Sashe 43
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dubasa securities sun sansa but baima sani ba sabida kallon Safeerah dayake, horn da akamai yasa yaja motan yashiga dawani jaraban gudu, yana kallon sanda ta tsaya taja gyalen zatacigaba da gudu dan ta cinmusu yayi wani wawan parking da saida tires nasa sukai screeching making scary sound da saida Safeerah ta tsaya ta bala in firgice dan ta dauka an kusan bigeta ne ko hatsari akayi sabida yanda tires sukai kara takai hannayenta biyu tadaura a kirjinta tana wani irin nishi tana kallon motan da gabaki daya tinted ne batasan na waye ba, wani irin kallonta Salim yakeyi daga cikin motan tundaga saman kanta da gyalen ya zame yayi baya ana ganin gashinta zuwa wuyanta dayake iya ganin skin din, zuwa kirjin ta da shi yake abude gabaki daya babu mayafi awajen, jelan gashinta na lilo kawai yabude mota a zafafe yafito yamata wani kallo yana maida kofan yabuga saida jikinta yayi motsi sabida kara kirjinta yashiga bugawa ganin yanayin sa tama rasa mezatayi bakinta na motsi, tana tuna all abubuwan daya gayamata jiya, hannayenta suka shiga rawa takai daya tana kokarin jawo gyalen yarufe kanta da kyau tama kasa ja cus bamataji gyalen saman kanta ba tace get in the damn car! Ya daka mata tsawan da saida taji kaman cikinta ya hargitse batasan sanda tasa hannu tabude motan ta shiga ciki ba tamaida kofan tarufe bude motan yayi yashiga ya kunna tanaso tacemai su Waleed amman takasa magana yayi wani crazy reverse azuciye saida yabuge flower pot nawani gida yajuya zuwa kofar gidansu yayi parking yajuyo yakalleta cikin kakkausan murya yace wani kalan shiga ce wannan? Yanuna kayan jikinta, kasa magana Safeerah tayi wlh gabanta faduwa yake sosai, idanunsa looks kaman zai kasheta tsabagen fushi. m talking to you Safeerah! Runtse idanunta tayi jikinta har zabura yake tace ampa da gyale cikin zafin zuciya Salim yace haka matan auren gidanku ke sa kaya? Kasa magana tayi, buga sitarin mota yayi yasaka mata tsawa sosai yace magana nake miki, is this how matan aure ke sa kaya gidanku? I hate loose girls masu exposing jiki, look at your hair outside, gyalenki not covering your hair, your neck and jikinki, kina gudu akan titi? Wat is this? So kike duk mazan duniya suga jikinki susan kinada kyau? Mena gayamiki jiya? Kinsan ke matar aure ce ? Yanda yakema Safeerah ihu da wani zai fito zai iyajinsu, jikinta rawa yafara na bala i saitaga yakoma mata sak Abbati, this is yanda yake ihu yadawo gida tsakar dare especially idan yayi shaye shaye, daganan ya zare belt yafara dukanta yamata lis sai yahau kanta ba imani, yanda jikinta ke rawa was so intense da har kujeran datake kai yadauka takoma baya sosai ta jingina da kofa takasa kallonsa sai lips dinta dasuka fara rawa sosai, ta mugun mugun tsorata da Salim cus of the way he behaves, ijiyan zuciya Salim ya fuzar ransa ya mugun mugun baci kaman zai haukace and he sees ya mugun firgitata shida yakeso tarage tsoronsa, he just needs water to calm down a bit dan kirjinsa tafarfasa yake hakan yasa ya yunkuro dan ya mika hannu yadauki bottle water abaya wani irin ihu Safeerah tayi. Mamaaaaaaa! Wlh da suna waje ba mota ba ihun datayi sai duka estate din nan yadauka dawani irin sauri ya kalleta kunnuwansa na amsa ihu daidai tawani taho luuuuu zata buga kanta a gear yakai hannunsa rufff tafada kan hannunsa gyalenta na faduwa jikin kujeran, bugawa kirjinsa yayi ihun daya mata shine harya tsoratata ta sume haka or wat? Ahankali yakai dayan hannunsa yadaura saman soft black gashinta yadago kanta daga hannunshi wani luuuu tadago muryansa ya daidaita yace Safeerah! But ko gezau, faduwa gabansa yashigayi sai kawai yadan jirkito yajawota yasa kanta akirjinsa yakai hannunsa daya yadauki bottle water abaya yazo dashi gaba yabude da sauri ya tsiyaya a hannunsa ya ijiye goran yakai ruwan ya shafa a fuskanta, calmly yace Safeerah! EPISODE 4 Motsi hannuwanta suka shiga yi sai kawai jikinta yahau rawa takai hannuwanta takama hannunsa dake wajen fuskanta gam, today is the first time hannayenta ke sauka akan wani bangare na jikinsa, hannunta is so soft and warm, ture hannunsa tayi da muryan da bata fita fa kyau tace karka dakeni dan Allah Abbati, kayakuri Innalillahi surutai tafara da at a point baya ganewa sai kawai yakai hannuwansa biyu bayanta yasata a kirjinsa da kyau yawani matseta yana daura bakinsa saman kanta dake kamshi sosai yace shiiiiii it s okay babu wanda zai dakeki! Shiiiiiii ahankali tasoma rage surutan datakeyi saitai shiru tareda manna kanta ajikinsa shima sai yayi shiru having wani kalan feeling of peace da natsuwa da bai taba jin kalansa ba tunda Allah ya halitto sa a duniya, motsin datayi yasa ya zare hannyensa daga bayanta yana zare fuskansa daga saman kanta, bude idanunta rass Safeerah tayi jinta a kirji mai bala in taushi da kanshi yasa adaburce tafito daga jikinsa tana komawa baya tama kasa kallonsa sai hannayenta data daura saman kanta ganin bataji gyalenta ba yasa tajuya mai baya tana neman gyalen, gashinta yabi da kallo kasa daurewa yayi yamika hannu yataba jelan gashinta dasauri tajuyo hakan yasa yacire hannunsa jin gashinta ne, tadaura gyalen saman kanta, ahankali tace m sorry bazan kara ba cikeda isa yace good! The next time kika sabama dokata you will be punished dan kallonsa tayi aranta tace wani irin miji kaddara yasa naje na aura? Ko tausayina baijiba na suma a reality ta gyadamai kai batai magana ba, dan sassauta murya yayi yace wacece ke tare da Waleed? Anatse tace my cousin Yasmeen yarinyar Ummi dakai magana da ita baisake cewa komi ba yace kawomin credentials dinki gyadamai kai tayi tabude kofa ahankali tafito ta maida kofan tarufe duk yanda yaso yadaure kasawa yayi hakan yasa yabita da kallo sai yaji abun nakara bata masa rai yanda tafito ahaka yadena kallonta, files na credentials dinta tadauka har tafito daga dakin nata sai ta sami kanta da komawa tadauki maroon hijab dake kan sallaya ta warware tasaka tafito, yana zaune cikin mota yaga tabude kofa ganinta sanye da hijab saiya sami kansa da tsareta da wasu mayun idanu hakanan zuciyansa tamai dadi sosai kusan ta goge duk wani haushi dayaji earlier dawowa tayi tabude motan da sallama tashigo tamikamai karba yayi yace okay zaki iya tafiya gyadamai kai tayi sai chan da murya chan kasa tace naje na nemo su Waleed? Jin yamata shiru yasa tadan kalleshi ahankali tace Yasmeen batasan ko ina ba a Katsina take zama tazo hutu ne maybe bata gane gidan bane saisa basu dawo ba har yanzu batare daya kalleta ba yace koma ciki i will look for them gyadamai kai tayi tafito ahankali tamaida kofan tarufe tawuce tashiga ciki yatada motan yayi kasan layin hanyar dayaga sunbi yabi hango playground na yara yasa kawai yayi wajen Yasmeen yagani tsaye Waleed na wasa sosai tana mai clapping, murmushi yayi kadan yana kallon Waleed wlh he loves the boy har ransa, parking yayi yabude mota yafito yazagayo Waleed na cikin wasa kaman ance yadago kansa yaga Salim dawani irin sauri yataho da gudu bai damu da kasan dake jikinsa ba Salim yabude masa hannu Waleed yazo da gudu kawai yadaga sa sama yace Assalamu Alaykum Champion Waleed Waleed yace kumu salam murmushi yamai Yasmeen takallesu ganin Waleed ya sansa yasa tace ina yini gyadamata kai yayi batare daya bata second look ba yace muje gida bude gaba yayi yasa Waleed yarufe kofa yazagayo ya shiga mazaunin driver hakan yasa Yasmeen tadan taho tabude baya cikeda fargaba tashiga ta zauna, Salim yaja motan Waleed na wasa a kujeran har gidan parking yayi Yasmeen tace muje gida Waleed make mata kafada yayi, batare daya kalli Yasmeen ba Salim yace shiga ciki zan dawo dashi batai musu ba tace toh tasauka yatada motan yabar wajen, shopping yayoma Waleed sosai harda kayan wasa sannan yadawo dashi yakira Safeerah awaya yace fito fitowa tayi shima yafito dauke da Waleed yace Waleed go to Mom dasauri Waleed yamikamata ball dinsa yace Ummyyy see murmushi Safeerah tayi tace laaaa Abee yasai maka ? Dan kallon Safeerah Salim yayi itama saida tai maganan taji wani irin kunya saitaga kaman tana chusa masa yaron da ba nasaba, Salim kuma har cikin ransa yaji dadin sunan datake koyama danta yakirasa dashi, karban Waleed tayi batare data bari sun hada ido ba tace angode tajuya tawuce ciki baya yabude yaciro ledan yazo wajen kofa ya ijiye yawuce mota yamata text akwai kaya gaban kofa sannan yatada motansa yabar wajen, saida sukaji tafiyansa Yasmeen tace ke wannan hadadden mutumin ne mijinki? Kinga yanda yakeson Waleed kuwa kai amman wlh baida kirki, baiso na shiga gaba yasa Waleed awajen ya aikani baya maganan ba karamin dariya yaba Safeerah ba tace Alhamdulillah na dauka ni kadai na ke ganin baida mutunci kema kin gani Yasmeen, saisa bana sonsa kawai sabida su Baba ne Allah ma yasani, amman ni I hate men, I hate aure! daidai text dinsa na shigowa, ahankali tamike Yasmeen tace ina zaki ? Batai magana ba tabude kofa taga katuwan leda saitai gmmm hakan yasa Yasmeen tazo wajen tasa hannu tadauka tace Waleed zokaga toys naka da sauri Waleed yazo wajenta suka zauna anan falo suna fito da komi Safeerah tamaida kofa ahankali tarufe tadawo kawai ta zauna tai shiru tana kallonsu barinma yanda Waleed ke murna toh he has not been getting toys ga snacks dayawa daban daban na yara, Parking mota sukaji anyi dasauri Yasmeen ta tashi tai window ganin su Mamanta da Momma harda Salma yasa tajuyo cikin whispering tace ke harda matar nan da yarta daidai nan Baba yayi sallama yashigo Mama biye da shi sai Mom, sai Momma da Salma dasukabi ko ina na gidan da kallo idanun Salma na sauka kan iPhone 16 data gani a hannun Safeerah taji wani abu a wuyanta, yaushe su Baba da Mama suka fita daga gidan nan? Tasan suna nan fa dazu, suna hada idanu da Momma Safeerah ta sauke kanta kasa tajuya ahankali tace ina yini Momma lafiya kalau murmushi Zainabu tayi duk aka zazzauna Safeerah ta wuce zatai hanyar stairs Baba yace zo Mamana juyowa Safeerah tayi ta kalli Baba ita suke boyema abu, Salma takalli Waleed tace zo Waleed