Sashe 12
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba Baba ya zube yana hada hannu yace Mama Kubra wanake dashi banda ke? Ina kikeso naje? Taya zan fara? Ga makanta? Bara kikeso naje nayi cikeda rashin mutunci tace sai me toh akanka aka fara baran, sabida na rufamuku asiri sai ahaumin aike, mara mutunci kawai butulu daku marasa godiyan Allah matsalan talakawa kenan kamusu dare su maka rana lumshe idanu Safeerah tayi hawaye na zubomata this is the reason why she never talks take hadiye komi, cus everything she says affect parents nata more, they are being humiliated, abune ya tsayamata a kirji ganin yanda suke begging Momma tana duramusu zagi baki tabude zatai magana kawai sai zuciyanta ya karaya ta fashe da kuka sosai tace Momma dan Allah kiyakuri, wlh wlh Mama bata aikoni komiba, baki fahimci maganata bane dan girman Allah kiyakuri Ijiyan zuciya Momma ta sauke tana kada kafafu tace okay zan salllami masu gadina! Shu aibu ka tattara matarka da yarka ku koma dakin masu gadi dake gate dagayau kaine zaka dinga bude gate tunda na kore ka bawai kanada wajen zuwa bane dasauri Baba yace naji na yarda zuciyan Safeerah ya mugun sosu, bude kofan sama akayi Salma tafito dawani mahaukacin kayan bacci ganin su Mama duke gaban Momma a falo yasa ta harari Safeerah tace yarinya sai mugun hali kuma saidai aiki ya kashe Uwarki da Ubanki yanzu suka fara, yazama gateman your mother kuma our cook and maid die da bakin ciki, in kinyi zuciya ke nemo naki kudin kawai an dawo gidanmu ana cinye mana kudin gadon da Baban mu ya barmana, kai Baffa dalla tashi kafita tashi Baba yayi ahankali yajuya yawuce idanun Safeerah suka kada sukai ja. EPISODE 1 Momma itama ta dakama Mama tsawa tashi kibar nan kekuma wuce kije ki shirya kafin nasa Shamsu ya tattakamin ke da gudu Safeerah tayi kofa Salma tabita da kallo saikuma tazo wajen Momma tazauna tace Wlh Momma I hate Safeerah, I hate her ta uban Yaya ma tafini kyau ?Dasauri Momma tajawota jikinta Salma ta kankameta ashagwabe, Momma tace wat are you saying Salma? Yarinya fara kal dake inake ina hada kanki da black skin Safeerah haba haba, ai sama taiwa yaro nisa saidai yadaga fuska ya kalleta shafa gashinta Salma tayi tace Momma harda gashi tafini fa dasauri Momma tace Kin fita keda kesa relaxer jibi gashinki common stop the comparison kina ragema kanki daraja ne, the kind money kike spending on your body why will you compare kanki damai shafa alayyadi ? Turo baki Salma tayi ta bala in jin dadin maganan mamarta tai blushing ta gyara zaman kanta a cinyan Momma tace re the world best Momma Dakinsu Safeerah tabude kofa ta shiga idanunta sunyi jaa, waje tasamu akujera ta zauna hawaye na saukowa daga idanunta tana gogewa da bayan hannu, ita kadai tasan metakeji azuciyanta, itafa da ace ita suke zagi, suke ciwa mutunci, suka maida jaka wlh bazata damuwa as long as iyayenta nada martabansu da kimansu, mesa Momma da yaranta this small Salma ke zagin mahaifinta da mahaifiyarta? Why? Wlh kawai tausayin su Mama takeji kuma harda bataso taja musu fitina dasaitama Salma dukan da akace ta zagi Baba bazata karaba, marasa tarbiya kawai da girmama na gaba dasu, she hated gidansu na Kano sabida yan daban anguwansu but yanzu she rather lives there sau dubu da wannan rayuwan gidan na Abuja wani kalan kaskanci iyayenta ke facing? Zata nemi aiki da zai taimaka mata tarike iyayenta da danta, saikuma tai shiru nawa ne kama haya? Nawa abinci? Asibitin Baba, abincin Waleed? How can she do all of those? Itada batada any qualification, takai almost 20min kuka take sannan ta tashi ahankali ganin seven yayi tawuce dakinsu tabude kofa ta kalli gado Waleed na bacci abinsa zuwa gaban gadon tayi ta duka takai hannunta tashafa kan Waleed murya chan kasa tace Waleed pray for Ummy kaji! I don t want this life for you my Baby tai maganan ahankali takai dayan hannunta ta goge fuskanta sannan ta mike tawuce bayi ta watsa ruwa a gurguje tafito Vaseline nata ta shafa ta warware gashinta da sauri gashin yazubo saura baifi 2inches yakai waist nata ba gashin baki sosai ta shafa man kitso tadan taje sannan tasake packing tai donut da bakin sannan tabude sip din tanada tufafi ba laifi tun na akwatin ta na zamanin aurenta ne, wani blue atampa tadauko gown aka maga ta saka sannan ta dauki sky blue gyale mai duwatsu masu kyau babba taciro sannan tayi dauri taciro file na credentials nata datai photocopy tadauki bagpack nata tasaka sannan tasaka flat shoe tafesa body spray nata mai dadin gaske tafito, tajuyo ganin Waleed na bacci still tafito tabude kofa tafito tsakar gida tayi kyau sosai wlh gata da tsayi ba sosai ba dai, she looks so good, flat din tawuce tabude kofa ahankali Momma tagani da Shamsu suna zaune a dinning suna breakfast ya shirya tsaf cikin kananun kaya duk suka kalleta karasawa wajen tayi tace Ya Shamsu ina kwana wayansa yadauka da car key yamike yace muje ke I have somewhere to be kina batamin lokaci gyadamai kai tayi Mama tafito daga kitchen rikeda kula Safeera tace natafi Mama Mama bata kalleta ba gudun kar ace tai laifi tace adawo lpy Safeerah tajuya tabisa suka fito compound Baba ya wanke motarsa tsaf yana kara gogewa sai sheki motar take suka taho wajen, yayi murmushi yace an fito sannu da kokari Shamsu nagode sosai, Safeerah sai an dawo ko, ayi addua, Allah bada sa Ameen Safeerah ta amsa ciki ciki dan fushi take da Baba, Shamsu bai tankaba yashiga motan itama tashiga gaba yaja motan aka bude musu gate suka fice, saida suka shiga kan titi cikeda isa Shamsu yace saura mukaje ki disgani! This is number one biggest construction company a Nigeria kaman irin su Julius Berger haka suke, suna gina titina, railways, estate etc, this people are bastardly rich, the Maradis kenan! Kudinsu gado sukayi tundaga zamanin kakannin kakanni and gasu all of them are bless, Babansu shine Maradi Jet co yana harkan jirage he s the only person a Nigeria dake kawo jirage yana saidawa yana bada shatter, sai dansa shine mai Maradi construction din nan Babban Soja ne kaman wasa yabude this construction company boom sun zama global, bama ya iya managing abokina dawani Indian Man Paresh ke mishi managing company, sai kanwarsu Layla tana auren dan shugaban kasan Nigeria sai sisters dinsa biyu da basuyi aure ba lemme even tell u I m trying to see yanda zan samu daya na aura sabida family mu yazama so powerful but that big brother nasu baya wasa and seems he doesn t like me, nafara magana da Lubna yahanata tacemin school zatayi she blocked me so dan haka banso ki kofsani, mind your business kiyi aikinki kibar wajen kidawo gida, wlh if you do anything dayasa aka kirani I will kill you Safeerah u hear me yadaka mata tsawa gyadamai kai tayi tace naji Ya Shamsu company sukakai yanada girma tsaresu akayi a gate saida Shamsu yakira Auwal yasa aka barsu suka shiga company is so big ga manya manyan motoci na goni daban daban parked a big space din, parking yayi inda ake parking sannan yafito ahankali Safeerah tabude motan tafito wani iri jikinta yamata saitaji wani irin tsoro da anxiousness irin wanda kakeji din nan idan kaje sabon waje tafiya Shamsu yafara hakan yasa tabisa tana tafiya ahankali suka shiga building din, receptionist ne a lobby din saiga wani status na ginin gida da titi anyi komi me kyau is just a work of art ta tsaya tana kallo Shamsu yafara tafiya jin shiru yasa yajuyo ganin ta tsaya tana kallon abun yasa yaji kaman ya dura mata ashar amman ba dama a kufule yace Safeerah! Firgigit Safeera tajuyo da kanta ta kallesa yamata wani mugun kallo ta taho da sauri kanta akasa suka wuce 2nd floor wani office da aka rubuta CEO suka wuce secretary tace are you Mr Shamsu? Dasauri Shamsu yace yes yes murmushi tayi professionally tace welcome Sir, Mr Auwal is expecting you tayi maganan tana bude musu office Shamsu yace thank you ya shige Safeerah biye dashi ta shiga tana zaro manya manyan idanunta tana kallon office din da bata taba ganin me kyau dinsa ba ga wani mutumi zaune gaban table yana magana dawasu ma aikata dasuka karesa hakan yasa tashiga bin ko ina na office din da kallo kaman bakauya while Shamsu yasami kujera yayi zamansa comfortably, shikuma Auwal ya sallami ma aikatan suka juya sai alokacin idanunsa suka sauka kan wata yar yarinya dayabi da kallo tundaga kan kafafunta har zuwa saman kanta Shamsu yataso cikin murmushi yace Boss Auwal mutumina suka wani kashe hakan yasa Safeerah ta natsu takallesu Auwal yace Shamsu wai har yanzu kaki aure Shamsu yace kai kayi ?Suka kara kwashewa da dariya sannan suka saki hannun juna Auwal yakoma yazauna yakalli Safeerah yace Sister ka ce ? Kallon Safeerah yayi datazo wajen table din da sauri gabanta nadan faduwa tace ina kwana shiru yayi yana kallonta saita sauke kanta kasa, murmushi Auwal yayi yace you remind me of Lubna kanwata haka takeda tsoro, sit down please yanuna mata kujeran gaban table din zama Safeerah tayi ahankali, Auwal yace give me the necessary document bagpack nata tabude taciro komi tadago kanta tamikemai karba yayi yashiga dubawa saiya dan dago yasake kallonta kanta akasa saiya kalli Shamsu yace kacemin kanwarka dan sosakai Shamsu yayi yace kaga surname dina da nata daban ba well kasan Momma da kwashe kwashe woman of people, wani brother ta tadauko daga chan Kano da iyalansa itane cinsu shan katsesa Auwal yayi yace I get she s your cousin Sister dan yatsine fuska Shamsu yayi baiyi magana ba, saiya sake murmushi yakalli Safeerah da kanta ke kasa yace welcome to Maradi Construction Company Malama Safeerah dan dago kanta Safeerah tayi takallesa saita gyadamai kai anatse tace thank you Sir zaro idanu yayi yace wani Sir call me Yaya Auwal tunda ni abokin Yayanki ne can I see designs naki gyadamai kai tayi tasake bude jakan taciro wani files ta basa ya karba, to be honest she s an average designer bawai ta iya zanen hauka dinnan dazasuyi wowing naka bane,