← Book details Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 93

Sashe 54

Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yafara amman tadaure tabude kofan tsaye tagansa cikin dakin yacire rigan dagashi sai wandon aiki dayadan sauka kasa she could even see white boxer dake jikinsa na CK, ko riga babu jikinsa, faduwa gabanta yayi sosai tajuya da sauri zata fita yace "ina zaki? I thought you come to say something"? Bakinta na rawa dan bata taba ganin jiki irin nasa ba kaman na yan wrestling tace "eh amman zan iya jira kagama" hannu ya mika yadauki white t-shirt daya dauko ya warware yasaka mai V-neck yace "nagama you can turn around" wani wawan ijiyan zuciya tasauke da shi kansa saida yaji tajuyo but takasa kallonsa, kanta na kasa tashiga wasa da fingers nata saikuma ta dakata takai hannunta taja gyalenta tana rufe kanta da kyau tana kara gyara wa tana rufe wuyanta da kirjinta da kyau she's just so restless idanunshi kur akanta, ahankali tace "nagode, Allah saka da Alkhairi, thank you for bringing Waleed back to me" baice komiba yakai hannunsa yadauki rigan daya cire zai wuce, ahankali tadan kallesa jin shiru ganin rigan daya rike yasa ta maida kanta kasa calmly tace "kawo rigan na wanke daman zanyi wanki" rigan ya kalla yace "thanks but no" yawuce yabude closet nasa ya ijiye rigan yafito ganin still tana a tsaye yasa yayi dan gyaran murya dan kallonsa tayi murya chan ciki kaman mai tsoron magana tace "nadafa tuwo uhmmmm..." hakanan maganan ya makale takasa cewa takawomai, ahankali yace "I could use that zan sauko naci, can you make tea please"? Yayi maganan so politely, gyadamai kai tayi dasauri tajuya zata fita saikuma ta tsaya batare data juyoba tace "dan Allah ka aramin wayanka nakira Mama nabar tawa agida" wayan dake gefensa ya kalla yace "zoki dauka" juyowa tayi ahankali tadan kalli gadon wayan na dab da shi dan kallonsa tayi bama ya kallonta agogon hannunsa yake kallo, dan takowa tayi zuwa gefen gadon ahankali tasa hannu tadauka saita juya da sauri tafita daga dakin. EPISODE 50 Kasa tasauka tana taba wayan nasa taga babu password, call logs nasa tashiga taga miss calls na Layla yafi a kirga saikuma Aunt, number Mama tasaka kafin tagama sakawa ma taga Mom2 yafito jimmm tayi saitai dialing number Mama ta taho dinning, har lokacin Waleed abincin sa yake ci, tabude kofa tashiga kitchen, tariga taga komi na kitchen din dazu tashiga hada shayi, daukan wayan Mama tayi tareda sallama ahankali tace "Mama nice" dasauri Mama tace "Safeerah yaya kun tashi Ipy" dan murmushi tayi tace "Mama Waleed yadawo" dasauri Mama tace "Salim ya karbosa?" Murya chan kasa tace "eh ya karbomin shi" Mama tace "Alhamdulillah, Alhamdulilah hope bai masa komiba"? Ahankali tace "gashi chan dai yanacin abinci" Mama tace "kin gani ko amman kika dinga shirme jiya kin masa godiya yanzu?" Ahankali tace "eh, nama basa hakuri" dan murmushi Mama tayi tace "good girl, kinga inda su Ummi ki suka jera miki kayayyaki?" Ahankali tace "eh" Mama tace "tom Alhamdulillah daman nace su dakata da kawo miki ragowan kayayyakin ki especially magungunan da Umma mai gyara ta kawo miki yau da safe wai gudun mawarta kifara sha yau, zansa driver yakawo su" ahankali tace "Mama azo da Yasmeen dan Allah da wayoyina" Mama tace "tom" murya chan kasa tace "ina Baba"? Bata wani daga murya take magana da Mama, Mama tace "wani makaranta sun kirasa kaman za'a basa matsayi na principal yatafi" murmushi tace "Alhamdulillah" Mama tace "tom koma wajen Mijinki sai anjima Allah muku albarka, Allah yacigaba da kareku ya tsare" ahankali tace "tom" katse wayan tayi ta ijiye a gefe tea na tafarfasa sosai tajuya tadauko wani flask mai balain kyau tai tacce tahada komi a tray mai bala'in kyau tasa mug mai kyau da karamin tea spoon da honey tabude kofan kitchen din tafito, zaune tagansa a dinning kusada Waleed, ya karbi bowl din yana ba Waleed dan ragowan abincin daya rage a baki da kansa, bai kalleta ba itama dasauri ta dauke kai, tazo dinning ta ijiye tadan kallesa kaman mai tsoron magana tanaso ta tambaya kota saka masa amman takasa sai kawai tadauki mug ta tsiyaya masa tea dayakejin kamshinsa daga wajen tasa horny bada wani yawa ba ta sa a tea plate ta matsar dashi gabansa gently, saita matsomai da horny da lemon datai slicing sannan ta matsa tadauki plate mai kyau tadauki tuwo ta bude daga leda tasamai a plate, tadauki bowl tazubamai soup dake kamshi, da manya manyan kifi aciki tadan kallesa tanaso ta tambayesa ko tabasa yaji da man shanu, kitchen tawuce ita batamasan yaushe Mama tamata su yaji da manshanu ba datana girki ne tagansu dazu, daukowa tayi zata juyo daidai yana bude kofan kitchen din yashigo rike da bowl na abincin Waleed da spoon din, sauke kanta tayi kasa, ahankali yawuce wajen sink itakuma tafito hadamai abincin tayi tsaf takalli Waleed dake wajen yana kallon abincin data hadama Salim tace "zomuje kai bacci"make mata kafada yayi daidai Salim na fitowa Waleed ya kallesa tareda washe baki Salim yazo ya zauna kusa dashi yadauki tea yakai baki ya kurba kadan yamai bala'in dadi tea, jiya yasayo kayan shayi da kansa ya ijiye a one of the drawers na kitchen baisan ta iya dafawa hakaba, juyawa tayi zata wuce ya sauke tea kai tsaye yace "come back and eat" dan juyowa tayi saikuma batai gardama ba tazo dan bataci abincin ba ina taga kwanciyan hankalin ci, plate tadauka tasaka tuwo guda daya normally she can finish two but kukan datasha yasa batada karfin cin biyu, miyanta aciki tazuba tamike zata tashi Waleed yace "Ummy sit"dasauri ta kalli Waleed hararansa tayi ashagwabe yace "Abeee Ummyyy" maida kanta kasa tayi da sauri ganin iskancin da Waleed yamata kuma harda kai karanta, anatse Salim yace "eat with us Ummy" washe baki Waleed yayi yace "yes Ummy"faracin abincin sa Salim yayi he's not a fan of any miya mai yauki hardly yakeci but this particular one yanada dadi, debowa Salim yayi a spoon yakai bakin Waleed amsa Waleed yayi Safeerah takalli Waleed da bala'in mamaki saita maida kanta kasa tasa hannu dan ita bazata iyacin tuwo da spoon kaman yanda taga Salim nayi ba, she's not comfortable so bata iya taci ba, kusan 5spoon Waleed yayi na tuwon yace "Abeee water" ruwa Salim yadauka yabasa duk Safeerah tahau jin wani iri Waleed bai barsa yaci abinci yanda yakeso ba, batawani ci abincin ba tamike tawuce takai kitchen taga ya dauraye bowl na Waleed ya ijiye a gefen sink din looking dirty, maza ba abinda suka iya, wanke bowl tayi da plate nata da kyau ta gyara wajen sannan tafito bata gansu a dinning ba but taga babu mug na tea Salim, tuwon yaci yabar kadan but ya cinye miyan yaci fish tass, batasan mesa ba hakan yamata dadi komi ta kwashe tawuce dashi kitchen she washed everything ta maida komi right place nasa saita fito daga kitchen din ta goge dinning da towel dake hannunta ta koma ta ijiye tasake fitowa bataji muryan Waleed ba, sama tawuce tana tafiya ahankali ringing wayansa taji a kasa sai alokacin ta tuna ta karbi wayansa ta barsa a kitchen da sauri tashiga sauka kasa kitchen ta shiga tadauka taga Aunt ke kiransa tahowa tayi saman daidai ta karaso taga yabude kofa yafito daga dakin Waleed ya kalleta, sauke kanta kasa tayi ahankali gabanta nadan faduwa takaraso wajen tabasa wayan, karba yayi ya kalli screen din sai yayi picking while Safeerah na satan kallon dakin, Waleed taga yayi bacci abinsa comfortably kan gado ga iPad a kan side drawer na yara, iPad din babban gaske and it looks new, juyawa tayi zata wuce hannunta taji Salim yarike afirgice tajuyo ta kallesa waya na kunnensa yace "Aunt" kokarin fizge hannunta Safeerah tayi sabida shocking datakeji amman takasa sabida yanda yarike, yakai dayan hannun yajawo kofan dakin Waleed da kyau sannan yafara tafiya yana rike da ita gaban Safeerah na faduwa sosai yabude dakinsa ya shiga ya maida kofan yarufe sai alokacin yayi magana awayan yace "I am sorry Aunt, something come up, but gatanan" yakalli Safeerah yana bata wayan, hannunta dabai rikeba tasa ta karbi wayan takai wayan kunnenta while Salim na kallonta kaman zai hadiyeta da idanu, awani irin kunyace tace "ina yini" ran Anty Asabe a bace yake but jin cool voice na Safeerah yasa tace "Safeerah Masha Allah Amaryan mu, jiya mun hada karaman waleema to welcome you amman bamu ganku ba" abalain kunyace cikeda jin nauyi tace "dan Allah kiyakuri laifi n..." hannunsa Salim yasa ya karbi wayan yamaida kunnensa yace "Aunt zan kawota gobe" yayi shiru kaman magana takemai yace "you will talk to her gobe Aunt she has guest now" yayi maganan yana kallon Safeerah da kanta ke kasa dukta kosa yasakin mata hannu ta tafi, jikinta har rawa rawa yake yanda yake rikeda hannunta har lokacin, yacire wayan daga kunnensa yatura a aljihun wandonsa kai tsaye yakai hannunsa saman yalen data yafa da kyau saman kanta dawani irin sauri tadago kanta ta kalleshi takai hannunta ta daura saman gyalen ta wajen kirjinta gabanta na bala'in faduwa, mezai mata? Meyake shirin mata? Shine all abubuwan dake ranta take tambayan kanta, wani mugun kallon daya mata yasa ta maida kanta kasa, hannunsa daya yasa yakama hannunta data rike gyalen dashi a wajen kirjinta yasauke kasa yashiga zare gyalen, runtse idanu Safeerah tayi gamgam yana shakan wani kamshi da wuyanta da gashinta da jikinta gabaki daya keyi, gyalen dayake zarewa yanasa yana kara jin kamshin ta sosai. Ya tsare gashinta da kallo kafin ahankali yakai hannunsa yadaura kan ribbon dake wajen datai donut dashi kawai yakama yaja gashinta yawani zubo kasa va barbaje harta wajen fuskanta damn! She looks hot! Juyawa Safeerah tayl dadan sauri more like gudu zata bude kofan tafice kawai Salim yafizgota tadawo jikinsa kirjinta na buguwa da tasa, kasa daurewa tayi kawai tafashe da kuka sosai tana kokarin dukawa hanata yayi ta hanyar kamata yana sata a kirjinsa, cikin kuka tace "dan Allah karkamin komi, kace fa you don't want anything from me, please Abee" hannunsa yakai yadebo silk hair nata yakai hancinsa yana shakan kamshin da gashin keyi dake kwance masa lissaft, cikin wani irin murya kaman batasa ba yace "I've changed my mind!" Yayi maganan yana daura hannunsa kasan habanta yadago da
Chapter 54 · 0% Book details