Sashe 13
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nothing special, Shamsu shima na ganin zanen yayi tsaki yace danasan baki iya zane ba daban kawoki nan ba doluwa kawai dan kallonsa Auwal yayi yace t be harsh Bro! Duk ahaka muka fara muma ai it s okay! She will get better with time yakalli Safeerah da kanta ke kasa yace t mind Yayanki, you are trying, naga 6weeks zakiyi ko ? Gyadamai kai tayi yace okay zansa secretary dina takaiki HR department zasu danyi magana dake sannan su kaiki inda yadace dake dazakiyi aiki pay, attention and learn bazaki samu problem dakowa ba, for me the only thing da zaisa nayi fada dake is late coming, this is one of the strongest rule na company nan we don t tolerate late coming, be punctual okay Safeerah gyadamai kai tayi ahankali, Shamsu yace wai ke wawiyan inane baki iya magana bane ko bakinki na ciwo ? Dasauri tace toh naji Yaya Auwal Shamsu zai kara magana Auwal ya danna wani bell yayi kara hakan yasa aka bude kofa secretary tashigo tace m here Sir files da komi na Safeerah yabata yace take her to Mr Gorge HR, he will take it from there yes Sir karba tayi takalli Safeerah tace s go beautiful Miss dan murmushi kadan Safeerah tayi tamike tsaye tabita suka fice, ganin Auwal yabita da kallo yasa Shamsu yadanyi gyaran murya dasauri Auwal ya kallesa, Shamsu yace t mind me I m grumpy sabida bacci bai isheni ba Momma tace saina kawota nan, ga yarinyar da shegen shirme dudda tayi aure harda d dasauri Auwal yace Matar aure ce Safeerah ? Girgiza kai yayi yace no bazawara ce! Mijin ya saketa, tanada yaro that s almost 3 now ahankali Auwal yace ayyah that s sad Shamsu yayi murmushi yace but kasan Salma ba my BabySis she s still very single she s only 22yrs dan shiru Auwal yayi yana kallonsa part of the reason baiyi making Shamsu a close friend ba dudda tare sukai Havard University a kasan waje sabida halinsa ne yanada wasu halayya da ya tsana he s strongly against, this less than 5mins sitting yayi abubuwa da dama da bayaso from yanda yayi treating Safeerah, see rayuwan nan not all fingers are equal, akwai masu kudi akwai talakawa but why will u be feeling special sabida kanada kudi kaman kafi talaka? Look at the way yake treating yarinyar sabida yaga yana kallon Safeerah yadauka sonta yake shine harya faramai tallan sister sa taciki Salma, dan murmushi yayi yace wooooh ahh ni inada Babe dina zamuyi aure soon ma jira nake agama na Ya Salim Shamsu yadanyi wani disappointing smile bai kara maganan ba sukayi hira kadan Auwal yasake yin baki hakan yasa Shamsu yatashi yamai sallama yatafi. EPISODE 1 Mr Gorge was so good to her, she must be special dan basu taba accepting yan IT ba, ko yan NYSC, he was kind to her yamata explaining komi tunda IT ne kuma 6weeks zatayi dau zata dinga yin one week a each department sabida tasami vast knowledge on how construction companies work, yace this week she will start with Marketing/Customer Care Service Department yatashi tabisa abaya suka koma first floor wani babban daki that looks like classroom yabude yashiga tana biye dashi mutanen office din sunkai 15, kowanne gaban laptop ga chair mai kyau ga coffee machine da water dispenser, ga TV, ga telephones dayawa wasu na waya, very fine office kaman wani conference room duk aka bisu da kallo cikin murmushi yace we have newbie, she s here for 6weeks IT, her name is Safeerah Shu ibu let s welcome her tashi dukansu sukayi suna tafi duk kunya yakama Safeerah banda school nasu bata taba zuwa organization ko kampani haka ba, tayi murmushi kadan tadanja gyalenta tana rufe bakinta kaman wata yar kauye tama kasa magana balle ta gaidasu, wata mata tazo wajen yar babba haka tana sanye da abaya kafin tai magana Mr Gorge yace meet head of this department Madam Maimuna ahankali Safeerah tace ina kwana murmushi tamata takai hannu ta karbe gyalenta daga wajen baki tace welcome to my dept Safeerah, don t be shy, lets go to your sit takama hannunta Safeerah tabita taja mata kujera ta nuna mata ga laptop awajen tace zauna zama Safeerah tayi ahankali ta sauke jakanta Gorge yawuce yafita Madam Maimuna tawuce wajen coffee machine tasaka paper cup tamata coffee tadauki wani cookie daganan pantry takawo ta ijiye gaban table na Safeerah dasauri Safeerah ta kalleta murmushi tamata tace have some coffee and calm yourself down i will be back to give you proper orientation nai assigning miki task gyadamata kai Safeerah tayi tawuce ta tafi, bakaramin dadi taji ba sai tadan fara natsuwa kowa kuma yacigaba da aikinsa babu mai wani kallonta. Wuraren 11 ya shigo falon, Ammi natare dawata bakuwa makociyarsu ce, ahankali yace ina kwanan ku Ammi tace ka fito zokai breakfast girgizamata kai yayi yace sauri nake Ammi I have meeting with Paresh and Auwal, where are the girls? Murmushi Ammi tayi tace sun tafi school juyawa yayi yace natafi Ammi adawo lpy Allah bada sa yabude kofa yafita, anatse yake tafiya wajen wata black Lamborghini Urus yaje yabude motan yashiga yadauki black glases dinsa yasaka sannan yaja motan gateman dinsa na gaidasa rage gudu yayi yasa hannu a dayan seat na motan yadauki bandir daya na yan 500 dake Wajen yabasa sai godiya yake yawuce yatafi. Wuraren 12 yakai company nasu kwata kwata shi baya parking anan waje, wajen parking motarsa yaje a kasan basement yadan dade cikin motan sannan yafito sai wani uban kamshi yake yawuce yafito direct wani elevator dake wajen ya shiga daya kaisa 3rd floor yafito yawuce wajen wajen wani off office dake wajen gawata secretary dake aikinta awajen bamata lura dashi ba, kamshin turarensa dataji yasa tadago kanta dawani irin sauri tamike tsaye tace welcome back Sir, it s so good to see you batare daya kalleta ba yace thanks I need coffee please coming right up Sir office dinsa yabude yashiga that looks like a suite ya mahaukacin hadu wucewa yayi yazauna yashiga bude files da aka ijiye mai awajen dan ansan yau zaizo ya kunna desktop din yakalli agogon sa he needs to be in barrack by 2 yanada meeting yau da Lieutenant General, glasses na idanunsa ya zare akai knocking kofa yace common in Auwal ne yayi wani murmushi yace welcome Boss thanks ya amsa yana duba files din, aka sake knocking wani dan india ne yashigo sanye da suit zai iyakai 45yrs yace welcome Boss thanks Mr Paresh yafadi still reviewing files din saiga secretary ta shigo tace Sir your coffee just the way you love it ta ijiye agabansa yace thanks Miss Becky murmushi tayi tajuya tafita, yadauki coffee yakai baki ya kurba ya ijiye sannan yakalli Auwal yace mergin na gross profit namu yayi decreasing compare to last year, what happen? Yanda yake magana bazaka taba dauka Auwal kaninsa bane babu wani wasa is just a strict work conversation, bayani Auwal yashiga yi yana hadawa da report na accounting department, meeting din yakaisu har zuwa one but it was productive suka fito dan zuwa salla shida Auwal suka jera sai gaidasa ake duk randa ya shigo idan zai tafi he gives them lot of money araba so ma aikatan sa loves him die, nan masallacin su suka shiga dake nan cikin building din ga AC ga komi. Tasowa Madam Maimuna tayi takalli Safeerah dake aikin shigar dawasu record a computer simple work ta bata as per new comer tace tashi muje salla gyadamata kai tayi tamike tsaye wayanta kawai ta dauka suka fito tare, matar tace sunana Maimuna yarana uku duka mata yata tafarko zakuxo tsara haka murmushi Safeerah tayi tace ya sunansu Aysha, Habiba, Maryam daidai sun iso restroom bayin very clean fitsari tawuce tayi tafito tashigayin alwala, ta gama ta gyara dankwalinta gashin goshinta ya kwanta lub she looks damn beautiful, Madam Maimuna sai kallonta take gyalenta tayafa akai da kyau Maimuna tace muje tunda kin gama wucewa tayi suka fito suka sauka nan kasa hanyar wani door sukayi, Madam Maimuna agaba tama biye da ita, bude kofan sukayi dan corridor ne ga takalma awajen na maza da mata, suka cire nasu Hajiya Maimuna ta shiga masallacin ahankali itama tasanya kafanta ciki ta shiga wani irin sanyi taji ya ratsata sosai ko uban AC mosque dinne oho sai kawai ta kasa motsi ga wajen da few maza dake zaune dan an idar da salla yanzun nan, su mata sai sun shigo sannan zasu bude wani kofa su shiga side na mata asalin kofansu ana gyarawa so dole ta side na maza suke shigowa, Hajiya Maimuna hartakai kofan shiga tajuyo ganin Safeerah na chan kofa tsaye batai motsi ba ta kame yasa tace taho mana Safeerah! Hakanan sunan ya daki kunnensa da zuciyansa dummmm! Rabon dayaji sunan nan tun 5yrs ago! Tundaga that time ko haduwa da mai suna Safeerah bai karayi ko ji aduniya ba sai yau, juyowa Auwal yayi da sauri jin an kira Safeerah saiya mike ganinta a tsaye takasa tafiya yace s probably shy ba a bude kofanku tawaje bane Madam Mamu? Madam Maimuna tace eh Yallabai ba a gama gyaran ba Safeerah yakalla da itama daidai lokacin tadan dago kai ta kallesa jin muryansa, Auwal yace wuce kije kiyi salla ahankali ta gyadamai kai tace tom! Wani kalan juyowa Salim yayi dasauri azabure kaman zaki daidai Safeerah na shigowa kanta akasa tanakai hannunta tana shahare ruwan gefen fuskanta looking nervous tawuce wajen door din tana tafiya ahankali dabazai taba mance yanda take tafiya ba, bugawa kirjinsa yashiga yi dum! Dum! Dum! Baiga fuskanta da kyau ba, but side view nata looks exactly like her! Especially dan gashin daya gani a goshinta, her voice, the way she walks, but wannan kaman tafi Safeerah tsayi, wannan tadanyi jiki kadan, though ba sosai ba, but takara shekaru 5 Safeerah can be this tall da jiki haka ai takara girma da wayau she s an adult now, is something wrong with him? Gizo idanunsa kemasa sabida he s looking for the girl madly? How can Safeerah be here? Juyowa Auwal yayi yakallesa ganin yana kallonsu yasa yace t be offended Yaya, she s our newbie,