Sashe 28
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
you is not capable of loving anyone a riga an cire emotion dinnan a filin yaki! Baki Salim yabude zaiyi magana Dad yacemai get out before I loose my temper dan zan sabamaka sosai wucewa Salim yayi wajen kofa haryasa hannu zai bude kofan ya tsaya yajuyo yakalli Dady calmly yace Dady I know kai mahaifina ne saisa natako zuwa nan na sauke hakki nabaka hakkin ka, I am an adult that can make decision about my life, I don t need you kamin aure zan iyayi dakaina, I am simply here dan na sanar dakai zan auri Safeerah and make her my wife today! Yana maganan yajuya yabude kofan yafice Baffan sa yagani agaban office din ya tsare Salim da idanu murya ciki ciki dan ransa Salim yace ina yini Baffa yawuce abinsa bai jira amsan sa ba yasauka kasa yakai wajen parking yana kokarin bude motansa akace Salim, juyowa yayi Baffan sa yagani hakan yasa ya tsaya Baffa yazo wajen yace Salim mesa zakama mahaifinka wannan furucin? Wani aure kake shirin yi bayan ana shirin bikinka Salim ? Ahankali yace Baffa ni yaro ne? Bashi zai ciyarmin da matar dazan aura ba, he think sabida yahani zan hanu, idan bazaku nemanmin auren ba zan nemi wasu sujemin, i am tired of the way Dady ke treating dina kaman ba shi yahaifeni ba, he was never there for any decision nawa daman, why did i even come here today thinking zai yarda? Baffa stay out of this sai ajjima yabude motansa yashiga yaja abinsa yatafi, juyawa Baffa yayi yakoma office na Dad yashiga har lokacin yana tsaye yana huci yace Yaya kaji maganan banzan da Salim yake gayamin? Is because ka lallabani that year na hakura ban kira an koresa daga camp na soja ba, look at what this boy becomes today eh Baffa baice komiba yawuce fridge na office din yabude yaciro ruwa ya tsayaya a glasscup yazo yamikamai yace karba yayi yakai baki ya kurba ya ijiye cup din Baffa yace zauna to muyi magana Aliyu zama Daddy yayi ahankali yadan sauke ijiyan zuciya, Baffa yace kadaisan yanda nake yabanka in terms of sauraron yara da biya musu bukatunsu ko runtse idanu yayi yace nasani amman abinda Salim yazo dashi ba me yuwa bane Yaya kagane, bikinsa saura kwana goma yazo dawata magana kumama bazawara zai aura haba Baffa yace to menene a bazawaran eh? Dasauri Dady ya kallesa hannu Baffa yadagamai alamun ya isa yace calm down kawai kaduba zancen, auren nan kaika hada dakazo mai da maganan baice a a ba, yanzu yazo maka da tasa saika yarda kaima me aciki he s matured enough to hold both of them, kadena treating Salim kaman wani yaro wani kallo yama Baffa yace yanzu anma yar karaman Nana adalci? Baffa yace shi fa namiji mijin mata hudu ne kowa yasani sabida baka yiba doesn t mean is wrong, bagani da mata biyu ba Dady yace ai kaga har yau bana shiri da amaryar ka Uwargida ce tamu murmushi Baffa yayi yace dan Allah ka saurari yaron nan stop trying to control Salim the more kanayi the more yana kufce maka sosai yakalli Baffa yace a haifi yaron dabazan controlling ba, mubar maganan cus I will never ever support auren nan wlh kuwa EPISODE 2 5 na yamma za a shiga aikinsa around 4 yashigo hospital din yau tukasa ake aka budemai baya yafito yana sanye da kayan sojoji, wucewa cikin hospital din yayi zuwa dakin yayi knocking tareda Sallama Mama tabudemai tace Salim shigo shigowa yayi yakallesu yace ina yinin ku, ya karfin jiki Baba atare sukace da sauki, kujera Baba ya nuna masa yace zauna Salim zama yayi ahankali yana tunanin ina Safeerah da Waleed basa dakin, dan shiru Baba yayi chan yace mesa kake taimakon Safeerah Salim? Mahaifiyarta ta sanar dani komi hartakardun filayen an nunamin, in everything this is the only question nakeda shi, na ganka naga mutum mai amana da fadin gaskiya, aiki za a shiga dani bansan ko zan fito da raina ko akasin haka ba, Salim ka gayamin mesa kake taimakon Safeerah ? Shiru Salim yayi kaman yana tunani sai chan yakai hannunsa na dama yadaura akan hannunsa na haggu ya yacire bitirin hannun rigansa yaja hannun rigansa sama gabaki daya har zuwa muscles dinsa da ananne rigan taki matsawa sama, hannunsa na haggu a kone fatan takoma mai tabo gabaki daya dinnan Mama tace Subhanallahi kataba yin hatsari ne tabon kuna nake gani haka gabaki dayan hannunka? Meya sameka haka? Dago kansa yayi yakalli both Mama da Baba ahankali yace shekaru biyar da suka wuce abin yafaru sai yayi shiru yace lokacin ina mata kin lieutenant a soja nazo kano wani aiki ina gudu a titi wani yaro kawia ya shigomin da gangan bayan na kaisa asibiti yace na kaisa gida ina shigowa layin naga kawai an taru akaina an kaini wajen taya aka kulleni yayi shiru yadan lumshe idanu kaman he s remembering something ahankali yace I dont know meya faru but nasan Allah ne kawai ya kubutar dani daga wutan data faraci takama hannuna rigata ta kone na gudu awannan babban unguwan gidanku na fada! Yayi shiru Baba saiya shiga kokarin mikewa zaune da kyau Mama na rikesa, cikeda mamaki yace kaine mutumin da Safeerah taboye agidanmu lokacin nan? Ahankali Salim yace nine Abba, bayan an tafi dani nayi sati a ICU na shaki hayaki sosai na wahala dan saida nayi wata daya a hospital inajin sauki babu wanda na fara nema aduniya sai ku!Saida na hargitsa anguwan nan da Kano ina nemanku ana kuma nemanmini ku yayi shiruu yace nadade ina neman ku dan na godema Safeerah da iyayenta amman ban ganku ba, kullum Safeerah na raina ranan daya kawai naganta a kampanina! Baba da Mama sukai murmushi Baba yace Allah kenan! Iko saina Lillahi! Ijiyan zuciya yasauke saikuma yadago yakalli Baba da Mama dasukai shiru duk suna kallonsa ahankali yace nasan this is not the right time! Baba ni ba yaro bane shekaruna 39 ina neman arba in in few months time, dan haka Baba inaso kubani auren Safeerah! Atare Baba da Mama suka kallesa, Mama tace Salim nasan kaganta da d a amman dudda haka hakkine mu gayamaka bazawara ce fa Safeerah, ta taba aure, tayi zaman aure na watanni shidda, tanada yaro Waleed dake neman shekaru uku he is 2yrs 7months gyadama mata kai yayi yace nasani Mama! Zan aureta ahaka, ko tanada yara goma zan aureta, zan rike yaran kuma idan za a bani, sannan zan riketa itama amana Safeerah tamin komi ita Allah yaturo ta ceci rayuwana! Mama da Baba sukai shiruuu, sauke ijiyan zuciya Salim yayi yace Banbata gidan nan danta aureni ba! Kafin namata maganan aure nabata gidan bata amsa ba, I only use auren sabida nasamu ta amsa kyautan, Abba badan komi namata kyautan nan ba saidan hallaci sanadina gidanku aka kone is only right na maisheku gidanku dan Allah ku karbi gidan Abba Baba yayi shiru yana sauraronsa Salim yace Abba agidan mu nine babba inada kanni hudu daya na miji uku mata, daya tayi aure, biyu na gida basu yi ba, Abba inason kannina sosai especially matan sabida sunada rauni, all I want is na kula dasu, bazan taba cutar da Safeerah ba, zan kula da ita zan killace ta, kome zanma Safeerah bazan taba iya biyanta abinda tamin ba, shekaru biyar kenan ina nemanta ido rufe yanzu da Allah yahadani da ita bazanso takara kufcemin ba, ina so na auri Safeerah Abba! sun mugun natsu da Salim the way yake maimaita yanaso ya aureta is so deep for him da kana iya gan i a kwayan idanunsa dudda mutum ne shi mai wuyan ganewa, dudda bawai sun sanshi bane but yashiga ransu, banda haka ya nada natsuwa sannan ba yaro bane kaman su Abbati dan babu abinda yara suka iya sai shirme da yawon party, ga uwa uba gidan chan sunce kar Safeerah takara dawowa sannan yayarsa daya sani kaman yanda taki sayo abincin Waleed makarantanta ma ba maganan shi yanzu, to da wannan wahalan ba gwara sun aura mata Salim mai sonta ba, wanda yadade yana nemanta, shima yagaji da halayyan yayarsa zai shiga gidan da aka bawa yarsa tunda sadakinta ne da kyauta ne bazai zama comfortable ba but yanzu natane aure yabata, as long as yarsu is safe burinsu yacika, and yaga Salim can give yarsa that safety da babu wanda zai kara hantarar ta. Anatse Baba yataba hannun Mama kamawa tayi ta matse alamun ta yarda hakan yasa Baba yace mun yarda dakai, ni mahaifin Safeerah nabaka auren ta, ina fita daga asibiti katuro magabatanka mu daura aure banson hayaniyan biki albarka nake nema a wannan auren nata karo na biyu kaji Salim! Karikemin Mamanah amana, bana wasa da yarinyar nan ina matukar son Safeerah ita kadai Allah yabani, tanada taurin kai da kiriniya amman Safeerah tafi kowa kirki aduniya tanada zuciya mai kyau, nabaka aurenta Salim, Allah yamuku Albarka! Ahankali Salim yace Ameen Abba nagode! Shigowa Dr Isa yayi da surgeon yace Baba ka shirya? It s time murmushi Baba yayi yace na shirya Mamana na masallaci tanamin addu a ba tsoro araina muje Doctor, saina fito Salim Gyadamai Kai Salim yayi yace Allah baka lpy Abba EPISODE 2 Saida aka shigar da Baba operation room sannan yabar Mama kadai awajen yafito shi baije wajen masallacin ba but daga inda ya tsaya yana hango masallacin. Hangota yayi tafito daga masallaci she is still with that hijab, day 3 kenan she s still wearing the same thing stubborn girl, eyes nata sun sabe today but har yanzu basu gama washewa ba saida tafito tajuya tai wani dan karamin murmushi tamikama Waleed hannu alamun yazo da sauri yakama hannun yana wasa slippers nata tasaka tajuyo tafara tafiya out of nowhere wani mutum haka yatare gabanta yaga yana mata magana hakanan Salim yaji abu just hit his heart, kuma sai yaji zafi sosai kaman ciwo does he have heart problem ne? Ya tambayi kansa saiya juya zai koma ciki ina yaji in all levels yakasa kawai saiya juyo yasake kallonta bawai murmushi take ko magana ba but ta tsare mutumin dake mata magana da manyan idanunta ko kyaftawa batayi amman shi bata iya kallonsa