← Book details Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 93

Sashe 22

Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yasa ta tashi tawuce bayi shima abude tabar kofan tayi komi tafito daure da alwala batasan inane gabas ba bangare daya kawai ta kalla ta kabbarta salla ta idar tafara azkar kanta na sarawa, hakan yasa ta kwanta kan dadduman ance ba a cheating nature bacci barawo ne yayi nasaran kwasheta. Kadan kadan take bude idanunta dake cike da mugun bacci jin kara, bin saman dakin tayi da kallo kafin firgigit ta tashi zaune kanta na amsawa tuna inda take ya akayi tai bacci haka agidan mutane ta kalli gadon dasauri tuna danta, Waleed tagani yayi daidai agado abunsa yana bacci, jin ringing waya yasa tamike ahankali idanunta basama buduwa da kyau tafito da shiga sauka kasa da sauri ta taho falon inda ya ijiye wayan tasa hannu tadauki wayan da yana inda yabarta taga Major Salim a jiki hakan yasa takai wayan kunnenta cikin muryan bacci dakenan yar karama kaman tana whispering tace Helloooo shiru taji anyi kaman babu kowa adayan side din da sauri takai hannunta ta goge idanunta da bayan hannu tazare wayan daga kunnneta takalli screen din again ganin the call is still on yasa tamaida kunnenta ahankali tace Assalamu Alaykum cikin wani husky natsassiyan murya yace m outside open the door hakanan taji kirjinta na racing dagajin muryansa juyawa tayi tabi dakin da kallo, ganin basu bata komiba yasa ta ijiye mai wayansa back tai wajen kofan, sakatan tacire ta murza key tabude kofan ahankali hada ido sukayi yana tsaye gaban door sanye dawata yadi that looks soft and textures milk mai kyau dan yau Friday yana wani irin kamshi, he looks squeaky clean kaman ka lashesa, faduwa gabanta ya shigayi sosai, adan rude tasaki kofan takoma baya tadan tsuganna ahankali tace ina kwana kallo daya yama fuskanta yadauke kai ya shigo this time around ya maida kofan yarufe dawani irin sauri abirkice ta mike kaman zai cinyeta tana kallon kofan daya rufe, kaman baiga yanda ta tsorace ba wuceta yayi ya shiga falon ya ijiye ledan wani super market akan kujera da basket na kuloli that looks like abinci, sannan yajuyo yakalleta batare dayama zauna ba tana tsaye chan wajen dinning sabida tsoro tana wasa da yatsun ta kanta akasa kaman yace woop ta arce aguje, hannuwansa yazuba a aljihu rigansa ya sassauta murya yace are you feeling better today? Duk duniya ita kadai ne idan zaima magana saiya gyara muryansa, ya tankwara yakuma tausasa cus yaga tsoronsa takeji, gyadamai kai Safeerah tayi ahankali, yana kallonta still yace Waleed fa ? Dan dagokai tayi ta kallesa suka hada ido dasauri ta maida kanta kasa, she felt wani iri dataji harya rike sunan danta sannan ya tambayesa kuka kawai taji yataso mata amman tadaure asanyaye tace yana bacci shiru falon yayi bai kara magana ba itama bata sake dago kanta ba banda wasa da yatsunta datakeyi, gently tadan dago kanta ta kallesa hada ido sukayi yana mata wani kallo da takasa sanin na menene da idanunshi dake tsorata mutum, cikin wani irin yanayi na girmama mutum dakuma jin nauyi ahankali tace uhmm nagode! Thank you for everything! Dama uhmmm idan Waleed yatashi zamu tafi ? Idanunsa na kanta bayako kyaftasu har yanzu yace ina zakuje? Dago idanunta tayi ta kalleshi suka hada ido zata sauke idanunta strictly yace t try it! Kasa maida idanun kasa tayi ta tsaresa da kallo kirjinta nawani irin bugawa none stop his eyes are wild Ya Allah! Sai kawai lips nata yahau rawa takasa daina kallonsa takuma kasa magana this is the first eye contact dasuke having tunda ta sanshi dayakai na kusan 30seconds, he noticed saiya kara tausasa murya yace I said ina zaku Safeerah! ? Wani irin blinking idanunta suka shiga yi he s too much for her eyes kaman yamata asiri kasa karya tayi tace ..ma ban sani ba! idanunta suka cicciko da hawaye sai kawai ya dauke kansa, kaman yasaki kuruwanta wani ijiyan zuciya ta sauke itama ta sauke kanta kasa, ahankali yace okay yanuna mata table din yace have breakfast, take drugs that are here sai ku shirya, call me when you re ready to go gyadamai kai tayi ahankali tace thank you wucewa yayi wajen kofa yasa hannu yabude yafice saikuma yajuyo hada ido sukayi dasauri ta sauke kanta kasa, ahankali yace zanje wajen Baba and talk to him you need to go back to your parents da sauri ta sake kallonsa sai kawai tafashe da kuka sosai tana goge fuskanta da bayan hannu batare datai magana ba, ya tsaya jimmm yana kallonta kafin yasa hannu yazare key tabaya yajawo kofan yasa key cus ya lura gidansu ne batason komawa something is definitely going on, yanda yace zaije yaga Babanta karyazo kafin yadawo tagudu tabar nan what if tafada in the wrong hands ga yaro karami tareda ita, dasauri tai wajen window tana kuka taga yaja mota yabar wajen. Rolex din hannunsa ya kalla is 11AM, he needs to help his helper whatever it takes, yarinyar that helped him a death row he will go to the end of the world just to see that smile in her face not cry or sorrows. Cikin 20min yakai kofar gidansu yakashe motan wuraren 11:30, babu kowa a kofar gidan yayi jim sai yafito a natse yazo wajen yakai hannunsa ahankali yayi knocking ya dakata shiru, sake knocking yayi na biyu ya tsaya shima shiru, yakai hannunsa yasake knocking akaro na uku, karan bude kofa yaji hakan yasa yadan koma baya kadan sai yaga an dan daga wani marfin lekowa yaga idanu hakan yasa yace Assalamu Alaykum ganin ba yan gidansu bane yasa anatse Mama da duk tayi wani iri tabude kofa tafito kallo daya Salim yamata yagane itane mahaifiyar Safeerah, Safeerah really looks like her but tanada haske Baba though Baba yafita haske, Mama kuma baka ce, saisa Safeerah is not black she s caramel, anatse yadan duka cikeda kunya dakuma girmamawa yace ina kwana calmly Mama tace lafiya lau wa kake nema? Dagowa yayi yakalli Mama dake kallonsa ganin bata sansa ba calmly yace Abba nake nema, Baban Safeerah! Dasauri Mama takara kallonsa tana tunani dan unguwan nan ne? Tasan Baba na gaisawa da yan layin ko zaman dayake awaje saisa ma yake dan samin kudi sukan masa kyauta once in a while, ahankali tace bayajin dadi ne yana kwance, waza a gayamasa ? Dasauri Salim yace meke damunsa Mama ? Kallonsa Mama tayi da kyau jin yanda yakirata Mama, hakan yasa Mama tace wayekai bawan Allah? Dan shiru yayi kafin ahankali yace sunana Salim nine Ogan Safeerah a inda take aiki, jiya tazo company mu da daddare da signs na duka toh daman maganan nazo yima Abba kenan, zan iya dubasa Mama in yaso sai nayi maganan dake sosai Mama ke kallonsa tanajin wani natsuwa dashi especially natsuwansa sannan ba yaro bane irin su Shamsu, babba ne kuma kamili wanda yasan kansa, ganin batai magana ba yasa ahankali yace Abba yasanni mun hadu so daya dan ijiyan zuciya Mama ta sauke, sannin Momma bata nan hakama Shamsu Salma ce kadai agidan kuma tasan tana bacci war haka yasa tace shigo Bismillah tajuya yabi bayanta a natse, ga mamakinsa dakin dake gefen gate na masu gadi yaga sunyi a babban gida haka da base on the little info he daya samu jiya this house na yayar Abba ne cus ance Shamsu yakawota yaron sister kenan, and mahaifin Shamsu is tsohon gwamnan Jigawa he s late, why will her own blood brother be living a side na masu gadi? Bude kofan Mama tayi tashiga ciki saiya tsaya agaban dakin, juyowa Mama tayi tace shigo ahankali ya shiga dan karamin falo ne ga yar katifa awajen dake a gyare tsaf ga ganamasgo da jakan school din Safeerah ke kai, ga gwangwnayen abincin Waleed a wajen sai few kayan wasan yara da ball, babu komi falon, dadduma Mama takawo ta shimfidamai ya zauna ahankali tace bari nafito dashi tawuce ciki taduka gaban Baba da baya gane wanda ke kansa idanunsa ganin ya bace gaba daya, ahankali tace Malam Malam motsi yayi yace am Mamana na dawo? Waleed fa ? Shiru Mama tayi tun jiya kawai Safeerah yake tambaya ahankali tace kayi bako sunansa Salim, yace ka sansa shine Ogan Safeerah, kampaninsu Safeerah taje jiya dasauri ya yunkura zai tashi yakasa kamasa Mama tayi suka fito tazaunar dashi Baba yace ina Safeerah Salim ? Ruwa Mama tasa a plate mai kyau pure water ta ijiye masa ta zauna gefen Baba, anatse Salim yace ina kwana Abba da kyar Abba yace lpy lau ina Mamana Salim ? Shiru Salim yayi he s feeling very sad seeing how sick Baba is yace she is safe Abba, namaso nataho tareda ita nadawo da ita amman taki yarda, meya faru, waya daki Safeerah haka? One thing about Salim is bayida tsoro ko kadan kokuma irin kunyan nan da jin nauyi bai iyaba unless idan bai damu da abuba shi ba yaro bane he is here for something and he will sure do that. Kafin Baba ya bada amsa Mama tace rashin kunya tayi da dambe da dan sauri Baba yace Salim kasan kowani family nada one or two issues haka, yar matsala aka samu jiya, one thing da Safeerah shine dan banzan zuciya ne da ita inhar aka tabani ko mahaifiyarta bata daurewa Baba yayi murmushin manya yace Safeerah ta taso ita kadai bata da siblings so kwata kwata bata understanding cewa Yaya da kani can fight, that is basically abinda yafaru nasan nai magana da ita na lallabata zata dawo Mamana akwai rigima kam Masha Allahu Mama data kasa daurewa tace Malam kasan dai koka lallaba ta tadawo yan gidan ba barinta zasuyi ba ko, itama kuma rasakunyan bakinta ba mutuwa zaiyi ba kasan dai Safeerah cikeda damuwa Baba yace zan bawa Mama Kubra hakuri da yardan Allah zata barta ta ..ta Hannunsa yadaura akirji kawai yayi baya Mama tace Malam Malam dasauri Salim yatashi kama Baba yayi yarike yaji jikinsa zafi rau yace he needs hospital Mama daukan Baba yayi yace muje asibiti chak yadauki Baba, Mama da already tasa hijabi tabiyosa tasaka slippers fitowa sukayi daidai Salma na zuwa wajen tana sanye da Shedanun kayan bacci tawani kalli Salim dake dauke da Baba daga sama zuwa kasa tace wa kuka
Chapter 22 · 0% Book details