da Safeerah ta faffada acikin gida akuma gabanka, inaso kasan Safeerah yarinya ce yar kankanuwa, she is only 20, girman jiki ne kawai dakuma kaddaran dayahau kanta harta haihu this early, yarinyar ce data taso taga kalubale daban daban arayuwanta, don't pay attention to abubuwan data fada bata da wayau kuma bakomi bace illa shirme" anatse Salim yace "I know Abba" shiru Baba yayi saiyakai hannunsa yakama na Salim yarike gam sannan yadaga kai yakalli fuskan Salim yace "Salim" dago kansa Salim yayi yakalli Baba ahankali, anatse Baba yace "harga Allah na yarda dakai na aminta dakai, Salim ga amanar Safeera nabaka amananta, ban yarda ka dokarmim diyaba kaji" Baba yayi maganan muryansa tayi rauni and sounding serious, girgixama Baba kai yayi, Baba yace "Safeerah nada shirme kome tamaka ka sanar dani zan bata kashi na hukuntata, ita kadai gareni dan Allah ka kulamin da ita, kamin haka kamin komi aduniya"gyadama Baba kai yayi, Baba ya fuzar da iska anatse yace "nasan yanda takeson Waleed amman inaso na gayamaka ko da munci nasaran karban yaron a musulunce yanda yafadi bai yarda yaron ya zauna gidan wani ba Waleed bazai iya zama daku ba saidai yadawo hannunmu" dan lumshe idanu Salim yayi yabude su ahankali yace "I know Abba, I will handle that, I want Waleed yataso karkashina da mahaifiyarsa" Baba yayi shiru yana kallon Salim wato Salim na son Waleed matuka ahankali yace "tom shikenan Salim na yarda dakai" anatse yace "Abba Waleed d'ana ne, please kada ka kara magana haka, everything will be fine, namaka alkawari I will bring Waleed back" yadan juya yakalli motan sannan ya kalli Baba yace "I promise you zan maida kukan ta farin ciki!" Wani sanyi Baba yaji azuciyansa Salim yace "Safeerah is not alone anymore, duk matsalolinta nawa ne and I will do my best to see na kauda damuwanta, Abba bawanda zan bari yayi hurting matana da raina saidai in bana numfashi! Just take care of yourself da Mama, Safeerah will be fine kaji Abba kaima kadena damuwa" wani kwanciya hankalin Baba yayi ya kama hannun Salim gamgam yanajin wani kaunarsa yace "nagode Salim je kutafi saida safen ku" sakin hannun Baba yayi yawuce yasa hannu yabude motan yashiga batare daya kalleta ba yaja kofan yarufe saiya kunna motan yayi reverse yayi kwana yaja motar yafita daga yayi reverse yayi kwana yaja motar yafita daga estate din yanajin kukan datakeyi har cikin ransa but baice mata komiba cus baida abinda fada no body can understand the pain of a mother especially yaron da tunda ta haifesa tana tareda shi sai yaune rana na farko da basa tare. Kusan tafiyan 40min yakaisu har barrack, dudda she is crying baihanata ganin barikin sojoji ba, ga sojoji rututu sai saramai ake, yashiga ciki anyi tafiya sosai sukakai wani hadadden estate nasu aka bude gate ya shiga, yayi parking agaban block nasu batare daya kashe AC ba yayi shiru yana sauraronta, she's seriously crying though bawai ihun hauka takeba but yana jiyo sautin kukan he knows she's extremely sad, yakai kusan 10mins zaune a motan sannan yabude motan yafito yazagayo ta side din datake yakai kusan 10mins zaune a motan sannan yabude motan yafito yazagayo ta side din datake yakai hannu yabude kofan ko dago kanta batayiba balle ta kalleshi, calmly yace "let's go inside" kaman bada ita yayi magana ba dudda tajishi sarai wani bata mata rai muryansa yayi duk taji she's regretting auren, dabatayi ba da ba'a rabata da Waleed ba, mema yakaita tayi auren nan, kaddara kawai, ganin taki motsi yasa yakai hannunsa ahankali yakama hannunta dake kan fuskanta tana goge hawaye dasu dudda yaji wani irin shocking daya taba hannunta amman saida ya daure bai nunaba yadaure yakama hannun fizge hannunta Safeerah tayi batare data kalleshi ba gabanta na faduwa sosai, tsayawa yayi yakalleta ganin bala'i takeji sosai, ga tsoron tanaji but she's still doing her silly stubbornness, strictly yace "you have 3 seconds to get off this car" kirjinta harwani girgiza yake sabida voice nasa, tafito daga motan da kanta tabi gefensa tawuce batare data kallesa ba,gently yamaida kofan yarufe yazo ya wuceta yasa wani card yabude kofan yajuyo yakalleta, tahowa tayi ahankali ta shiga gidan da kafan dama, biyota yayi abaya ya maida kofan yarufe yayi locking yataho ya tsaya gab da ita inda take tsaye, asanyaye yace "let's go to your room" makemai kafada Safeerah tayi cikin kuka kasa kasa da idanunta da sukai jajir ta kallesa wih faduwa gabansa yayi da kyar ya daure ya dake ya kalleta, kasa jure kallon tayi itama takai hannuwanta tadaura akan fuskanta tana facing nashi gently tasaki wani irin cool serene yet piercing kuka for him, baisan how she does it ba but he's feeling kukan ta har kasan kogon ransa, cikin kuka sosai Safeerah tace "I know you've helped me da su Baba, because of you Baba yaji sauki idanunsa ma yabude, but ni nafasa aurenka! Wih zan maidamaka da gidanka and I promise kome ka kashe mana zan biyaka wlh kuwa, but dan Allah karabu dani kasakeni sabida yadawo min da Waleed!"Tacigaba da reramai kuka tana facing nasa batare data yarda sun hada idanu ba, kai tsaye babu shakka ko sugarcoating da dan zafi kan muryansa Salim yace "da ace na aureki ne dan nasakeki bayan kwana biyu da bazan ma aureki ba in the first place, so l can't grant this wish Safeerah! You are stock with me forever" Jaye hannayenta