← Book details Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 93

Sashe 38

Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

the wrong choice today, I know you don t have a single feelings for Auwal toh why marry him? Shima Auwal din haka ne? Why move from frying pan to fire when you have your whole life ahead of you? Matar mutum kabarinsa gwara kaji kunyan duniya dakaji na lahira, aure is a big thing haramun ne kana gidan miji kana son wani kana kuma kallonsa yana burgeka, soyayyan Salim is not something dazaki yakice in 5days kafin rannan tarewa, kawai ki hakura da aure into this family kinji, ko ba hakaba Anty Dije? Anty Dije shafa fuskan Nanah tayi tace kwarai mamanki tafadi gaskiya Nanah, being married in that family will only hurt you more and more ahankali Nanah tafito daga jikin Mom tana goge fuska muryanta babu ma kwari tace Mommy zaku iya fita kubani 2mins nayi making decision? Gyadamata kai sukayi duk suka fice daga dakin, gently Nana ta sulale akasa tadaura hannunta saman baki tana wani irin kuka mai motsa rai, kaman ta mutu takeji ita Salim zaima haka? Mai tamai soo bad dazai wulakantata haka? And funny enough this 2days saitaji son datakemai ma yakaru yafi na koda yaushe, Idan batai aure into this family dake mugun sonta ba how sure is she the next mijin dazata samu iyayensa will love her kaman yanda su Dady ke sonta and can do anything for her? Batada this guaranty, son da Dady yake mata ko shi Abba fadi yake Dady yafishi sonta, that is that, abu nabiyu what will society say? Nanah the finest girl diyar lecturer buzuwa an fasa bikinta ango yace ya fasa aurenta ayita gulmanta maybe ma blogs su dauka da wanne zataji a lokacin Salim ya barta ko trending dazatayi both in social media and off social media? Sai lastly Salim won against her kenan tahakura, ya ci amanarta ya yaudareta and he will just go free? Ai she will want to see uban waye bazawaran nan da Dady ya keta kira ya aura, so bazawara ma ya aura mai yaro yabarta budurwa intact, sealed sabida wata data taba haihuwa? No she wants to torture Salim ganinta kadai agidansu married to kaninsa can torture him kuma hakan can make him realize yana sonta cus dole yaji kishin ganinta da Auwal, banda haka she wants to use that love da kowa ke mata na gidan tai making sure nobody in that house will love bazawaran matansa, she wants to be close to him tana ganin rayuwansa da kyau sabida tasan dame zatai hurting nasa the most, sai lastly yanda yayi breaking aurensa da ita saitasan mezatayi tayi breaking aurensa da bazawaran she promised sai sunyi one one, maybe hakan yafaru she will be at peace tasa Auwal yasaketa tazo tanemi wani miji mai sonta ta aura, tasss tagoge hawaye ta tamike tsaye tafito. Mommy dake wajen tace kinyi making decision? Gyadama Mommy kai tayi, Mommy tace Alhamdulillah Allah miki Albarka, I am proud of you, you are not alone Nanah na, I will always be here for you and support you in this difficult phase na rayuwanki, love comes and goes but a mothers love baya taba tafiya, and I love you my precious most treasured adorable Khadijatu wani sanyi zuciyanta yayi she don t wanna hurt Mommy amman tarasa yazatayi kasa suka koma aka zazzauna Dady yace Masha Allah me nene final answer naki Nanah? Mommy Nana ta kalla, ahankali tace Mommy I am sorry kiyafemin I don t think har ahada I can get Inlaw s dazasu soni sama da Dady and Ammi ba maida kanta tayi takalli Dady tace Daddy na I will Marry Yayana Auwal sosai Anty Asabe ke kallon Nanah, itama Mommy kallon Nanah take kawai Dady yamike yazo wajenta yace stand up stand up dawowa Nana tayi Dady yakama hannunta sai yashiga dan rawa yace you are my African Queen, Daughter of my dreams sai Abba yazo yakama dayan hannun kawai suka shiga rawa da yarinyar iyaye mata na kallonsu da Baffa da Liman ma haka, wato boko yama Dad dashi Abban Nanah yawa, Nanah sai murmushi take na dole but kuka ne azuciyanta Babanta da Dady na farin ciki suna raye raye da ita ran Mommy yayi matukar baci. EPISODE 3 Around 2 na rana Auwal na zauna an office wayansa yahau ringing screen din ya kalla ganin Daddy ke kiransa hakanan yaji tsoro ya rufesa, are they back daga gidansu Nanah? Daddy yakira ya gayamai bata yarda ba ne ko? Tace tafasa auren gabaki daya dan idan shine Nanah I will never go for brother idan yaya rejected me gwara na hakura da auren duka, sake ringing wayan yayi hakan yasa yadaga muryan Dady so sharp awayan yace dan albarka na! My champion! My Auwalulu, Yaron Babansa, kasan mene namaka order 5 luxury latest cars they will be here in 2weeks, nasaya maka yatch, Auwal fadamin kome kakeso and it s yours! Wani sanyi jikin Auwal yafara cus from yanda Dady is happy Nanah must have agreed sai kawai yaji jikinsa yahau zafi kaman zazzabi zai rufesa Dady yace Auwal ahankali yace uhnn Daddy yace Nanah ta amince zata aureka, I ve sent my designer nasan kana company yazo yayi measuring naka amaka dinkunan biki, yanda kacireni kunya Allah ya biyaka da gidan Aljanna, I love you so much my Rahul Bayya, Choti Choti Chupke Chukpe Beta Auwalu duk yanda yakeji saida indiancin Daddy yasa ya murmusa Dady kam is happy, bakomi as long as mahaifinsa is happy, Yayansa is happy toh shima he is, he will treat Nanah well and respect her, he s okay with her idan she accepts him they will live normal and make babies other wise it s her call he is very much okay with her daman bawai yanada budurwa bane ahankali yace Dady your Hindi sucks nidai bye I m working Dady yace chalo my fine beta, bye ya katse wayan ya ijiye. Jiya aka daura auren, jiyan Mama taje kasuwa and bought everything dazata bukata na ma yarta magunguna harda zabi, daganan tabiya gidansu mai magani ta biyata payment nata full zata dinga zuwa kullum daga safe zuwa yamma ta tafi though basu san kwana nawa Salim zai barta anan ba matan dai tace bill datama Mama na 2weeks ne Maman tace okay Mama tadawo gida tafara nata, zata mata nata magungunan dayan matan zatai mata dakuma gyaran fata da gashi. Tsakanin jiya da yau da matar tazo Safeerah taci abubuwan da wasu har batamata rai suke, she knows menene kayan mata she knows wat they do ai ta taba aure, but kawai bataga amfanin bata ba, auren nan sabida su Baba tayishi shima kuma yace he s not marrying her for anything toh why all this stress kuma tun jiya da aka daura auren dudda ya aiko mata da waya bai kirata ba, yauma gashi yamma tayi bai kirata ba. Karasa cin abun da mai gyaran tabata tayi da kyar tana batarai Matar tai dariya tace Mama wannan Safeerah batason magani Mama tace ai wannan dama sauki bazakiga tashin hankali ba sai ance Feerah tasha kwayoyin asibiti ko allura rannan zakiji kaman ki yankata Matar tai dariya tace aiko Safeerah ki shirya shan magani yau day one ne, gyara zan miki na musamman, bakaramin dadi naji da mamar ki tacemin CS aka miki haihuwan Waleed ba aikina zai zama simple, dudda koda haihuwan ma d kanki kikayi still zan iya aikina kuma komi lafiya lau kawai CS is easier, zakisha mamakin gyara takalli Mama tace nan da 3days zata fara chanzawa idan nutrients din suka fara bin jikinta, package din matan sanata kika biya zakuga aiki da cikawa murmushi Mama tayi tace ko bayan aure idan akwai wani abu ki sanar dani sai adinga kaimata, gyara ai shine mace, ance duk kyanka ka kara da wanka, sai inda karfina ya kare akan wannan mai kan kwakwan turo baki Safeerah tayi Matar ta kwashe da dariya tace haka kikeda shagwaba ahh gaskiya mai gida ya more mikewa Mama tayi tace dan Allah koma zaki koya mata irin yan abubuwan nan ne Matar dasauri tace ga M shakur Safeerah ai Coitus Junction class nata zata shiga kawai, kinga su shagwaba, iya kwanciya da miji wlh sai mijinta yayi kuka Dasauri Safeerah tamike zatabar wajen kunya kaman zai kasheta sabida Mama, Mama tace sha zamanki nayi nan yimata maganan Hajiya Rakiya Mama tafice matar tace kalli Safeerah kinsan mesa nake sonki? Sabida y ata itama ta taba rashin dace ita wata biyu tayi gidan miji ya sakomin ita but yanzu yarinyarata is the happiest girl agidan miji, and lokacin kaman ke take bata wuce 20yrs ba, na kalleta saina fara kuka inacewa this my small girl bata chanchanci zama bazawara ba at this young age, but as rayuwa yacigaba da tafiya nazo na gane cewa everything happens for a reason Safeerah, sabida aurenka na farko yamutu don t be ashamed, hakka Allah yaso, sabida mutane na kiranki da bazawara don t feel anything bazawara sunane da mutane suka kirkiro suka radama mata irinku just to make you feel kaman bakuda daraja or kaman taku takare kun shiga uku kun lalace kaman irin kunada bad luck, in reality you girls are just victims or marriage that didn t work! Or marriage that s toxic, or marriage da akwai rashin compactability, second marriage means second chance! Ki shiga second aurenki with everything you ve got! Tsoron Allah, biyayya, hakuri, juriya, kawaici dakuma yawan addu a cus babu inda ba jarabawa shiru Safeerah tayi maganganunta sun ratsata sosai matan tace the only difference between ke da y ata is ita mijin datazo ta aura yanada wata matar kekuma tacemin kaman ke kadaine yafadi komi akansa amman baice yanada mata ba da yanada ita dazai fadi, so a irin auren nan you will face challenges wajen family sa cus yaro yakama ya auri wacce ta taba aure harda da as first wife ana bala i, zakiji maganganu daban daban, akiraki bazawara, ragowan wani, akira danki dan Angola but don t pay attention, remember cewa this aure kinshigo sa ne as someone with past experience, maganganun nan karma u shiga zuciyanki balle haryayi affecting yanda zaki treating mijinki ko yaga bacin rai ko wani abu,
Chapter 38 · 0% Book details