Sashe 49
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
babu wasu outsiders haka, babu kuma mutane dayawa, ga abinci da chefs sukayi makota sun shigo anata sa alkhairi babu wani hayaniya hira kawai ake while Safeerah na sama da su Salma da Yasmeen, Safeerah duktai zuru zuru kaman auren farko, Salma taci uban makeup ranta fess sai dadi takeji har Yasmeen na tambayanta murnan metake haka tace ina ruwanta. Wajajen asir makota suka watse and sun ba Mama gifts wlh some money, Baba shima yadawo gida abunsa yarage yisu yisu suka rage sai hira ake kowa yayi kyau, dayake kofan falo abude sabida baki nabarku shigowa falon wata hamshakiyan mata tayi tana sanye da lafiyayyen lace bayanta wani matashi ne da akalla he will be 33yrs yana sanye da jean crazy dayake a yayyage dawata shirt da botura uku na kasa kawai ya rufe sauran na saman a bude babu ko singlet a jikinsa yasa bakin glass a idanunsa bakinsa da cingam yana tauna doss doss doss kaman mace, dudda akwai glasses a idanunsa but kansa na kallon Waleed dake rike da ball a tsakiyan dakin ganin baki yasa ya tsaya yana kallonsu kaman yaga tv yana sanye da milk gizna mai kyau ba babban rigan a jikinsa just jumper yarage. Kaman yanda matar tagaba itama ke kallon Waleed sosai dukansu babu wanda yayi sallama, mikewa tsaye Baba yayi, haka ma Mama tana kallonsa sai Zainabu, itakuma Momma nadaga zaune tana kallonsa tai wani smirking tareda daura kafa daya kan daya ta kada, gabaki daya fara a da walwalan Baba bacewa yayi daga fuskansa kaman ba Baba ba, babu walwala akan fuskansa yace meyakawo ku gidana? Waya baku izinin shigowa gidana ? Taba baki matar tayi ta karaso cikin falon tazauna kan kujera tana kallon Waleed, shikuma guy din yakai hannu yazare glass din idanunsa, idanunsa sundanyi ja kadan sun kankance kaman wanda yayi shaye shaye yataho yana bouncing irin na niggas dinnan yazo gaban Waleed yaduka tareda yin murmushi yace Hey Yhoo Kiddo Wassup Dan turo baki Waleed yayi ganin strange faces yayi rau da fuska zai fashe da kuka Baba yasa hannu yadaga Waleed ya daukesa cikin daka tsawa yace nace mekazo yi agidana Abbati! Meya kawoka ? Mikewa tsaye Abbati yayi yakai hannu yana goge fuskansa yana yatsine fuska yace damn! Kadinga matsawa baya idan zakai magana wannan yawu haka ran Zainabu baci yayi takalli matan dake zaune ta daura kafa daya kan daya tace Hadiza meya kawoku gidan nan? Tayaya ma kukasan gidan nan? Idan da kunyi anyi hakuri not anymore talk to yaron nan yakama kansa yasan inda yake karyace zai raina Malam agidansa hannuwa Abbati yadaga sama yana daurewa a kunnensa yace enough enough enough! I hate ihu guys! Yafadi yana yatsine fuska, Baba yace get out of this house! Wani kallo yama Baba yanuna kansa yace you think I enjoy being here?! Common nazo na karbi wat belongs to me ne? D ana nazo karba! Ba Baba kadai ba hatta Mama da Zainabu saida gabansu ya buga dim! Hadiza na daga zaune tace before kufara this and that kome kuka kashe akan Waleed tundaga kan cikinsa, har haihuwa, har zuwa yau arubuta mana zamu biya but munzo karban danmu! Kuma babu uban wanda ya isa yahana tunda dai d a na Abbati ne, shi yayi cikinsa, shikeda hakki akan Waleed ba wani ba wani yar dariya Mama tayi takalli Hadiza tace did you just say hakki?! Ku kunsan me hakki? Baku da d a a hannunmu, Waleed dan Safeerah ne kadai not dan Abbati bushewa da dariya Abbati yayi sosai yana tafi yana dan tangadi yarike cikinsa yanayi kafin chan yayi shiru yakalli Mama yace idan kin isa yau ki hanani daukan d ana! Yajuya ya kalli Baba yamika hannunsa yayi murmushi yace zonan Kiddo? Come to Pops Lamo Waleed yayi jikin Baba cus Abbati looks creepy and wired a idanunsa, haushi ne yakama Abbati dan baida hakuri yanuna Waleed da yatsa yana dakamasa tsawa da saida gidan ya amsa yace kai zonan nace, ina wasa dakai ne! Dan Mace kawai! Fashewa da kuka Waleed yayi yakankame Baba atsorace Baba yace wai mehaka Abb fizge Waleed Abbati yayi daga hannun Baba yana hankada Baba yafadi haryana bugewa da table cus ya shammacesa daidai Safeerah na saukowa dan taji tsawan Baba dazu Salma da Yasmeen biye da ita while Mama da Mom na daga Baba up dasauri Momma tamike tace Abbati mehaka? Ko yaronka kazo karba we do it in a civil way why are you being aggressive jibi yanda ka kayar da Shu chak Safeerah ta tsaya tama kasa motsi jikinta kawai yahau rawa tana kallon yanda Waleed ke kuka yana ihu a hannun Abbati yana turesa yanaso ya sauka yagudu amman Abbati yarikesa gam Waleed yakasa motsi, Hadiza ta tashi tace muje dasauri Mama tasaki Baba tamike kafan Waleed tarike tace saidai kaje damu gabaki daya ture Mama yayi Safeerah tace Abbati! Chak yajuyo, hada idanu yayi da Safeerah hakanan gabansa yawani irin fadi dummm! Tana sanye da wani black and red lace Ya Allah! Yamata kyau na bala i, tayafa red veil babu makeup a fuskanta but wlh ka kalleta saika kara kallo sabida yanda tai kyau da baitaba sani tanada shi ba, sak Amarya lallenta yayi kyau na bala i, lumshe idanu yayi yana tuna all his moments da ita, takara girma, lokacin nan kirgan dangi ne a kirjinta but look at how sexy and cute she is now, Safeerah is the only virgin daya taba ci arayuwan sa and he enjoy those moment yaso ya more da ita but takama tai ciki, sosai gabansa ke faduwa daya rasa dalili amman yadaure yahade rai kaman zaki yana kallonta, tahowa Safeerah tashigayi dudda tana tsoronsa da shakkan sa but akan danta she can do anything Wallahi a duniyan nan, tsayawa tayi agabansa tana kallon kwayan idanunsa, idanunta sun kada sunyi jaaaa tace where do you think you are taking my Son toh? Kallon Safeerah Abbati yayi yakara kallo Safeerah dake fitsari a wando lokacin nan tsabagen tsoronsa ne ke ke kallonsa right into his eyes tana mai magana haka, cikin wani kaskantaccen look daya mata yace who do you think you re dazaki questioning Abbati? I am Waleed s mother! Tafadi azafafe, tace ka ijiyemin d ana ka wuce kabar gidan nan cus you are not welcome Waleed daya matse gam yana kuka yace Ummyyyyy comeeee, zoooo matso wa tayi dab da Abbati kaman mahaukaciya dan kukan Waleed yakara haukatata tace nace ka ijiyemin d ana! Bakaga kuka yake ba he is afraid of you, ka ijiyemin d ana Malam hannu Abbati yakai akufule zai kaimata duka sabida yanda yaga tanamai tsiwa Baba yataso azuciye yarike hannunsa gam yana kallonsa ransa abace yace as long as inada rai kagama taba lafiyan y ata! Ka ijiye mata danta Safeerah da hawaye na gab da zubomata ganin yanda Waleed ke kuka ya matse yaron he is hurting him tace nace ka ijiyesa you re hurting him, drop my son and get out! Wani murmushi Abbati yayi yasake matse Waleed da gangan kaman zai kashesa yace yaron nan d ana ne nina miki cikinsa kika haifesa, my blood runs in his veins, my DNA is all over him, ko a musulunci nafiki iko da Waleed! So listen very well to wat I m about to say to you Cikin kakkausan murya yace wat ever kika kashe akan Waleed give me the bill I can even pay you here just sabida nafita daga hakkin ki, but as long as I am alife d ana bazaije gidan wani yayi rayuwa ba! Wani bazai tufatar da d ana ba! Ko wani ya ciyar da d ana ba, you have two choice kodai kije kiyi zaman aurenki Waleed natare dani! Koki fasa auren nan muyi aure mu raini yaronmu tare Allah ya kyauta! Komai kama dakai bazan taba aura ba balle kai Abbati! Banama makiyini fatan aurenka balle ni! You re nobody dazaka gayamin mezanyi and Waleed bazai taba zama dakai ba, baka isa karabani da Waleed ba! Mutuwa kadai ne zata iya rabani da yaron nan not you, not your family, not anybody aduniyan nan! Sosai yake kallonta wani wutan so hakanan yaji yana fizgansa ta mahaukacin masa kyau and she smells magical, gyadamata kafada yayi yace okay then you make your decision loud and clear yajuya zai wuce azuciye Safeerah tarikeshi daidai kuka na zuwan mata hankalinta na tashi sosai tace wlh bazaka tafi da d ana ba shima Waleed yakara rushewa da kuka ganin mamansa na kuka wucewa waje abinta Hadiza tayi ta kunna mota tai reverse abinta, Zainabu ta kalli Momma tace wai bazaki magana ba Yaya kene kikasan mutanen nan, Hadiza ba kawarki bace Momma cikin fada tace nace me? Ko kotu akaje shine uban Waleed kuma Safeerah bata isa ta rabasa da dansa ba wlh, yanda takeda iko akan Waleed haka yakeda shi they just need to find solution cikin kuka sosai Safeerah tace baida iko akan Waleed da bayaso! Cikin dayaso ya hallaka! Yamin dukan bala i just sabida cikin yafita, ya tsani cikin ya tsani Waleed an kirasa an gayamasa na haihu yace ba nasa bane bayason yara, why is he coming back for him all of a sudden now?, idan kaga kafita da Waleed a gidan nan yau saidai idan na mutu! Abbati baiyi wata wata ba bayan hannunsa yakai gefen wuyan Safeerah yamata wani mummunan duka dayasa kowa na dakin saida yayi ihu Safeerah tai baya a sume Mama na tareta, Baba ya chakumesa yace Abbati! Hankade Baba yayi da kyau Baba yafado kan Mama, Zainabu, Yasmeen da Salma dake kan Safeerah data sume tsabagen yanda Abbati ya watsar dashi yayi kofa yafice da sauri da Waleed dake kuka yashiga mota Hadiza tajasu sukabar estate din Baba har jiri jiri yake gani, Mom takamasa ya zauna Yasmeen na kawo ruwa ana watsama Safeerah amman shiru bata farfado ba, ahankali Baba yace ku kamata kusa akan kujera kamata sukayi suka kwantar yace kubata iska zata farka sumar da ita yayi da gangan bata iska sukayi kowa yayi shiru Mama sai goge hawaye take da bayan hannu she knows how much yarta ke son Waleed, Baba na zaune yaciro wayansa jiri jirin dayake gani yasa ahankali yace Yasmeen zoki