Sashe 32
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yakawosa ba hakan yakara tabbatar mata da dagaske yake, bugawa zuciyanta yafara sosai tai shiru chan kuma tace ba bikin mu saura 7days ba? Baby wallahi I am not understanding anything please explain ? Tai maganan muryanta yayi rauni sosai, ijiyan zuciya Salim yasauke yana kallonta da kyau yace wani accident happens to me 5yrs ago that almost cost me my life, but wata yarinyar lokacin saved me, I ve been looking for the girl all this while, 5yrs kenan da faruwan abun ban ganta ba sai recently na ganta, na aureta today! Wani zafi Nanah taji kirjinta nayi saitaji kaman ma an rike mata numfashi idanunta suka cicciko da hawaye wani irin mahaukacin kishi na turniketa numfashi na gagaranta, wani zafi da daci jikinta ke mata tundaga kan dan yatsa zuwa brain dinta, duk yanda zatai bayan n abinda takeji abin yawuce, mijinta fa, wanda zata aura, an fara event today just 6more days to go yazo yana gayamata ya auri wata magana kawai na saukan mata aka uwa aradu, takallesa sosai, shima ita yake kallo baice komiba cikin wata kalan murya mai rauni tace ni zaka yaudara Salim ? Zuba mata mugayen idanunsa yayi batare dayace anything ba, dudda gabanta yafadi sosai bai hanata fashewa da kuka ba tace mena maka da zakamin kishiya and baka gayamin ba sai bayan kayi auren? I ve been calling you nonstop for 3days but no response ashe kanachan kana auren wata abunka, I suppose to be your first and only wife wata from nowhere tazo ta tunkude ni the waya kakeyi daman ko sun magana da mace bakayi daman kana magana da wasu matan? I thought you are this strict da kowa, kaci amanata ka yaudareni, few days to bikinmu saika auri wata, you re very mean Salim, u are a bad person, you are inconsiderate! Bakada Imani, how would you feel idan wani yama kanwar ka Ameerah ko Lubna hak Khadijah! Salim yadaka mata tsawan da saida tadan matsa baya sabida tsoro, cikin kakkausan murya yace t ever bring sunan kannina into I and urs conversation sosai take kuka harda shesheka tajuya azuciye zata bude kofan tafita yayi locking yace ban gama magana dake ba, idan nagama i will release you kitafi! Juyoda kanta Nana tayi tana kuka tace I don t wanna talk to you ka kyaleni kariga kayi abunda kayi niyya ka barni in tafi tashiga kuka yadan lumshe idanu yabude, ahankali yace I have something important to discuss ki saurareni pls dago kanta tayi takai bayan hannu ta goge fuskanta tajuyo takallesa ta turomai baki sosai cus ta dauka lallashinta zaiyi jin for the first time tunda ta sanshi yace mata please. Ijiyan zuciya Salim ya sauke yace Nana Khadija you re a bright free spirited girl data taso cikin soyayyan iyayenta, yan uwanta da sorroundings nata, baki lacking anything ba as far as iyakan sanina a rayuwanki yadanyi shiru itakuma takara turomai baki ashagwabe still zuciyanta namata zafi, ahankali yace recently I came across wani incident that left a question in my heart yasa inata tunani, is about aure daya mutu in just six month due to so many up and down from auren iyayene suka hadashi zuwa kan lack of soyayya which I believe yarinyar batason mijin, mijin bayason yarinyar, she s just like an item iyayensa bought for him he feeds on it, abuse it dump it, now basa tare she s left with a young innocent Baby a hannunta yakalli Nanah da kyau dake kallonsa ya tsareta da idanu yana sake mata kallon kurilla he wants to force kansa yaji ko yanason yarinyar but babu do ko daya, hakanan Nanah taji gabanta nafaduwa kawai taji kaman labarin daya bata da ita yake magana sako yakeson gayamata, calmly yace I dont love you Nanah Khadijah! Wani radadi sosai Nanah taji kawai ta kulle idanunta ta runtse su gamgam, anatse yace I dont have feelings for you Nanah! I don t want to ruin rayuwanki because of our parents, just like labarin dana baki na incident dinchan yayi shiruuu ahankali yace re beautiful, you re unique, you re kind, akanme zaki wasting all this features akan someone like me da duk bana ganin this amazing features naki? Yadan fuzar da iska kadan yace I know kalamai na are hurting you but I have to tell you the truth! Yasakeyin shiruuu chan yace Nanah Khadija bazance nafasa aurenki ba but nafada miki gaskiyan abinda ke zuciyata the ball is in your court, idan after knowing the truth still kinaso ki aureni ahaka is fine, idan kuma kinji mutum irina doesn t deserve you, kin chanchanci ki sami better man that will see you for you and fall for you please call off the wedding i believe that is the right thing to do, but decision din naki ne! Yanda zuciyan Nana yawani rirrike mata she thought she was dying in that car, batun yauba she knows baya sonta but tanata delulu tana yaudaran kanta tana gayama kanta haka sojoji suke da murdaddun hali, gasu abaibai, basa nunama mata so da sauransu, but she was wrong yaga wacce yakeso dagudu ya aureta, bayan ya aureta yau yazo gidansu, gidansu dataketa rokonsa yazo yaki but yau yazo sabida yagaya mata baya sonta karta auresa sabida yasami wacce yakeso shi ya aura, bude idanunta tayi ta kallesa tanaji kaman ta kashesa takallesa idanu cikin ido tace na tsaneka Salim! Na tsaneka! Na tsaneka! Tafashe dawani irin kuka bana wasaba tace duka yan uwanmu from across all garuruwan Nigeria da yan Niger ma suna gidan nan! All my friends na university all of them na gidan nan! Souvenirs na bikinmu with printed names namu ajiki duk suna nan infact yau an raba wasu ma na kauyawa day, Salim ka kalleni I m just 25yrs kamin adalci? Are you trying to turn me into a laughing stock aduniya? Kamin adalci? Wat wrong have I ever done to you? Kamin kishiya kakuma gayamin ka tsaneni bakason aurena ka kyautamin? Tafashe da kuka sosai Salim yayi tsit cus she s really hurt, imagine now she s feeling hurt to ta auresa fa? He don t wanna hurt her so menene amfanin aurensa? Bayan hannu takai ta share fuskanta tass saitai murmushi ta kallesa tace ni ba yarinya bace i know how the world works, kai kasami wacce kakeso ka aure sharp sharp kazo kana gayamin baka sona amman kabarmin hukunci na zartar idan zan aureka ko zan fasa auren ko? Tai shiru saikuma tai murmushi tace all I want to do is to hurt you real bad Salim! Kaman yanda kai hurting nawa kacimin mutunci, maybe the only way zan iya hurting naka is ta hanyar aurenka da bakaso nayi din! So I will think idan zan fasa auren ko zan aurenkan dama kace the ball is in my court i promise you i will play the ball well and it will hit the right spot, budemin kofa nafita tai magana azuciye, baice komiba ya danna lock tabude motan tafita ko kofan bata rufomai ba yabita da kallo kafin ya yunkuro yarufe kofan da kansa ya kunna motan yatafi. NOW READERS BE THE JUDGE! MEKUKE GANI SHINE DAIDAI TSAKANIN NANA DA SALIM? AUREN KO RASHIN SA??? SALIM YACIKA TSAURIN RA AYI KO?? DA GASKIYAN DADY DAYACE YANADA WICKED HEART LOOK FA KO TAUSAYIN NANAH BAIJIBA KUNA GANIN SAFEERAH ZATAJI DADIN ZAMA DA MAI MURDADDEN HALI KALANSA KUWA?? IDAN AKA FASA AUREN AKWAI BALA I TSAKANIN IYAYEN SALIM DA SALIM WANDA SAIYA SHAFI SAFEERAH SOSAI KOH??? KU KASHE WUTAN NAN MEYA KAMATA AYI NE?? WAIT GA IMPORTANT QUESTION WAI SON SAFEERAH MA YAKEYI NE KO MENE SHI SALEEM DIN??? EPISODE 3 Ahankali Layla tace Ammi dan Allah kiyakuri dan Allah, Ammi kumai addu a, this is dsame thing that happened dazai zama soja, dazai bude company sa, Ammi I m sorry but idan ban gayamiki maganan nan ba zata iya kasheni, Ammi you better than kowa kinfi sannin waye Salim, why in the first place ma zakima bar Dady yace yazaba masa mata when kunsan halinsa? Kubarsa ya nemo mata da kansa kunhadasa da yarinya when kunsan waye shi da how he is? Ammi ko ya auri Nanah inbadai wani ikon Allah ba bakin ciki zakisha kuyita sulhu, mesa zaki yarda Ammi tace yazanyi da Babanki? Daya hada auren tareda abokinsa I was not there daga baya yake gayamin yama Salim mata Layla tace Ammi ai sai ki barsa suyita gwabzawa dashi da Dady daya hada komi, when he knows Salim is just like him, shi Dady akwai wanda ya isa ya chanzamai ra ayine? Please Ammi kidena damuwa just pray Allah knows best, Allah knows why all this is happening kinji Ammi na lemme hug you Layla ta tashi ta rungume Ammi for the first time Ammi tayi murmushi tace yara mata rahama ne wlh! Meenal is so lucky tasami my beautiful angel Layla as her Mom, kinga Yara maza are nothing but headache especially yayanki Salim murmushi Layla tayi tace Ammi Yayana is the best wlh, idan ka fahimce sa he is the simplest person kawai yanada wuyan sha ani ne she comforted mahaifiyarta sai wajejen 12 nadare tabar dakin. Shigowa boxing arena KB yayi just about 15 people ne aciki duk suna tsaye suna kallon Salim dake cikin ring dawani soja suna boxing yana sanye da short na gym da riga mai kama da singlet all black, hannunsa daya normal daya a kone ga handglove a hannunsa suna boxing sosai, boxing is his hobby yawanci yana cikin morning routines nasa idan bazai fita aiki da wuri ba, sai tafi ake clap, KB yace Zero you have a guest Salim na boxing abinsa batare daya kallosa ba yace ? KB yace Baffa ne! Chak ya tsaya yana dagama sojan hannu alamun yadakata yana zufa sosai ya kallo KB batare dayayi magana ba, KB yace a barsa ya shigo ba saida yakirani wai wayanka akashe, come he s outside dan ijiyan zuciya yasauke yana zare handglove din yadaga rope yayi wani tsalle yasauko yawuce yadauki wani karamin towel yashare fuska ya yafa akan shoulder nasa yafito yana tafiya awani bubbude yana tafiya like a damn bijimin lion, Baffa na tsaye gaban motansa awaje