Sashe 23
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawo mana gida batare dakun nemi iznin Momma na ba? Wlh sainasa kuma takore ku kaman yanda takori Safeer wani black kallo da Salim yamata yana saukowa daga few staircase dake wajen yasa tahadiye maganan ganin bata taba ganin hadaden guy irinsa ba damn he smells incredibly good, duk yawonta duniya bata tabajin kamshi mai dadi irin nasa ba, wuceta yayi yay gate yabude Mama tabisa itama Salma tabisu da sauri wata jeep urus tagani kofar gidansu aranta tace who is this Man! A ina suka sanshi? Baba yasa abaya Mama ta zauna kusa dashi yazagayo ta gaba ya shiga yaja motan da gudu Baba yafara tari sosai tana wheezing yakama hannun Mama cikin wani kalan murya yace ina Safeerah ? Cikin damuwa Mama tace na shiga uku Malam meke damunka iyye? Malam why are you confuse, kaga calm down tana kampanin datake IT lafiyanta kalau Oganta ma shiyazo nemanka kunyi magana, Malam kadena magana kaji asibiti zamu cikin wani irin murya yace ki rikemin Safeerah amana, ta wahala wannan mutumin yakusan kashemin y a! Mama Kubra ta cutarmin da yarinya amman bakomi akwai Allah akwai kuma rannan gobe kiyama, banso Safeerah takara wahala, agabana jiya an mari y ata, an doketa, an fasamata baki duk agabana, da Safeerah ta zauna inda za a cigaba da dukanta kaman jaka gwara na daukeku munje muyita bara a titi, kicemata nace tazo bazamu koma gidan ba, munbarsa, na yarda, bazan kara zama inda za a dinga zagin mahaifinta agabanta ba kinji, kucemata tadawo Mama na goge hawaye tace zan gayamata kadena magana ya isa kaji, babu abinda zai sameka Malam yana wani nishi yace ku saida kaya duka asaima Waleed abinc da kudin daidai sunkai wani military hospital nan da nan aka karbe Baba anan emergency akai ciki dashi nurse tace Sir zoka cike form yakalli Mama dake kuka yace muje Mama EPISODE 2 Binsa Mama tayi jikinta yayi wani irin sanyi ganin condition na Baba, she s regretting dama ta tsaya tabar Safeerah tai haukan nan data kwakkwadeta, yanzu ga jikin Baba ya birkice ta ina zata fara idan Baba ya rasu? How? Cike komi tayi tamike musu sannan takama bakin hijabinta takai saman idanunta tadaura awajen wani huci tafarayi sai kawai Salim ya sauke kansa kasa cikeda tausayin Mama kana ganinta kasan tayi bottling so many things aranta but yau takasa, ahankali Salim yace he will be fine Mama, babu abinda zai sami Baba da izinin Allah bakin hijabin tasa ta goge fuskanta tass tasaki hijabin she s very sad da jijiyan goshinta harya fito takada kai tace nagode Salim muje he felt really bad ta wuce yana biye da ita har zuwa wajen dakin da Baba yake ta zauna a kujeran wajen tabuga tagumi tana kallon dakin gabanta faduwa kawai yake jijiyoyi na bayyana na fuskanta, hawaye suka sauko takara gogewa dasauri ita kadai tace Safeerah bataji, bataji, bataji, yanzu abinda ta aikata wani fa ida ke tattare dashi? Saidai tashin hankali look at where Baban ta yake yanzu Mama tai shiru saikuma tajuyo takalli Salim da kyau ranta abace tace tasan mahaifinta baida lafiya Salim mesa kome aka mata bazatai hakuri ba, eh? Kallon Mama yayi asanyaye she is really angry kana ganinta kasan she s feed up tace Babanta baida kudi but muna rayuwan farin ciki da muna Kano, abu yafaru dayasa aka kona gidanmu bayan sunma Malam duka shine har yau baida lafiya, ga baya gani da kyau, nine nakira yayarsa Kubra wannan damuke gidanta na sanar da ita ga abinda ke faruwa haka ta aiko da kudi dubu dari da bamu dashi muka biya a asibiti aka dan bawa Baba taimako na gaggawa kafin drebanta ya iso yadaukemu muka dawo Abuja wajenta Mama tai shiru saikuma tafashe da kuka sosai Salim ya sauke kansa kasa, Mama tace nasan the reason Safeerah ke all abubuwan datakeyi sabida she had enough, kullum tana ganin ana zagin iyayenta ana cimana mutunci between Kubra da yaranta but nasha gayamata ke haka masu kudi suke barinma yan Abuja, society yakoma wani iri da me kudi ake respecting banda talaka, yau da ace Malam na da idanu yana aiki nasan rashin mutuncin bazai taba kaiwa haka ba sabida yanada nasa yanada na rike iyalansa no ita takiji takasa ganewa shashashan kanason kaga fadan Safeerah azageni ko mahaifinta agabanta bata iya hadiyewa, kasan mi Safeerah tayi rannan kuwa ? Mama ta share fuska da hawaye ke kwance tace rashin kunya da rashin da a ta sufafawa Yayar Babanta, wacce ta girmi mahaifinta fa sannan ta kama Salma da dambe, aiko Kubra tasa hannu da Salma suka bata kashi ban hanaba maganin mara kunya ai kenan fitsararriya har lokacin bai dago kai ya kalli Mama ba, Mama ta fuzar da iska tace Salim kaga nasan waye Mama Kubra nasan metakeyi amman no matter what ba abune mai kyau karamin yaro ya kalli tsabaragen idanun babba yayi rashin kunya ba bahaka iyayenmu suka taso damu ba, Mama Kubra tamana abubuwa da dama ciki harda lalata rayuwan Safeerah kaga bayan dawowan mu Abuja dayake anata fama da kai Malam asibiti tace tagaji zata aurar da Safeerah ga mai kudi ayi amfani da kudin a kai Baba asibiti tagaji da kashe kudinta wai kudinta gadon yaranta kasan marigayi tsohon gwamnan jigawa take aure Mama ta hadiye wani abu awuya tace ninasan harda jin haushi da tsanan Safeerah cewa sukayi wai abinda yafaru ita tajawo mana fitinan so she just wanted to teach the girl a lesson shine tasamo wani yaro mara tarbiya wai Abbati dan kawarta Malam na tsaka da ciwo tace aurar da Safeerah zatayi da ni da Malam babu wanda ya isa yace wani abu, haka ta aurar da yarmu agaban mu yabiya sadaki miliyan biyar Mama tafashe da kuka sosai kaman maganan was very personal for her kana goge fuskanta da bakin hijabi kana ganinta kasan she has been swallowing this pain aranta, Mama tace yarinya ta was just a little girl ko zance basu tabayi da yaron ba banda so daya da aka nuna mana yaron atare da mu da ita muka gansa yazo wajen Mama Kubra bata taba kebewa da yaron sunyi wani magana ba, rannan da akakai Safeerah rannan takirani tana kuka yamata duka sosai tana nishi kaman zata rasu! Dunkule hannu Salim yayi ahankali kansa akasa har lokacin, Mama tace haka na mike zumbur cikin daren nan hankalina tashe naje flat dinsu natadasu ina kuka wiwi na gayama Mama Kubra ga abinda Safeerah amman kiri kiri tamaidani shashaha tace idan banyi shiru nakoma na kwanta ba sai raina yabaci taso Safeerah nake kota lafiyan kaninta Mama tai shiru tana kallon tiles na floor na wajen looking lost a tunani tace kullum rannan duniya for good 6months sai yaron nan yama y ata duka ba dare ba rana amman dukan yafi faruwa da daddare idan yayi shaye shaye yadawo haka watarana asibiti suka kiramu ita Mama Kubra wai Safeerah na asibiti batasan inda kanta yake ba mukaje muka tarar ya mata shegen duka yasaketa saki uku wai shi bayason haihuwa kuma tayi ciki, watanta daya a asibiti tana jinya babu ko sisinshi Mama Kubra tabiya komi Baba yaso yaje police station tahanasa wai haka yaran masu kudi suke, karmu damu tunda tanada ciki zai dawo menene menene ahaka yarinyar ta haihu Mama Kubra takirasa yace kar akara kiransa ba dansa bane, he is not ready for kids, mu mukai komi, ganin anata surutu shine last 2yrs tasaka yarinyar a school, shima Safeerah tayi kuka dan nursing takeso da kyar na lallabata ta tafi architecture din Safeerah nada taurin kai wani abun sabida mu take shiru ga fada, nadade banyi fushi da itaba amman abinda tayi jiyan nan bazan hakura dawuri ba saitaga fushina this time around Mama ta fuzar da iska. Dr neyafito yataho wajen Salim hakan yasa yamike tsaye yace Dr Isa ? Anatse Dr yace Alhamdulillah he s stable for now, BP sa yayi sama sosai any further damuwa can push him to having stroke, Madam ya akayi BP sa yayi raising haka yanada damuwa ne? Fuska Mama ta goge zatai magana Salim yace zata iya shiga ta gansa?gyadamai kai Dr yayi yace of course Mama Salim ya kalla yace Mama je wajen Baba bayan nagama magana da Dr zanje nakawo Safeerah gyadamai kai tayi tace toh nagode Salim, Allah ya sakamaka da mafificin alkhairi gyadama Mama kai kawai yayi tawuce ya shiga dakin shikuma yajera da Dr Isa dayace who are this people Major? Why are you so ordinary dasu? Ina escort naka ? Wani kallo dayama Dr yasa Dr Isa ya kame tareda saramai yace Sir! Wani banzan kallo yamai yace give my patient your best I will be back yajuya yabar wajen yafita daga hospital din yashiga mota yaja. EPISODE 2 Bayan fitanshi tadade tsaye anan wajen dinning din kafin daga bisani ta wuce wajen ledan tabude kaman mai tsoro taga kayan yara sabbabbi riga da short masu bala in kyau da takalmi da pampers sai Chicco cream na yara da powder da soap, saikuma ledan maganin H-medix drugs ne aciki, tsayawa tayi tana kallon komi tana tunanin why is he so thoughtful? Yasan kome suke bukata kaman tabude baki ta rokeshi, wani bakin sealed leda dabata budeba tasa hannu ta dauka tabude ahankali ta ciro abinda ke ciki Saudi abayane mai kyau black ta warware dasauri size nata ne kuma 58, abayan smells kaman turaren sa it doesn t look like shi wannan yasayo a shago ne kaman daga gidansu ya dauko, maidawa da sauri tayi ta ijiye komi kawai saita wuce kitchen abincin daya zubar shida Waleed tasa broom ta share ta wanke bowl and spoon dayayi amfani dashi and keep everything a waje daya saita dawo falon tabude ledan, kayan Waleed kawai ta dauka da man shafan da sabulun tahada sauran abubuwan tamayar ledan chap itane zatasha magani, she hates magani ita chan magani shine ma abinda ke sata zazzabi, tawuce sama kawai daidai Waleed natashi daukansa tayi tawuce bayi ta tara ruwan zafi tamai wanka tafito ta shiryasa cikin kayan kuma daidai jikinshi yayi kyau tasamai takalmi sai kallonsa take he looks damn expensive a kayan kaman yaron yan gayun nan, kitchen tawuce tamai abinci tabasa yaci sosai itama tazo kaman