← Book details Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 93

Sashe 25

Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tajuya zata koma ciki dasauri Safeerah ta matso takama hannunta cikin kuka murya kasa kasa tace Mama dan Allah kiyakuri wlh bazan karaba karya kike cikani, cikani, kuma bazaki shigo dakin nan ba wannan ne hukuncin ki wuce kujeranchan ki zauna kiyi tunanin abubuwan dakikayi da basu kyauta ba, sai kinyi realizing mistakes naki kin fadesu da bakinki sannan zanyi tunani idan zan hakura na yafemiki ko bazan hakura ba, cikani Mama tajuya fizge hannunta tanuna mata chairs na zaman wajajen, wucewa Safeerah tayi ahankali taje ta zauna, Mama tace good start evaluating your action mara kunya tana maganan tabude kofa tashiga tsaf Salim yaji komi amman yayi kaman baisan abinda yafaru ba, yadubi Baba da oxygen ke hancinsa yana bacci yace ya farka Mama? Mama na daukan Waleed dayazo wajenta tace eh ya tashi dazu sun kawo masa abinci bai iyaci ba sai suka basa orange juice ya shanye gyadamata kai yayi yace Allah kara sauki bari naje naga Dr Isa Mama tace angode Salim Allah yasaka da mafificin alkhairi yamike tsaye Waleed ya zabura zai sauka daga jikin Mama tarikesa tace dadina dakai bakasan ya isa ba ko Waleed, ba a yawo a asibiti likita zaije gani kaji raurau Waleed yayi da fuska zai fashe da kuka hakan yasa Salim yaji wani iri a ransa saiya kawo hannu yace barsa Mama tsare Salim Mama tai da idanu tasaki Waleed dasauri yasauke jikinta kawai yayi hugging Salim, Salim felt something da little hug da yaron na yaro saiya duka ya daukesa yace ba inda zani don t be sad murmushi Waleed yamasa ya kankamesa, kofa yabude yafito Mama tabisu da kallo kaman wacce noticed something. Yana fitowa yahada ido da Safeerah da idanun nan suka rine da kuka is true fa old habit die hard tun tun tana yarinya daman ta iya kuka yanzu ma still ta iya, aransa yace stubborn girl dauke kai yayi yaja kofa yarufe yawuce abinsa batare daya kara kallonta ba tafiya one two three yayi yaji muryanta. Please kacema Mama tayakuri tabarni inga Baba juyo da kansa yayi dasauri ta sauke kanta kasa tana wasa da yatsu, murya kasa kasa yace why should I beg for a stubborn person when I know very well zaki karayin rashin kunyan girgiza kai tayi tana goge fuska da bayan hannu tace bazan karaba tsayawa yayi yakalleta kukan ya isa haka shima yagaji da ganinta tun jiya tana abu daya one thing about Salim is baida kunya and he s not just super bold he s extremely bold, dauke kai yayi yawuceta yakoma wajen dakin Safeerah tajuyo dasauri ta kallesa kofan yayi knocking tareda budewa Mama dake zaune gefen Baba tadago kai tana sauke ijiyan zuciya dan tunani take, ahankali yace Mama amata afuwa! Bazata karaba! Mama na kallonsa tace karya takemaka indai Safeerah ce saita kara ta gefen idanu yaga Safeerah tazo wajen tadan rakube a bangon dake gefen kofan hakan yasa strictly yace Mama duk randa takarama babba rashin kunya I promise dakaina zan umarci sojoji suzo su dauketa akulleta gidan gyara hali! Dawani mahaukacin sauri Safeerah ta kalli Salim dake kallon cikin dakin gabanta da kirjinta sun mugun bugawa, wanda yagama cewa ta aure sa ne zaisa a kulleta wato muguntan sojoji daban ne, Mama najin maganan tawani sauko daga gado tace ubangiji Allah yamaka albarka Salim! Kai kai kai Alhamdulillahi yau ka farantamin rai, ina ja iran hope tana jinka, ni dama kasa an tad da ita yanzu an horata ta gyara halinta dudda yanda idanunta suka kumbura saida ta kwalalosu sosai jin abinda Mama tafada, yace Mama tace bazata kara ba kibata second chance amata afuwa bari naje yajuya yawuce batare daya kalli Safeerah ba yana wucewa Mama ta leko ta kalleta tace Allah yakawomin maganinki bazanji tausayi ba wlh duk randa kika kara zan badake akaiki gidan gyara hali ahankali tace bazan karaba kiyakuri kwafa Mama tayi tajuya takoma ciki Safeerah tabiyota da gudu tai wajen Baba dake bacci ta rungume sa sosai sai kuka Mama ya watsamata harara dudda tabata tausayi Safeerah can be stubborn but abu kadan ke horata, she is sure maganan gidan gyara halin nan ya tsoratata tadauka da gaske suke. Saida Salim yayi hanyar office na Doctor ya dakata da tafiya ya kalli Waleed saiya tsuntsure da dariya, dariya looks so wired a face nasa dan baisabayi ba the way fuskansa was looking da dariyan yasa Waleed ya kwashe da dariya, ganin yanda Waleed kemai dariya yasa ya gyara fuskansa yayi murmushi kadan yace matsoraciya! Abun really crack him up he can t remember the last time yayi dariya haka, bude office na Dr Isa yayi yashiga. Almost 10mins yayi an office din suka fito tare zuwa mosque yana rike da Waleed sukaje masallaci sukai salla suka fito yakalli Waleed yace kanajin yunwa? Gyadamai kai Waleed yayi hakan yasa yadaukesa yashiga dashi cafeteria na hospital din cake yasaya masa yabasa bayan ya budemasa yafito suka wuce cikin hospital din sallama yayi gaban dakin tareda budewa daga Mama har Safeerah kallonsu sukayi Waleed da kansa yake tafiya hannunsa daya rikeda cake yanaci while dayan hannun nasa Salim na rike dashi gently yace jeka wajen Mama bari naje office tsayawa Waleed yayi yakallesa saiya dakatar da cake din dayake ci yayi wani iri da fuska zaiyi kuka Mama ta taso ta daukesa tace kaifa bakada adalci ko Waleed ka barsa yatafi aiki sainamaka bambooo Mama tadanmai kallon tsoratar da yaro lamo yayi ajikin Mama sai kawai yafashe da kuka that is so deep wani yirrrrr jikin Salim ya dauka ganin yanda Waleed yafashe da kuka Safeerah ta sauke kanta kasa ahankali, Mama tace laaaaaa kaga harda hawaye da gaske ne kukan nan yau adan hankali Salim yace Mama kawosa Dasauri Mama tace mance dashi katafi aiki abinka Salim zaiyi shiru juyoda kansa Waleed yayi yakalli Salim wani irin kuka yake harda ijiyan zuciya yana hawaye dawani irin sauri Salim yamiko hannunsa Waleed yataho dasauri daukansa yayi feeling very bad yaron na kuka yayi hugging nasa yajuya yace shiiiii stop crying ya isa ya isa yabude kofa yafice Mama tabisu da kallo zuciyan Safeerah yayi wani iri this cry confirms to her how much Waleed ke son mutumin nan, sai zuciyanta ya sosu ta tuna Abbati da shine yakamata Waleed nama kuka haka but he hates yaron tun yana ciki, wani tausayin Waleed yarufeta hawaye ya gangaro mata da sauri ta share Mama tace lurada ita but sai tayi kaman bata ganiba, suna wajen kusan 10min yakara knocking tareda bude kofa Waleed da kansa ya shigo rike da sweet da chocolate ga cake yamai waving hannu yace babyeeee shima Salim yace byeeee Mama tace angode Salim sai anjima wucewa yayi Mama ta kalli Safeerah tace bazaki je kimai godiya ba ahankali tamike dan bataso takara batama Mama rai, Mama tadauki Waleed itakuma tabude kofa tafito basa awajen dasauri tashiga tafiya tafito yana kokarin bude mota yaga tafito kallonta yayi saida takusan zuwa inda yake yabude motan yashiga yazauna, wajen window sa taje tasa hannu tai knocking, sauke glass kasa yayi kadan yamata wani kallo yace get in bana magana da mutane awaje yaja glass din sama abinsa bata ganin komi kuma, dan jim tayi sai kuma tajuya tazagayo ahankali tabude motan batare data kalleshi ba tashigo tazauna taja kofan tarufe, tasauke kanta kasa tashiga wasa da yatsunta ahankali, motan yayi shiru, chan tadago kanta tadan kalleshi ganin ita yake kallo da sauri tamaida kanta kasa kirjinta na dukan uku uku tacigaba da wasa da yatsunta murya chan kasa tace thank you for everything tayi shiru murya kasa kasa tace Allah saka da alkhairi, Allah kara budi da matsayi da daukaka, thank you dan lumshe idanu Salim yayi yabude har cikin ransa yaji dadi but yayi shiru, dan shiru tayi tanaso tayi magana but tana tsoro sannan she feels idan batayi ba kaman she s taking advantage of him ne azamanin nan waye zai kashe maka kudi haka, ba a tambayi Mama ko kwandala in this big hospital ba only mean yabiya komi, dan dago kai tayi ta kalleshi hada ido sukayi da sauri tamaida kanta kasa su wai sojoji haka sukeda kallo, tana wasa da yatsunta maganan na mugun mata wuyan fita tana kuma fargaban fadamai but haka tadaure amman tai kasa chan da muryanta sabida tsoro da shakkan sa tace nawa ka kashe mana ni da Waleed dakuma kudin asibitin Baba? In sha Allah I will work hard and pay you koda kadan kadan ne, uhmmm nawa ka kashe? Tai maganan ciki ciki wlh kalaman ma basu fito da kyau ba tsabagen tsoro dakuma fargaba, kusan two minutes taji shiru hakan yasa tadan dago kanta kadan faduwa gabanta yayi ganin wani mugun kallon dayake mata dayasa taji hanjin cikinta ya kada tamaida kanta kasa tawani yunkura dasauri takai hannu da gudu zata bude kofa ya danna lock wlh batasan sanda tace .kaya kuri idan maganata ta bata maka rai dan daidaita muryansa yayi dan maganan datamai yabatamai rai yace I will be back anjima da daddare for an answer game da maganan dana miki! Gyadamai kai tayi not herself why is he insisting about auren nan ita she hates aure, kai tsaye yace get out! batasan sanda tabude motan da sauri ba har saida kofan yadaki next car dake wajen tafito da sauri tamaida kofan ta rufe, reverse yayi dasauri yabar wajen tabi motan da kallo idanunta sunyi ja sannan tawuce takoma cikin asibitin takoma tashiga dakin nurse tazo da takarda tabata tai signing tafice Mama ta kalleta sosai tace meya ce? Faduwa gabanta yayi jin tambayan da Mama tamata sai lips dinta yahau rawa Mama ta tsareta da idanu ahankali tace cewa yayi wai bayan an sallamemu mu koma gidansa daya kaini nida Waleed jiya dukanmu muyi zaman mu wai yabani gidan shine nacemai a a banso tai shiru Mama dake kallonta tace sai yace mene? Kallon Mama tayi batasan mesa gabanta ke faduwa ba murya chan kasa tace yace tunda inada girman kai bazan amshi kyautansa ba wai zai aureki yabani gidan a matsayin sadaki yabani zuwa dare nayi tunani Mama na kallonta tace wani shawara kika yanke Safeerah? Dasauri takalli Mama tace Mama mesa kike min tambaya haka? Mama na kallonta tace aure nabiyu ne wannan
Chapter 25 · 0% Book details