Sashe 16
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wardrobe anan jin ranta zai baci yasa kawai ta zauna tare da Waleed tashiga bayi ta wanke hannunta tace at least I m grateful for this food ko Waleed yaron yace murmushi tayi tabude Chinese rice ne sai Nan bread, humus da curry soup, sai turkey, salad da pinacolada murmushi tayi tace abincin yan gayu debo rice tayi takai bakin Waleed tace kin ci yayi ya kauda kai sai ta gutsuro Nan bread tabasa ya karba yahauci tafara ci ba wasa yunwa takeji, ita da Waleed suka shanye juice din dadi tabar ma Mama Nan bread da soup din tawuce bayi tayo alwala tazo tai la asar ta chanza kaya tadauki Waleed suka fito sukazo kitchen ta taya Mama aiki suka gama komi suka kara gyara ko ina sukasa turare, sannan suka fito suka koma flat dinsu tace Mama ganaki kallon abincin Mama tayi tace waya siya miki abinci? Ahankali tace Oganmu anatse Mama tace mesa? Yasanki ne ? Girgizama Mama kai tayi tabata labarin yanda batada kudin mota da komi, Mama tace inada 20k idan zaki tafi gobe saina baki saiki hada da 15k dinki ki samowa Waleed dan abincin daya sawwaka da pampers ko irin me guda goman nan ne shiru tayi ta tsare Mama da idanu tana kallonta, Mama tace menene kike kallona haka? Hannun Mama takama ta jujjuya tana kallon uban shedan yanka wasu sun warke wasu basu warke ba, takai hannunta ta taba kashin wuyan Mama, da fuskanta da duk yayi wrinkles, sai hawaye yafado idanunta dasauri Mama takai hannu ta share mata tace zaki fara yauma ko? Kina wani duddubani kaman patient, duk randa kike neman kuka abinda kikeyi kenan Lips dinta ne suka fara rawa tace Mama na tambayi wajen IT ko zasu bani aiki parmanently na tara albashina na kama mana gida mubar nan? Tsareta Mama tai da idanu sai kuma tai murmushi ganin yarinta tace yaro man kaza, shi aikin dakike magana akai ba su suka samo miki ba ? Ahankali tace eh dudda haka amman ai basune masu kampanin ba Mama tai murmushi tace ko dubu dari ake biyanki bazaki iya rikemu ba Safeerah mubar maganan ma dan Allah, kinyi tunanin makarantan ki? Mahaifinki duk wata wata yake zuwa checkup na idanu da hawan jini, ga Waleed very soon zai shiga 3yrs za a sashi makaranta dole, abincin sa fa, pampers waye waye, I know kin damu but u can t do this Safeerah! Rushewa da kuka sosai Safeerah tayi dayasa Waleed yazo wajen da gudu yana leko fuskanta Mama tace wai me haka Safeerah kinga zakisa yaron nan kuka ko zo Waleed Mama ta daukeshi yafashe da kuka yana kallon Safeerah data kasa daina kuka, Mama tace wlh banson wannan halin kawai saiki tasani agaba kina kuka ba a miki komi ba eh cikin kuka Safeerah tace Mama nagaji da ganinki ahaka nagaji, kullum daga safe har dare aiki kike, kin zama yar aikin wasu da ba a miki godiya sai zagi da cin mutunci, while Baba an maidashi mai gadi da wanke mota ana zagin mahaifina kullum agabana, Mama mubar nan ko barane muje muyi yafimin da this life we are doing here, school din banaso lets leave Mama dan Allah Safeerah kuka Waleed kuma Mama tama rasa wazata lallasa sai kawai itama tafashe da kuka tace Safeerah yakikeso nayi eh? Ina kikeso nasa kaina naji dadi? Ni yar rikoce banmasan iyayena ba Babana yarasu kafin ahaifeni mahaifiyata wajen haihuwana tarasu yar rikoce wajen yan uwan Babana, wahalan danasha wajensu bana shan kalansa anan, mahaifinki shiya ceceni ya aureni sukace sun yafeni banda kowa sai mahaifinki duk inda zaisa kafa zan saka tawa sabida yabani gatan daban taba samun kalansa aduniya ba, wannan shine hallaci duk runtsi duk wahala ina tareda shi, dagani har mahaifinki sabida ke muke zaune anan nothing is important arayuwanmu face ke da Waleed as long as zaman mu anan zaisa ki cigaba da samun education Waleed na samin abinci da kulawa fakat mu karmu samu mun hakura bakomi, stop crying we are doing this for you, no condition is parmanent watarana sai labari, zagi da cin mutunci baya kari, dan Salma ko Shamsu ko mahaifiyarsu sun zageni it s okay, watarana ko ance suyi bazasuyi ba, abinda nakeso is just focus on school naki, kigama IT dinki and become somebody, as for Waleed zan kula miki dashi as long as I m alive kinji, please karki bari Babanki yaji maganganun nan kar BP sa yatashi ya isa zo nan yarinya na nasan badadi ana zagin miki iyaye amman kiyakuri kinji Feerah na Mama ta rungumota zuwa jikinta lamo tayi jikin Mama haka shima Waleed yayi lamo yana kallon mahaifiyar tasa dake kuka Baba yadade gaban dakin tsaye dan yaji komi sai kawai yawuce yakoma waje yabuga tagumi, yasan watarana sai labari shi bayajin kyashin yima yayarsa Kubra komi sabida takula da lafiyarsa, tasaka yarsa a makaranta da sauransu, kawai baitaba sani yayarsa Uwa daya Uba daya zata iya maidashi mara daraja dan aiki mai wanke mota ba da gadi tana zaginsa da cimasa mutunci gaban iyalansa ba, shi yasan da shine mai hali Kubra tazo garesa bazai taba maida rayuwanta haka ba, zai iya kwashe iyalansa sunbar nan ba but tunaninsa shine aikin me zai samu baya gani? Tayaya zai rikesu? Mama Kubra ta cutar dashi sosai kawai baiso yayi magana ne sabida zumunci amman bazai taba mance lalata yaruwan yarsa datayi ba ta auramata dan shaye shaye mai duka. Basu dawo gidan ba sai wajen 12 tuni Safeerah tai bacci anan falo shima Waleed haka, Baba yafito daga uwardaka yafito yazo yabude musu gate, driver ke tuka Momma da Salma dake baya suka shigo ya maida gate yarufe yabiyo motan Momma ta sauko yace sannu da zuwa Mama Kubra kallonsa tayi sannan takalli driver ta tace kai zaka koma BQ yanzu cike da girmamawa yace toh Hajiya Salma tayi gaba batare data gaida Baba ba tace ka daukomin kayan dinki na a boot Momma tace ka tsaya kana kallona bakaji abinda Salma tace bane ahankali yace naji bude booth yayi yadauki jakan dinki yawuce flat Momma biye da shi har bene yashiga hawa Momma tace nasan ba hankali gareka ba ka ijiye agaban dakinta baka shigo ba daga ciki Salma tai kwafa tace yashigomin daki bana gaura masa mari ba hmmmm Baba baice komiba yawuce ya ijiye gaban dakin Momma tayi dakinta tace ka kashe wutan ko anatse yace Yasauka yakashe wuta yawuce yafita. EPISODE 1 Washe gari da sassafe Safeerah ta tashi ance ba ason latti bayan tai salla ta taho flat tas tashiga share share tana azkar ahaka ta gyara ko ina tasa turare 7 har yayi Mama tace maza jeki wanka wucewa tayi taje tai wanka wani black abaya tasaka yau is simple abaya babu wani kwalliya ajikinsa dan stones dake jiki sun dade da fita tun na akwatinta ne shima rigan, closed abaya ne black but a goge, tasaka wasu hook earings farare masu kyau Mamane tasayo mata su a kasuwa, batama tsaya gyara gashinta ba gyalen kawai tayafa aka tadauki jakan bayanta ta goya tafito she smells good very mild, Mama tries dasai mata yan turaruka da khumra haka da yan kudinta tasaka flat shoe black tafito, wucewa tayi zataje flat Baba dake shigowa gidan baiso yauma takara tafiya da bakin ciki yace wuce kitafi dasauri tajuyo tace Baba ina kwana hannunsa yasa a aljihu yaciro 10k yamika mata yace gashi ki hada da wanda mamanki tabaki ki sayoma Waleed abinci da pampers saiki cire na mota kisai abinci kuma kici murmushi tayi tace toh Baba nagode Allah kara bude, jama a Babana yafi nakowa principal Baba dariya Baba yayi yace uhmm Principal da ba idanu yanzu murmushi tayi tace da nazama Nurse dana maka magani yanayin fuskan Baba chanzawa yayi sabida burinsa kenan Safeerah tazama Nurse, wucewa Safeerah tayi tafice yabita ya tsaya a kofar gida tafiya tayi harta fita wajen layinsu tasami keke tahau yakaita bak n junction tasami mota yakaita har layin wajen aikin sannan tatako daga junction zuwa company 8:05AM tashigo kampanin kafin takai ciki was 8:09 zatai hanyar office nasu receptionist tace you need to sign in Miss Safeerah gyadamata kai tayi tazo tai signing receptionist din na kallonta ahankali tace re very pretty Miss, I love this plenty hair on your forehead kallonta Safeerah tayi sai kuma akunyace tace thanks ta ijiye biro tajuyo tawuce zuwa office tabude tashiga Madam Maimuna na desk dinta, ahankali tace morning sannan tawuce wajen Madam Maimuna dake kallonta tana murmushi adan kunyace tace ina kwana Anty ? Murmushi tamata tace lpy lau ga files naki jeki karasa sai na koya miki next abu, before then get coffee or tea, anjima da rana zamuje canteen muci abinci Oga yace kowa yadinga zuwa cin abinci bill on him, anytime Oga Salim ke gari enjoyment kawai akeyi a kompany, jiya yabada kudi araba naki na hannun Mr George gyadamata kai tayi ahankali tawuce ta zauna tafara aiki. Wuraren 12 yashigo company cikin wata army green motan kana ganin motan kasan na soja ne tundaga plate number, Parking akayi chan aka bude kafansa na sanye cikin boot din sojoji me ruwan kasa yafito anatse yana sanye cikin wandon sojoji daya zauna ajikinsa tsaf, ba rigan sojoji mai common flag ne ajikinsa ba wani green riga ce mai v neck data kama jikinsa tsam har 6packs dinsa kana gani yayi stocking da rigan gawani arnen belt na sojoji a waist nasa hannun rigan gajerenne so kana ganin muscles dinsa a murde sosai, idanunsa sanye da bakin glases sosai, kansa ba hula sumansa sunyi wani irin kyau ka gansa sai kwarjininsa ya cika maka ido maida motan yayi yafara tafiya anatse few employees nasa na gaidasa instead ya shiga ta basement ta main entrance ya shiga dasauri receptionist din tace welcome Boss dan gyadamata kai yayi yawuce yashiga hayowa staircase anatse yana bin ko ina da kallo har yaje fourth floor a staircase ko gajiya baiyiba office dinshi yawuce secretary dinshi na biyosa ciki tace welcome Sir, coffee or tea Sir? Batare daya amsata ba yawuce ya zauna yasa hannu ya kunna desktop nasa sannan yace none, excuse me dasauri tace yes Sir tajuya tafice fuzar da iska yayi kawai yaja