Sashe 53
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kana sumar da ita!" Wani irin bugawa kirjin Abbati yayi yakalli Salim da kyau zuciyansa na bugawa yakasa magana, daidai ana kara kawomai taba kara na uku sojan yasamai abaki aka kunna zukan taban Salim ya shigayi sannan yakalli Abbati yace "ina Waleed!" Muryansa har baya fita da kyau cus motsi da kumatu ma radadi yake masa yace "yana ciki!" "Dawa!"? Salim yamai wani azabar ihu, gabansa na faduwa yace "da Kuku na!" "The woman?" Bakinsa na rawa tace "tana gidanta" wani kallo yamai yace "inane gidanta"? Ahankali yace "Oakville estate house 21" kai tsaye Salim yace "pick her up Boys" yakalli Abbati yace "waya baka address na gidan Matata?" Yanda kirjinsa ke bugawa yama kasa karya muryansa baya fita yace "Hajiya Kubra tabani Yayar Babanta" mikewa Salim yayi yace "we have extra candidate boys! GRA house number 10, take them to base" atare sojojin sukace Yes Sir! V ni lumshe idanu yayi yace "kazo har gida ka raja yaro da mahaifiyarsa for you to just bring him here left him with Kulu kayi tafiya ka club tun jiya sai yanzu kake dawowa" ahankali Abbati yace "a mini afuwa yallabai" dariya Salim yafara dayasa Abbati yaji kaman yanajin fitsari, yace "I've not even started with you yet! Common Boy kabani 24hiyrs dakai kafin kafara neman afuwa" rawa jikin Abbati yafara cus all he sees a idanun Salim is tsantsan mugunta, kashemai idanu Salim yayi yace "we need to catch up and walk down memory lane koba hakaba"girgiza kai Abbati yayi hawaye na fita daga idanunsa, Salim yace "idan hawayen nan suka zubo sai ka ciro eye balls dinka kabani!" Abbati yarike kukan, dan ijiyan zuciya Salim yasauke yadaga hannu yace "give me the damn papers Barrister!" Dasauri Barrister yataho da papers a hannunsa karba Salim yayi yabude yana dubawa page by page yace "Matar daka saka and abandon bayan kamata ciki kace bakason ciki, spent most of her time a hospital, aka haifi yaro aka kiraka you refuse to acknowledge yaronka kace bakaso, ko suna su suka sama yaron, you didn't contribute anything for danka, rana daya kace zaka rabasa da mahaifiyarsa which did everything for him and dedicate her life for him kayi kadan! You're nobody arayuwan su!" Jefar da papers din yayi akasa yace "we filled for child custody! Let's meet in court! For now Waleed needs his mother! Waleed's mother needs her son, tashi ka daukoshi!"Salim yafada cikeda authority kokarin mikewa Abbati yayi but yama kasa kafafunsa sunyi sanyi ganin yakasa tashi yasa yatabe baki ya mike tsaye karan tabar ya yar akasa ya share hannunsa jikin wandonsa yadan kakkabe jikinsa sannan yawuce abinsa flat din, yace "take the useless boy to base Boys" sukace yes Sir akai sama da Abbati daya fara hu ina za'a kaisa? Inane base? Yace "I need my lawyer" wani bushewa da dariya sojojin sukayi sukai waje dashi. Hannu yasa yabude kofa yashiga Kuku yagani yana fitowa daga ciki, hade fuska Salim yayi yace "where's the boy"? Atsorace kaman mara gaskiya ganin wani huge mutum da kayan sojoji ya nuna sama yace "upstairs second room" sama Salim yayi direct second room din yayi yasa hannu yabude kofa zaune yaga Waleed akasa yana sanye da tun shaddar jiya datai datti, ga majina da hawaye sun bushe a fuskansa, yana zaune akasan dakin hancinsa yayi jaa, idanunsa sun kumbura sabida kuka, ga abinci plates daban daban babu wanda yataba, chips, egg, rice, biscuits, juice, water duk yakici, fuskansa yayi red idanunsa sunyi red sun kumbura sai ijiyan zuciya yake saukewa yana haki sosai na kuka he looks pathetic, dudda yaji an bude kofa but bai kalli kofan ba, bala'in tausayin yaron Salim yaji ahankali yace "Waleed!" Dawani irin sauri Waleed yajuyo jin muryan Abee dinshi, ganin Abee baisan sanda yashiga kokarin tashi daga zaune ba yafashe da kuka mai hawaye agalabaice yace "Abeeeeeeeeeeeee" hannu Salim yabude masa yana murmushi farincikin ganinsa yace "come Son! Abee is here" dawani irin sauri baida ma karfi sabida yunwa pampers nasa namasa nauyi bama ya iya tafiyan da kyau da sauri yaje ya rungume Salim yana sake sabon kuka sosai harda tari sabon majina na fitowa duk ya gogamai ariga ko damuwa Salim baiyiba cikeda so yadagasa yana shafa bayansa yace "it's okay! It's okay! I promise nobody will ever carry you away from us again kaji, stop crying now, stop crying" sake kankamesa yayi sosai cikin kuka da muryansa looking very weak and sad yace "Abeeee Um.....Um....Umyyyyyy" shafa bayansa sosai Salim yayi cike da kaunar yaron yace "Ummy is at home waiting for Waleed, let's go to Waleed Ummy, muje." EPISODE 49 Juyawa yayi yafito daga dakin yasauka kasa kofa yabude yafito compound an fita da Abbati waje yayi waje yafito Abbati da ansa a mota yajuyo yakalli yanda Waleed ya kankame Salim gamgam yayi lamo ajikinsa sai ijiyan zuciya yake saukewa wani abu yaji ya tokaremai wuya da karfi, daya rike Waleed the boy was crying profusely amman jibi yanda ya rungume wanda ba mahaifinsa ba, wucesa Salim yayi cus he's carrying Waleed baiso yayi any improper abu gaban yaron yawuce zaiyi mota Abbati daya kasa daurewa yace "I will hire the best lawyers in town dan bazan taba barmaka d'ana ba! Nine mahaifin Waleed nothing can change the fact that I am his father! Nine mahaifesa!" Chak Salim ya tsaya saiya juyo ya kallesa tare da murmushi only sabida Waleed na wajen yace "Lemme share some words of wisdom with you, Haihuwa doesn't makes mutum a father! Sometimes wanda bashi ya haifi d'a ba can even father a child much morethan the child biological parents! You are nothing but a sperm donor! Kaje ka tambayi mahaifinka what it means to be a father! And how to be a father! See you in Base!" Yana maganan ya shiga motar da soja yabudemai ya yakalli barrister yace "my boys will drop you off, I need to drop my son at home we will talk" yamaida glass na mota sama driver yajasu, aka wuce da Abbati ma. Pampers din yaron is so wet baijin an chanzamai ba dan ruwa sai jikasa yake, yanda Waleed ya kankamesa zaka dauka za'azo asake kwaces ne, ahankali ya manna mai kiss a saman kai hakan yasa Waleed yadago kansa ya kallesa da sauri dan kunya Salim yaji baimasan ya akayi ba yama yaron kiss, cikin muryansa da ba karfi Waleed yace "Abee anan" yakai hannunsa yana nunamai goshinsa irin anan ake kiss ba'a kai ba, murmushi sosai Salim yayi yace "okay Waleed" kiss ya mannamai a goshi yace "I am glad my son is back ummm" washemai baki Waleed yayi yace "Abee ni ma, me too nan" yataba goshin Salim, dan dariya kadan Salim yayi yace "okay" yaduko da kansa, mannamai kiss mai karfi Waleed yayi yace "muuuahhhh Abeeee" dariya Salim yayi kaman bashi ba wlh he loves Waleed yaron is so adorable, har suka shigo estate nasu. Safeerah na zaune akan kujera a falon wuraren 12 idanun nan jajir sunyi suntum taji alamun parking mota dasauri tamike tsaye gabanta na faduwa sosai tai wajen window soja tagani yabude mota yafito yazo baya yabude kofan,Salim taga yafito dauke da Waleed kaman mahaukaciya da gudu tasaki labulen tayi wajen kofa tashiga kokarin bude kofan but bai budun mata ba jin alamun yana budewa daga waje yasa tadan koma baya tanajan gyalen abayanta tana dawo dashi gaba dan rufe gashinta, bude kofan yayi ahankali dasauri ta kallesu Waleed yace "Ummyyyyy!" Dasauri tayi wajen kasa matsawa dab dasu tayi Salim yamata mugun kwarjini, sauke kanta kasa tayi hawaye na cika idanunta, lura da hakan yayi hakan yasa yasauke Waleed akasa yace "Ummyyyyy has been crying tun jiya go and hug her!" Juyowa tayi takalli Waleed saita duka tabudemai hannu da gudu Waleed yazo yawani rungumeta duk yanda taso ya daure takasa tafashe da kuka sosai ta kankame Waleed kaman tayi shekara babu shi tace "I thought bazan kara ganinka ba Waleed uhnnn, I am happy you are back, Alhamdulillah, nayi kewanka Walyly" Waleed na rungume da ita kaman kaman wani babba yace "Ummyyy ci dena kuka, ba kyau" kara kankameshi tayi saita dago ta manna mai kiss a goshi shima manna mata kiss din yayi agoshi tasake rungumesa kaman zata cinyesa ta runtse idanu tana kuka, Salim tsayawa yayi yana kallonsu feeling wani fulfillment a zuciyan sa just looking at the two of them, a mother and Son, the love a mother has for her son is unquantifiable, dago da kanta Safeerah tayi tadan kallesa hada ido dasukayi hakan yasa yadauke kansa dasauri yajuya zai fita dasauri Waleed yasaki Safeerah yace "Abeee" tsayawa Salim yayi yace "yes Son" dasauri Safeerah ta kallesa jin sunan dayakira Waleed dashi, wajensa Waleed yayi kaman zai fashe da kuka yace "ina daka?" Kumatunsa Salim ya shafa yace "zan sallami sojan dake waje ne, je wajen Ummi amaka wanka kaci abinci, l'm coming" batare daya kalli Safeerah ba yace "his room is next to yours" yama Waleed murmushi yace "go to Ummy" baiyi musu ba yawuce wajen Mamansa Safeerah ta daukesa shikuma Salim yabude kofa yafita, sama suka wuce dakin next to nata ko tabude wow shima Waleed rudewa yayi ganin dakin yawuce wajen toys nasa, did he do this room for Waleed ko daman yanada d'ane shima? Wardrobe tabude sababbin kayan Waleed ga shoe rag takalma daban daban nasa, ga pampers wow da kyar ta natsu takama Waleed suka shiga bayi brush tamai ga shower cream da komi tamai wanka tafito dashi a towel shiryasa tayi tsaf tasamai simple kaya short wando dawata simple t-shirt blue yayi kyau he looks like rich boys dinnan, suka fito kitchen ta kaisa, hadamai abinci tayi suka fito zaunar dashi tayi a dinning ta ijiye mai ya iyacin abinci da kansa idan yaga dama, batamai godiya ba, taga rigansa kuma duk yabaci atleast ta karba ta wankemai tunda zata wanke kayan Waleed shima, baici abinci ba kuma shima yafita, atleast tace yazo yaci tunda taji motsinsa a sama, Waleed ta kalla tace "cigaba da ci karka bata wani abu ina xuwa" gyadamata kai Waleed yana cin abinci ba wasa yasha yunwa, wucewa tayi stairs tai sama zuwa agaban dakinsa, knocking tayi ahankali kanta akasa kusan 5secinds tabata sannan taji ance "shigo" hannunta rawa