← Book details Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 93

Sashe 47

Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dan saurayi guda daya Waleed sauke kanta kasa Mama tayi batace komiba amman maganan yamata wani iri, Ummi tace mace ko takai shekaru dari mace ce Umma tace mu baruwan mu da al adun nan, munga diya munaso munyi abinda yakamata makota suka keta guda, aka fara bude akwatina ba su Ummi ba hatta makota dasu Layla saida kowa yaga yanda fuskan Momma ya chanza kunga kayan da akama Safeerah kuwa, Momma ta kirga set set na zinare masu faska faskan sarka guda biyar wanda kudinsu duka zai iyakai 500million ga atampopi babu ta kasa da 200k abaya kusan guda 20 yan millions ne bayan 100k ba, ubanme yakai Shamsu kai Safeerah kampanin nan data sani da Salma aka kai, Innalillahi jibi arziki this people are rich rich crazy rich, abubuwan aka shiga shigowa dasu sukaci sukai kat sannan suka tafi Mama takawo 300k shima cikin kudin da Salim yaba Safeera tabayar da abubuwan da akayi suka karba sukai godiya sosai da nuna jin dadi babu rainuwa suka tafi for the first time sai Mama taji zuciyanta ya natsu da aure cus sunada mutunci ga karamci kudinsu baisa musu girman kai ba, jibi yanda sukai godiya da kudin mutanen da sunsan sunfi karfin ta. Neigbours sukama Mama addu a, Ummi tahada musu komi ta babbasu suka tafi, kaman jira Momma take tace aikin banza yarinya zatai aure amman har yau kun kasa sa yaro yazo gida ya gaidani ina head of family dinmu kallonta Ummi tayi ta tabe baki tace maida wukan Hajiya Kubra Head of Family Salim zaizo ya gaidaki zan sanar da Safeerah ta gayamasa wani kallo Momma tamata kaman ta maketa tace wai nazama tsaran wasanki ko kudi yasa kika tarama matarnan biyayya tanuna Mama data juya abinta Ummi tace wai me matsala ki eh? Adda me haka? An zauna agidan ki kin addabesu sun barmiki, yarinyar dakika kora tasamo miji sai bata rai kike cikin fushi Momma tace eh mijin da d ana Shamsu yayi sanadi ba, da bai kaita ba da zata iya zuwa kampanin ne ita tama isa tashiga kalan wajajen nan, ni din ce dai sanadin duk wani good abu dasuke dashi a duniya shiru Ummi tayi ta tsaya tana kallonta ganin bakin ciki karara bataso tabiyemata ayi fada gwara a lallabata ayi auren lpy tace to ki yakuri tashi tayi tace Salma tadawo ni natafi gida tawuce tafita abinta Ummi tace baki dauki komi a akwatin ba yakamata kisa albarka fa Adda Allah ya kyauta tabude kofa tafice Wuraren 2 Safeerah suka dawo me gyara ta takirata daki tana rike da Waleed, Yasmeen da Salma tara da ita akwatinan falo suka kalla, kallo daya Safeerah tama kayan ta wuce, mesa yamata akwatina dayawa haka tawuce wajen me gyara tana ijiye Waleed gefenta dahar yatashi tace ina zaka zauna kaga bari nabaka wayana ta kunna mai cartoon a YouTube yana kallo aka bata maganin sha, Ummi tashigo dakin tace Momma na so Salim yaje ya gaidata agida? Ki kira ki gayamasa kallon Safeerah tayi saikuma tace Ummi gaskiya ki gayamasa kedai dakuwa Ummi tamata tace kinci gidanku dakike cewa ni nakira, maza kirasa banson damuwan Adda please tai maganan tana wucewa tafita, dan shiru tayi saita kalli Waleed tace Waly bani wayan nayi kira kaji cikeda rigima yace uhhh murmushi tayi tace yakuri dan Allah, arama Ummy zan baka cheese dasauri ya sakan mata wayan yace cheezee gyadamai kai tayi tace takai wayan kunnenta harya katse bai daga ba sai gashi yakirata back ahankali ta daga tace ina yini muryansa kasa kasa yace yakuke how is Waleed? Ahankali tace gashinan kusa da ni murmushi yayi yace basa wayan zare wayan tayi daga kunnenta tasa a speaker tace Waleed gashi za ayi magana dakai karban wayan Waleed yayi yasa a kunne a juye da karfi yace aloooooo dariya Umma mai gyara tayi, itama Safeerah tai murmushi tana kalllon Waleed kaman zata cinyesa tana mugun son danta, daga ta dayan bangaren cikeda so Salim yadan daga murya a sigan yarinta yace Waleeeeddddd zaro idanu Waleeed yyi saiya juyo yakalli Safeerah yaron yanada mugun wayau ga brain cikin voice nasa na yara yace Ummyyyy Abeeeeee! Wani kunya Safeerah taji sau daya ta gayama yaron Abee by mistake but harya rike gyadamai kai tayi alamun eh shi ne, Waleed yasake juyawa yace Abeee! Wani piercing zuciyansa yanda yaron genuinely call him father yayi saiyaji yakara sonsa, cike da sincere love yace am my Son, how are you ? Dasauri yace fine Abee Salim yace yesss good boy, how is Ummy ? Dan kunya Safeerah taji jin ya tambayeta, juyawa Waleed yayi yakalli Safeerah dake kallonsa ta batarai sosai yace Ummy fine Abee sai yacire wayan yasa a kunnen Safeerah yace Ummy Abeeee, talk kaman Salim yagane me Waleed yayi saiyace Hello Ummy! Wani irin sanyi Safeerah taji a kunyace tawani sunnar dakai murya kasa kasa tace ni sunana Safeerah dasauri Waleed yace Ummy! Salim yayi murmushi mai sauti kadan yace kinji ko Ummy, why did you call? Cus yasan bata kira saida wani abu, ahankali tace ahmmm daman Momma Yayar Baba keson ganinka ta wannan gidan shiru yadanyi he knows akwai yaro awajen ahankali yace okay yace Waleeeeed dasauri Waleed yacire wayan daga kunnenta yasa anashi yace Abeee Ball dasauri Salim yace meya sami ball dinka ? Dasauri Waleed yakalli Safeerah cus jiya ta karbe ball din ta boye cus ya buga a tv, raurau yayi da idanu kaman zai fashe da kuka yace Ummyyyyyy idanu Safeerah ta zaro yanzu Waleed har ya iyakai karanta, ahankali Salim yace t cry zansa Ummy ta baka ball dinka bata wayan sama Safeerah wayan yayi a kunne anatse yace ina ball dinsa? Ahankali tace na karba na boye mesa? Ya tambaya ba wasa, Waleed ta kalla tace tv yake bugama kwallon strictly yace and so? Maza kibasa ball dinsa, seizing the ball is not a solution, he s a small boy he needs to play, correct him gently then kibasa his own space na ball, maybe back yard ko wani room is okay sosai taji kalaman sa hakan yasa tace okay dasauri Waleed yamaida wayan kunnensa yace Abeee murmushi Salim yayi yace Ummy zata baka but karka buga a tv is not good okay gyadamai kai Waleed yayi yace okay Abeee dan ijiyan zuciya Salim yasauke like is this how sweet kids are wallahi he loves the boy, ahankali yace bye bye Waleed raurau Waleed yayi da fuska da Umma mai gyara da Safeerah sukahau kallon yaro kaga yaro, sai kawai yafashe da kuka sosai kafin Salim yayi magana Safeerah tasa hannu ta karbe wayan ta katse ta harari Waleed dake kuka tace daga mutum yayi magana dakai saikahau mai kuka bazaije yayi aikin gabansa ba? Idan kana irin halin nan bazan kara baka wayana kayi magana dash Ringing wayanta yahauyi Umma mai gyaran tace wallahi shima yana bala in son Waleed gashinan yakira, ki barsa mana yarone jibi yanda kika sakashi kuka yanzu cikin kuka Waleed yamikamata hannu irin tabasa wayan nan daukan wayan tayi tamika masa ya karba yakai kunne dayake ta manta batasa a speaker ba but gani tayi yadena kukan yakai hannu yana share fuskansa saiyahau murmushi saikuma yahau dariya sosai, Safeerah sai kallonsa take batasan meyake gayama yaron haka ba dayake dariya, hawaye taji ya cicciko mata a idanu dasauri tadena kallonsa she s just feeing bad for Waleed, mahaifinsa ya tsanesa baitaba ganinsa ba rannan dayasan tanada ciki yakirata shi bayason ciki, data haihu an kirasa but still bayaso ko pure water mahaifinsa Waleed baitaba sha ba, look at yanda yakeson wani a matsayin uba wanin da bamatasan ko zai barta taje da Waleed gidansa ba, dudda yataba fada but batasan ko parmanent bane, taki maganan sabida ita duk inda zatasa kafa danta na wajen idan bai yarda ba yasaketa, maybe duk hiran na yanzu ne suna zuwa gida yafara wulakanta Waleed ko ta haihu ya banbance nasa yaran da Waleed it happens ai she s just feeling bad for the boy, kusan 20min yayi yana magana da Waleed sannan ya katse Waleed yabata wayan da kansa yana tsalle yana clapping. EPISODE 4 Wuraren 8 sukai parking agaban gidan Auwal Ango ke tuki, baiso yadauki KB cus he knows the people are not that nice sune sukai making life na matarsa miserable, wayansa Auwal yadaga yakira Shamsu nan da nan aka bude musu gate suka shiga ciki sukai parking, Shamsu yafito yana sanye da jean da riga, jean din yasauka kasan bombom dinsa yayi ass down kana ganin boxer sa kallo daya Salim yamai yadauke kai he sees why kaninsa baiyi keeping Shamsu as close friend ba, fitowa yayi a nutse Shamsu yace Inlaw Inlaw bayabo ba fallasa Salim yamikamai hannu batare dayace komiba shima Shamsu yadansha jinin jikinsa yamaida jeans nasa waist yace kumuje Momma na jiranku yana gaba suna biyeda shi abaya suka shiga falon Momma na zaune taci uban gayu tasha gwal ta tsare Salim din da kallo tana salati da sallallami ina Safeerah tasamo hadadden classic namiji irin wannan jama a, dan bata taba ganin Salim dinba sai yau, maza like this da Salma sukafi dacewa not wata Safeerah, murmushi tayi tace bismillah ku kuzauna akasa kan carpet Auwal ya zauna while Salim yayi zamansa kan kujera ganin haka Auwal yadawo kujera shima zauna Momma tace laaaa ga kujera da zaka zauna akasa Auwal anatse Salim don baison bata lokaci yace ina yini murmushi tayi tace lpy lau bari akawo lemu, Salmaaa daga ciki cikeda fi ili da kakale akace am Momma fitowa Salma tayi taci gayu anmata wani professional makeup tasaka wani mahaukacin lace hadadde sky blue batasa gyale ba kayan sun kamata tana wani irin kamshi na ban mamaki takalli Momma ashagwabe tace gani Momma murmushi Momma tayi ganin yanda tai kyau tace kawo ma bakin mu su lemu kizo ku gaisa murmushi tayi tace tawuce kitchen bata jimaba tafito da tray da lemu ke kai da dakbun nama yar aiki biye da ita da tray na small chops tazo wajen dukawa dab da Salim tayi tace Yaya ga ruwa dasauri Auwal ya kalleta ganin yanda ta duka kusa da Salim like wat is this? Momma tai murmushi tace ga Autana Ummu Salama kenan muna kiranta da Salma,
Chapter 47 · 0% Book details