Sashe 20
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zanje company danake IT akwai masallaci zan shiga na kwana awajen, Mama don t worry babu abinda zai sameni just take care of Baba, Allah zai bani yanda zanyi, I will arrange something mukoma Kano Mama tai shiru tana kallonta kaman ta rungumeta taita kuka, saita warware zaninta tamika mata 2k tace kije Allah ya tsareminke babu abinda zai sameki, Allah ya kareku keda Waleed, kafin gobe Babanki ya farfado zamu lallaba Momma kidawo girgizama Mama kai tayi tace Wlh bazan dawo ba Mama nagaya muku, kuma kuma saikunbar gidan nan hannuwanta Mama takama saita shiga dukan hannuwan bada wani zafi ba tace taurin kanki da zuciyanki yayi yawa fa Safeerah kina mace, mehaka iyye kalli matsalan dakika sake sakamu ciki again Malama ana nemanki ciki gardawan suka tsaya kan Mama, daya cikinsu ya kalli Safeerah yace bar unguwan nan goge fuska Mama tayi tajuya takoma ciki Safeerah tajuya dasauri tashiga tafiya kirjinta bugawa yake sosai, tanayi tana share hawaye today is one of the saddest day of her life, take cewa company su inda just jiyan nan tafara aiki how sure is she ma za a barta ta shiga ciki? Jijjiga Waleed dake kuka abayanta tadinga yi harta fita tahau keke zuwa junction ta tare mota tashiga sannan Waleed yayi shiru kaman yayi bacci . Around 8:30 tasauka bakin junction tashiga takawa da kafa tana addu a Allah sa abarta ta shiga, Allah daurata kan koma waye ke gadin, hartakai company wani dattijon security ne ke gadi ya tsareta agaban gate yana ganinta ya ganeta yace Hajiya me kike nema? Me kikazo nema ? Ahankali tana saita muryanta daya koma kaman ta kamu da mura sabida kuka tace na manta da key na a office namu dan Allah inaso na shiga na dauko kallonta yayi ga goyo dayagani abayanta yace can I see baby dake bayanki ? Gyadamai kai tayi ta juya ta daga hijabinta sama tace ana ne Waleed ya kalla dake bacci yana kara haskasa da touchlight yace okay zaki iya shiga yabude mata gate tawuce ciki yabita da kallo yana tunani, rayuwa sai ahankali mutane are fighting one battle or the other, ba yaune farko da zakaga wani ma aikaci yadawo company ya kwana ba, people are facing problem, from face nata yaga alamun mari ga kumburin baki harda dan jini idanu sunyi jajir hawaye ma basu gama bushewa ba, maybe mijinta yamata duka tazo nan ta kwana kafin gobe ta nemi option, if he can help her by letting her sleep why not, she s just lucky shine on post da abokin aikinsa ne da bazata shiga ba. Wucewa reception tayi tabude kofa ahankali akwai wuta awajen tawuce kofar mosque tabude ahankali ta shiga ta taba bango ta kukkunna wuta tashiga masallacin tawuce bangaren mata shima ta kunna wuta tashiga daga hijabinta ta kwanto Waleed dake bacci sosai ta rungumeshi a jikinta ta zare zanin ta shinfida awajen sannan ta kwantar dashi ahankali tana sauke ijiyan zuciya tana kallonsa hawaye na cika idanunta yanzu zuciyanta ke kara breaking sabida Waleed, wat is she gonna do yanzu? Ta ina zata fara? Yaya zatayi da Waleed? Sai kawai ta rushe da kuka tana yaushe bakinta cus Waleed na ji zai farka. Wuraren 8 yayi parking motarsa a compound dinsu yayi shiruu batare daya kashe motan ba ya lumshe idanu kawai, yakai sama da 20mins ahaka sai kawai yabude idanunsa yadan gyara zamansa yasa hannu yadauki wata iPad dake dayan seat na gaban motan kawai yayi logging in portal na company su yashiga CCTV to be honest baimasan mesa yayi ba wlh, yayi accessing all feeds na cameras din department by department yake dubawa, alamun mutum yagani a reception da sauri yayi clicking on camera mutum yagani da dogon hijabi tana tafiya ahankali tawuce masallaci babu camera a masallaci so baiga wayeba, bangaren details na ma aikatansa ya shiga yadauki number security gate yakira yakai wayan kunnensa ringing daya aka daga akace kai tsaye yace wacece tazo company mu this night? Kunmasan da mutum aciki? Dasauri mutumin yace Sir banine a gate ba I will resume post by 10:00PM Sir amman bari naje na tambayesa Abdullahi ne anatse yace okay, no need to hang up dasauri da gudu yafito waje daganan waya Salim yaji yace Kai Abdullahi Oga yakira wai waye yazo office da daddare haka? Dasauri mutumin yace wannan sabuwar zuwan ce yar IT kaman she s having problem ne she looks like wacce akama duka saisa I let her in maybe she s not safe katse wayan yayi yawani yi mahaukacin reverse yabar gidan, tafiyan 20mins normally ke kaisa company daga gidansu but yau 13mins yakaisa budemai gate sukayi duk sunyi mamakin ganinsa karasawa yayi yay parking wajen da ake parking ya sauko yana sanye da manyan kaya yadi milk anyi dinkin jumper yana zuba uban kamshi, anatse yawuce wajen kofa yashiga yayi hanyar mosque yabude kofan slippers dinta yagani abakin kofa, daga wajen yanajin kukan yaro da kuma kukan babba duka atare, gently yabude kofan mosque din batare daya bari yayi kara ba yashiga tafiya ahankali towards kofar side din mata yakai daidai kofan ya tsaya jimm yana sauraron yanda take kuka da yanda yaron ke kuka shima hannu yakai asanyaye yabude kofan karan bude kofa yasa Safeerah tadago kanta afirgice tajuyo takalli kofan while Waleed ya tsala ihu yashige jikinta yana kuka yana kallon mutumin shima da idanun bacci da yunwa cus baici abincin dare ba, bayan hannunta takai ta share fuskanta da sauri jikinta har rawa yake ta yunkura tamike tasa hannu tadauki zanin goyon dasauri tana rike Waleed dake kuka ajikinta ta taho wajen kofan inda yake tsaye kanta akasa muryanta dukya hargitse tace dan Allah kuyakuri na zo nan bada izini who beat you!? Ya tambayeta tone nasa na nuna bacinrai sosai, tana jijjiga Waleed dayaki dena kuka yana kallon Salim dake kallonsu kaman ya sansa daga wani waje, yace who slapped you and smacked your lips? Who did you fight with ? Yasake tambaya adan zafafe da saida gabanta yafadi sosai, murya chan kasa tace bakowa! Waleed ya kalla dake kuka sosai yana kallonsa kaman yasansa ga idanun bacci, ahankali Salim yamika hannunsa biyu dawani irin sauri taji Waleed yatafi wajensa daga hannunta hakan yasa tadago kanta da sauri cikin muryanta dake nuna kuka tace kai Waleed daidai Salim yana karasa kai hannunsa jikin Waleed hakan yasa tasaki Waleed din, gently Salim yadaukesa Waleed yawani shige jikinsa ya kwantar da kansa akirjinsa yana rage sautin kukan Salim yashafa bayansa ahankali yadan jijijgasa yace stop crying uhmm! It s okay! Lamo Waleed yayi batare daya sake kuka ba ko ihu, kallo daya yama yaron yagane danta ne yana yanayi da ita, kallonta yayi yanda take wasa da yatsunta kanta akasa yace is it his father that beat you? Girgixamai kai tayi da sauri tace a mun rabu shiruuu yayi yana kallonta dagokai Waleed yayi yakalli Salim idanunsa na cikowa da hawaye sai yafara jiniyan kuka again dasauri Safeerah ta dago kanta takallesu tadan matso dab da shi tamika masa hannu tace kawosa na goyasa mutafi, rigima zaita maka kaman badashi tai magana ba cikeda kulawa ya kalli Waleed kaman wanda ya fahimci yaron yace are you hungry? Kanajin yunwa? Gyadamai kai Waleed yayi dasauri yace aaaaa juyawa dashi Salim yayi yafara tafiya dasauri Safeerah tabisu gabanta na faduwa yayi waje, motansa yabude yashiga dasauri Safeerah tazo ta inda suke ta glass din Window tai knocking sauke glass din kasa Salim yayi strictly yace zaki shiga ko mutafi mu barki ? Hawaye yaga sun cika idanunta gabanta na faduwa but still tace ni kabani yaro na mutafi! EPISODE 1 Kaman badashi tai magana ba kunna motan taga yayi abinsa ya danna wajen glass na window yadhiga rufewa ganin yana kokarin reverse ga danta acikin mota da sauri ta zagayo ta gaban motan tabude ta shiga ta zauna tana kallon yanda ya zaunar da Waleed ajikinsa ya rungumesa yaja motan da hannu daya, is the way Waleed yayi lamo ajikinsa ke bata mamaki kaman ba Waleed ba, da gudu yake tuki gaban wani super market na yara yayi parking ya kashe motan batare daya kalleta ba yace wani abinci yakeci? Kin magana Safeerah tayi ita ya bata danta yaki ganin taki magana sai kawai yabude motan yafice rike da Waleed ya shiga ciki, yana shiga wani juice yafara budewa na yara yasa masa abaki tass Waleed ya shanye yana wani irin kallonsa irin kallon for the first time wani wanda ba Baba da Mama da Ummy ba yabasa abun dadi sai kawai yama Salim wani heart melting smile tsaresa da idanu Salim yayi shida baya murmushi sosai samin kansa yayi da sakinma Waleed full smile Waleed ya washe baki yana nunama Salim cheese balls, daukan masa cheese balls yayi yabude yabasa ya karba yafara ci sannan Salim yakalli matan dake wajen yace I want kids food for him hadomai abinci akayi daban daban, yasayamai sweet da cheese balls pack, juice da biscuit yabada card yabiya, ma aikatan wajen na fitowa da kayan yazo yabude motan aka samai komi a back sit sannan ya shigo yazauna, Safeerah takalli su adan hankali tahada ido da Waleed dakecin cheese duk ya batama Salim rigansa kayansa masu haske amman duk orange orange na cheese ajiki, tama Waleed alamu da hannu dayazo yawani kankame Salim abun yabata mamaki, Salim ya rufo motan yadan kalleta maida kanta kasa tayi, ahankali yace why were u at the company this night? Dan shiru tayi sai chan murya chan kasa tace bakomi ijiyan zuciya yasauke yace alright bari na maidake gidan na tambayi Baba meya faru aka miki duka haka a fuska basusan ke mace bace ya kunna motan dasauri tace ni bazani gidan nan b takasa karasa maganan sabida rawa da bakinta yafara kuka na neman kufcemata hawaye yazubo mata takai bayan hannunta ta goge fuskanta da sauri muryanta na breaking tace .nidai kabani Waleed nayi tafiyata thank you for everything takai bakin hijabinta ta daura kan fuskanta sabida bataso Waleed yasan she s crying yahau kuka shima, dan ijiyan zuciya Salim ya sauke yaja motan dasauri tasauke hijabin takalleshi ahankali tace ina zaka kaini shiru yamata bai cemata kala ba takai hijabin tana goge idanunta, Silver garden estate taga sunje