Sashe 24
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
karta ci abincin but yunwa na neman halakata saita bude taga waina da pepper soup sai rice da stew yaji kaji manya manyan, deban waina tayi taci sosai tanaba Waleed dayaki amsa, ci tayi tai kat sannan tajita tadawo daidai takai komi kitchen tadauki Waleed sukaje daki ta ijiyesa tawuce bayi wanka tayi tafito kayanta takara maidawa tasaka kayan da Waleed ya cire a ledan sannan tadaukesa suka sauko kasa ta zauna falo zuciyanta sai bugawa yake tanaso takirasa ita tanaso ta tafi tun wuri dan tasan ya ake ciki, ball daya sayoma Waleed da kansa yaron yajawo daga leda yahau wasa da ball din ta tsare yaron da ido he s so happy baisan trouble da Mamansa ke ciki ba. Sunkai kusan 2hrs zaune nan falo sai taji alamun mota dasauri tamike tace Waleed zo tadaukesa tana karban kwallon ta ijiye akasa cike da rigima yace Ummy Balllll hade fuska tayi tace idan baka natsuba zan makeka I m not playing with you today kwabe fuska Waleed yayi yana kallonta tasa hannu tadauki zanin goyonsa tarike tana kallon kofa jira kawai take ya shigo ta tafi. Yana fitowa daga motan yazo wajen kofan saida yafara danna door bell sannan yasa key yabude kofan ganinsu yayi a tsaye, Waleed na ganinsa yashiga kokarin sauka daga jikin Maman aiko Safeerah takallesa da sauri tana hararanshi ko ajikinsa kiciniyar sauka Waleed keyi da karfinsa da yaji. come taji maganan sa agabanta dayake tana fama da Waleed kwata kwata batasan sanda yama karaso gabanta ba dasauri tadan koma baya tasakanmai Waleed yadaukesa Waleed na washemai baki yana kallonsa, calm murmushi Salim yayi kadan yana kallon Waleed din yace kayi kyau Fine Boy? Kofa Safeerah ta kalla ganin ya kulle kofan yasa tai wajen dinning da sauri gabanta na faduwa ta tsaya daga wajen, ahankali Waleed yanunamai ledan dake center table yace juice dan tuntuni yakeso yasha Safeerah tahana, yana dauke dashi yabude ledan idanunsa na dauka kan rigan dayaga ta bude ta maida ledan ta ijiye, ledan maganin da bai kama da an bude ba hannu yasa yaciromai caprisone yabude ya basa yadauko cheese balls ma yabude saiya saukesa akan kujera yace zaka kalli cartoon gyadamai kai Waleed yayi da gudu yana kai juice din baki, TV parlor ya kunna yasamai a Disney Junior volume bai wani yawa ba Waleed yawani natsu yanaci Cheese balls yanashan caprisone gabaki daya attention nasa na TV. Zamu tafi! Yaji maganan Safeerah hakan yasa yajuyo da kansa ya kalleta dasauri ta sauke kanta kasa, dan takowa yayi one two three step dawani irin sauri tai baya itama ta tsaya daidai kofan kitchen gabanta na faduwa sosai, hakan yasa ya tsaya anan falon gefen kujeran da Waleed ke kai yakai hannayensa tabaya ya harde, calmly yace ina zaki yanzu? Dan dago kanta tayi ta kallesa dasauri ta maida kasa, ahankali tace nima bansani ba! Waleed yajuya yakalla saiya juyo da kansa yakalleta yace kina tunanin Waleed? Dasauri tadago kanta dudda bata kallesa ba Waleed ta kalla he s so happy yanacin cheese yana kallon cartoon a tv spidey akeyi abunda yadade bai kalla ba cus ba a musu sub ba, a falon Mama Kubra kuma bai sa yayi kallo ba saidai in basanan, abu taji ya tsaya mata a wuya ahankali tace I will protect Waleed da duka rayuwana How? Yawo a street kina begging da shi under the hot sun, ko kasan bridge dakika ce zaku koma or Kano da people are there ready to kill you! The way kalamansa ke dukan kirjinta ko batasan sanda hawaye yazubo mata wani tsoro na shiga ranta ba, kalamansa just made her thing for the first time kaman abunda tayi was wrong, bayan hannu takai ta share fuskanta da sauri, anatse Salim yace the moment a girl becomes a mother you can t be considering kanka first always you neeed to think of yaranka, danka abinda ka haifa, because of yara koda ana zaginka saikai hakuri iyayenki sunyi hakuri sun jure komi not because they re weak but because of you! Why can t you do that for Waleed ? Wani huci tayi kukan bakinciki da kunci na fitowa daga idanunta tana sharewa da bayan hannu, sauke kanta kasa tayi zuciyanta na yin baki kirin tana wani irin shakkan sa hakan yasa takasa maganan da kyau hannayenta ta harde da karfi gabanta ma mahaukacin faduwa cikin murya yar kankanuwa tace ..ni ..dai ka banni natafi nariga na rantse baram koma gidan ba! Tsareta yayi da idanu yayi shiru hakan yasa tadago kanta jin shiru wlh ayanda taga idanunsa batasan sanda tajuya zata bude kofan kitchen dasauri tafada ba strictly yace t try that! Kasawa tayi ta tsaya jikinta na rawa, lumshe idanu yayi yadan sassauta muryansa yace bazanso this poor innocent boy suffer sabida foolish and childish decision naki ba, you can stay here as long as you want, bring parents naki su zauna tareda ku nabar miki this house! I will give you the papers anjima! The house is yours! Dawani irin sauri Safeerah tajuyo gabanta na faduwa so take ta kalleshi but takasa dan lankwasa kanta tayi ahankali tace thank you amman ni bazan karbi gidanka ba! Tsayawa yayi yana kallonta shima babu wani wasa ko tausasa murya yace idan ego dinki bazai barki ki amshi gidan nan dana baki ba how about nabaki gidan ta dalilin aure! Dummm! Dummm! Dummm! Gaban Safeerah yawani irin fadi this time around saida ta dago idanunta ta kallesa shima kallonta yake fuskansa babu alamun wasa kowani kwana kwana kai tsaye yace marry me Safeerah! Sarawa kanta yayi da bugawa all at the same time batasan sanda ta lumshe idanu ba, is this man okay ko daman ance sojoji nada mental problems ko cus mema yakawo maganan aure? For someone that she just looked yanzu bataga wani sign ko alamu na yana sonta ba ko yakamu da sonta but he is proposing marriage auren mene? Mezatayi da aure? Ita da babu abinda ta tsana kaman aure she promised kanta bazata kara wani aure ba har abada aure daga ina kuma? Juyawa tayi zata bude kitchen tashiga yace t get me wrong! Ba auren ki zanyi ba because ina sonki, or I need wani abu from you or anything nope! On the contrary bakida wani abu dazaisa namaji sha awan aurenki, I don t do small foolish girls! Yayi dan shiru kafin ahankali yace I told you earlier as a mother you don t own your life, rayuwanki belongs to children naki, the moment ka haihu you have to give your all for yaranka, hakkine akanki to protect your children, you need to be strong for them, kajure komi for them, this is the same thing your parents did for you, I spoke to iyayenki, I just left d hospital Mahaifinki na asibiti dawani irin sauri Safeerah tajuyo jikinta na rawa tama kasa magana sai hawaye, calmly yace he is stable for now, mahaifinki was saying he is ready to support you shima bazai kara komawa gidan ba kuje wherever you lead them to, ina zakikai mahaifinki dakeda serious BP kuje kuna bara? Ina zaki kai small little Waleed? How will you manage ki rikesu? Are you trying to jefa kanki a halaka? Idan karban gidan nan dana baki for free hurts your ego so much then ki karbi gidan a matsayin sadaki and marry me that way ba kyauta bane and it s yours kinada right akansa kisa Abba da Mama anan, ke da Waleed i will take responsibility naku, you have from yanzu zuwa dare to give me an answer, let s go to the hospital kawai yajuya yasa hannu yadauki Waleed yawuce yabude kofa yafice Safeera ta kankare a wajen kanta kaman zai fashe maganganun sa were to heavy for her to chew ta fahimta kuma. EPISODE 2 Kusan 7mins yana zaune a mota shida Waleed yanama yaron wasa Waleed sai wannan hausan da yar turenci kadan dayakeji yake masa yana amsasa gogar bata fitoba, kofa yaji an bude hakan yasa yadago kansa dayake tinted ne glass na motan tsareta da idanu yayi bakinta is still showing signs na kumbura, idanun nan sunci kuka sunyi suntum but she still looks very pretty, zanin goyon Waleed ne kawai a hannunta, ganin key jikin kofan ta gaba yasa ta murza ta zare, bakinsa ne yayi motsi yana kallonta yace stubborn girl! Zagayowa tayi tabude motan Waleed yayi wani ihu akan jikinsa yana murna yace Ummyy kalle yajuya sitarin mota ta dauke kai batare data kulasa ba tamaida kofan tarufe, reverse yayi abinsa baice mata ci kanki ba Waleed sai murna yake yana tayasa tuki, saida suka shiga major road yasa hannu daya ya rungumesa gently ajikinsa yace be good okay gyadamai kai Waleed yayi yay lamoo ajikinsa, suna shiga asibitin Safeerah tashiga bin ko ina da kallo idanunta suka ciko da hawaye sosai, parking yayi yabude motan yafito ko ina a hospital din sojojine yana fitowa few sojas dake wajen suka kame suna saramai, da hannu yamusu alamu su bace yahade fuska Waleed sai kallon sojoji yake da uniform ajikinsu, fitowa Safeerah tayi ahankali ta maida kofan tarufe hakan yasa yawuce rikeda Waleed, lurada bata biye dashi yasa ya tsaya yadan juyo ya kalleta hada ido sukayi kiris take jira tafashe da kuka tana kallonshi idanunta suka kara cika da kwalla, anatse yajuya yacigaba da tafiya hakan yasa da kyar tadaga kafafunta dasukai sanyi tacigaba da binsa harciki wani daki taga yayi knocking ya dakata aka budemai kofan Mama tafito tana ganin Waleed a hannunsa yayi kyau sosai sanye da tufafi masu kyan gaske tace laaaa Waleed ayoyo taho tamika hannu cikeda kewan yaron zata daukesa kin zuwa Waleed yayi yamakalkale Salim sosai dadan sauri Safeerah tazo wajen ta rakube tana kallon Mama dataki kallonta cikeda barkwanci tace kayi babban aboki fa Salim dan murmushi kadan yayi baice komiba, gaban Safeerah na faduwa sounding so guilty tace Mama ina wuni ko kallonta Mama batayiba tajuya tace shigo Salim Bismillah tafito ta matsamai gefe shiga yayi ciki Mama tama Safeerah wani mugun kallo haba sai kuka, Mama tanunata da hannu tace idan banzo na mammakeki awajen nan ba basunana Maryam ba, Safeerah, Safeerah, Safeerah sainaci miki mutunci, kinci sa a asibiti muke Mama