Sashe 69
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yace how is the menstrual cramp? Wlh she felt kaman ta shige kasa he s so raw, kin magana tayi tace uhmm sarai yajita but sai yayi kaman baijiba, ahankali yace how many days kikeyi ? Kifa kanta tayi a guiwowinta wayan na kunnenta wlh kunya yabata sosai taki magana hakan yasa sounding a little bit harsh yace saikin ganni zaki fara magana da sauri gabanta na faduwa tace dan shiru yayi sai chan yace a 4th day kike wanka ki fara salla ko sai the 5th day, or you mean on the 3rd day yake tsayawa 4th day kiyi wanka ?Safeerah aranta tace wai wannan wani irin mutum ne? Shi baya kunya dan Allah? Why is he asking her all this questions? Jibi wani tambaya shi an gayamai haka period keyi ita bama tagane tambayan ba. Murya chan kasa tace ni ban ganeba shiru yayi sai chan yace test result naki will be ready tommorow, are you comfortable in that side? Gyadamai kai tayi tace shiru yadanyi chan yace if anybody misbehave with you cikin kannina ko anybody let me know kin magana tayi aranta tace sabida na gayama kaci zalinsu, ahankali yace kinason wani abu na siyomiki tunda kin kasacin abinci ? Batasan mesa ba but tambayan daya mata she felt special yadan mata dadi ahankali tace ice cream dina na dazu nakeso dan shiru yayi baitaba tunanin zatai magana ba ohh daman ance akwai period cravings daman, calmly yace okay banda shi sai mene ? Kai tsaye tace abu me zaki nakeso banjin yunwa dan rage murya yayi yace sainasa an ciccire miki hakora murmushi tayi da batasan tayaya ma yafito ba, Salim yayi shiru yana sauraron yanda take murmushi zuciyansa na bugawa he wish yana gabanta take murmushi haka, ahankali yace bakisan haka akema masu cin zaki ba sake murmushi tayi saikuma tai shiru jin yayi shiru kaman sauraronta yake Calmly yace if anything comes up let me know, and bance kibi yaran gidan yawo kuje ko ina ba, anywhere akace kije call me ki sanar dani, don t come to the compound without hijab we have many workers stay inside if u must come out use hijab itadai ta shiga uku ahankali tace sarai yajita yayi kaman baijiba yace I will get your sweets na aiko miki dashi yana maganan ya katse wayan baima jira tamai godiya ba, shigowa Layla tayi takawo mata ice cream karba Safeerah tayi tafara sha abin yamata dadi chan saiga Lubna tashigo da leda mai kyau tace Anty Safeerah yaya yace nakawo miki akunyace Safeerah tace nagode dariya abin yaba Lubna da Layla sai sukahau dariya kafin suyi zamansu suna hira da ita sai wajajen 11 Ammi tashigo tace wai bazaku barta tai bacci ba yarinyar da batada lpy, oya Lubna to your room, Layla wuce ki hada kayanku gobe zaku wuce duk mikewa sukayi, Ammi takalli Safeerah da kanta ke kasa yace good night Daughter na akunyace Safeerah tace saida safe Ammi nagode Allah saka da alkhairi murmushi Ammi tayi tawuce tafita. EPISODE 6 Da asuba Safeerah ta tashi Ammi da kanta tashigo dakin dasauri taduka tace ina kwana Ammi anatse Ammi tace tashi tashi ga brush I know babu sabo a bayin dukawa tayi tasa hannu ta karba tace Allah amfana Ammi sannan tajuya tabude bayi ta shiga Ammi tabita da kallo kafin ta tsare yar karaman jakan da Salim ya aiko mata dashi da baifi yaci kaya kala hudu ba kawai tai murmushi tajuya tafice wanka Safeerah tayi tafito daure da towel ta shirya tsaf duk sai kunya takeji ganin yanda yadebo mata pants da bra tasaka wata atampa riga da skirt ne embellish mai royal blue da yellow patterns dinkin yamata wani irin mugun kyau ajiki, parking gashinta tayi da ribbon wlh tanaso tai kyau gashin ya isheta, hijabi tasaka ta gyara dakin tass sannan tabude kofa tafito babu kowa a falon saman she wants to cook dudda batasan ko tana musu shishigi ba, but tadaure nan falon saman ta gyara tai arranging pillows a chairs saita sauka kasa ta gyara kujerun tass ta tambayi Ammi ne kotaje tayi da ace zata kira Mama ta tambayeta yanzu da meme Mama zatace? Mama zatace tayi sabida a al ada matan yaro kema surukai girki, kitchen nasu dake kasa tabude ta shiga kitchen din wow babu kowa ciki komi a gyare store tabude ta shiga babu abincin da babu fridge akwai nama kan rago da tail da kafafu batasan me sukafi so ba but she will make English breakfast that is healthy and gargajiya breakfast, kan ragon taciro taga pressure pot hakan yasa tasaka komi a wuta sannan ta surfa gero a blender tasa kayan kamshi tahada tai tea na kayan kamshi tasa a flask, tafara soya fries tai ksai da sinasir tafara soyawa around to 7 Ammi ta sauko sabida kamshi daya addabeta she s use to girke girken chef dinsu kitchen din tazo Safeerah bamata lurada itaba tayi nisa a aiki Ammi ta tsaya tana kallonta she s using all burners din tana aiki da kuzari this is something dabata taba ganin Nanah tayi ba wlh kawai saitaji tana son Safeerah hardly take aiki amman saita karaso tace wani aiki zan taya diyata tawuce tana wanke hannu a tap dasauri Safeerah tajuyo ya duka tace Ammi ina kwana murmushi sosai Ammi tayi tace stand up, ai we have chefs by 7 suke zuwa fara hada mana breakfast kamshi daban danaji yasa saida na sauko, stand up tashi tayi Ammi ta zo kusada ita tace ya karfin jikin ahankali tace naji sauki calmly Ammi tace ciwon cikin fa wani irin kunya Safeerah taji dasauri tajuya tanadan rufe fuskanta Ammi tace Sarkin kunya, cire hijabin as long as kina cikin gida kidena yawo dashi gidan Maman ki ne nan, banda haka girki da hijab a kitchen is risky gyadama Ammi kai tayi tazare hijabin ahankali tawuce wajen kofa ta ijiye Ammi tadan bita da kallo how come small innocent girl like this tazama bazawara she s so beautiful dawowa tayi Ammi tace to me zanyi akunyace tace Ammi bakomi dan Allah kihuta chips Ammi ta tayata kwasheta taxuba sauran major girkin ita keyi Ammi Wlh kamshi yabaza gidan normally basa breakfast dawuri but kamshi yasa Dady shima yasauko kasa sanye da jallabiya yana kwalama Ammi kira yace Hajjaju what are the chefs cooking this morning fitowa Ameerah tayi daga daki tace Daddy good morning wlh nima kamshin ya isheni fitowa Layla tayi da Binafa tace nima haka the scent d aroma is new like is not the usual one damuka sabaji agida daidai Lubna nafitowa Dady yace Autana enter Ammi room ki kiramin ita Ammi datajisu akasa tace gani akasa ku sauko saukowa duk sukayi Ammi na tsaye wajen dinning tana murmushi tace duk kuzo ku zauna yau is early morning breakfast day zuwa duk sukayi duk atare suna tambaya me ake dafawa Ammi tace nima I don t know matar Yayanku kemana kari, Safeerah dan yatsine fuska Ameerah tayi Dady kuma yayi shiru yana kallon gaban kitchen din haka sauran ma Safeerah tafito dauke da kulan pepper soup she looks so pretty a atampan ta daura dankwalin dayadan zame baya takawo har dinning zata ijiye Daddy yatashi yakarba yace lemme help you ya ijiye dukawa tayi tace ina kwana Dady dan kallonta yayi saikuma yayi murmushi yace stand up me kike girkawa haka duk ya ishemu da kamshi akunyace ganin Dady is a very free person tace breakfast yanzu zan fito dasu dasauri yakalli su Ameerah yace maza kutashi kuje ku tayata ku kun zauna saidai Chef subaku tas hi sukayi harda Layla duk aka fito da abinci to be honest Dady bai wani trusting abincin ba irin yarinyar ce but baiso tai feeling discouraged yasa yazauna duk suka zauna banda Safeerah data kasa komi Ammi tace serve us bude komi Safeerah ta shiga yi kowa yayi turus yana kallon abincin ya kalleta Dady yadan gyara murya yace samin sinasir din da pepper soup, asamin shayi akuma samin kunu infact samin komi duk zan dandana and grade my new daughter Inlaw akunyace tashiga sama Dady a plates masu kyau ta ijiye agabansa yace madallah, E for effort you are so brave small girl dake haka kin dafa all of this Ammi takalla ahankali tace Ammi mezan zubamiki Ammi tace nima asamin komi kadan kadan amma sama Ammi komi tayi takalli Ya Layla tace Ya Layla kefa tace Nima komi kadan samata tayi takalli Ameerah kafin tamata magana Ameerah tace I will serve myself please dan gyadamata kai Safeerah tayi takalli Lubna tace mezan miki Lubby dasauri tace chips and pepper soup da kunu Anty Safeerah samata tayi Ammi tace sa naki wanchan idan taga dama tasaka nata tai maganan tana hararan Ameerah data sauke kanta kasa zama Safeerah tayi kusa da Lubna atare suka faracin abincin tun Dady na ci kadan kadan saiya faraci kaman zai hadiye plate abincin ya bala in masa dadi kowama na table din haka duk kallon Safeerah suke jama a girkinta akwai taste da dandano na daban they eat pepper soup kullum but nata feels and taste different a taste bude nasu tasss Dady yayi clearing platesnasa Ammi ma haka chips kawai ya rage Dady yakalli Safeerah da kanta ke kasa yace wani cooking school kikaje nasaka yammatan nan biyu na gabana especially auta cus ba abinda ta iya gaskiya kin iya girki wai Wai Wai I enjoyed this meal ahhh, Auta je dakina daukomin kudi nabada tukuici Sama Auta tace takawo ma Dady kudi bandit daya ya ijiye na dollar gaban Safeerah yamata murmushi yace thank you for the breakfast akunyace tace Allah amfana Dady Dady yakalli Layla yace zomuyi sallama Layla inada meeting yanzu zan fita saida ya sallamesu yafice Ammi tasa Ameerah da Lubna sukai clearing table while Layla tafito around 10 zasu tafi gida itama Anna Abuja take Safeerah taji kaman karta tafi cus tanada kirki Layla tace zansa Yaya yakawoki gidana take care of yourself okay gyadamata kai Safeerah tayi ta tafi sama takoma dan she s not comfortable da Ameerah bayi tashiga tai abinda zatayi tafito tadauki wayanta Mama takira sukai magana tai magana da Waleed dabai damuba kwata kwata hakan yasa zuciyanta ya natsu sosai.