← Book details Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 93

Sashe 10

Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

M SHAKUR
EPISODE 9
Ahankali Momma tace
yanzu dai mubar maganan yaya ake ciki? Kama abokin naka maganan? I mean IT da Safeerah zatayi
? Dan tsaki yayi yace
wlh Momma I hate yanda kikesa nake wahala unnecessary sabida this your brother da family nasa haba I got better things to do
cikeda lallabawa Momma tace
so kake ayi dani ace na maidasu yan aiki agidana banma yarsu komiba? Ko yanzu ma ubanme Aunt dinku ta gwagwalada batace ba, dole nayi using school na rufe bakin kowa kodon abinda yasami yarinyar so please kayi?
Gyadamata kai yayi yace
yes yace nakawota though yayansa shine owner of the company yana China he
s expecting zai dawo ko yau ko gobe besides his brother baida matsala zai yarda even though basu taba barin yan IT a company su ba, in nutshell dai she can start yayansa ma hardly comes to the company kinsan soja ne, so shine ke komi kuma komi ke hannunsa
ijiyan zuciya Momma ta sauke tace
yauwa Shamsudeeni godiya nake babban mutum
tashi yayi daga gadon yace
good night Momma
Around 8:30 nadare yashigo gidan this time around bai bari sojoji sun kawosa ba, parking yayi yana kallon motocin dake compound din yafito anatse sai lafiyayyen kamshi yake yazare bakin glasses na idanunsa ya ijiye a mota yarufe yawuce flat nasu yabude kofa da sallama yashigo cikin falon wani attajirin magidanci ne a falon wanda zai iyakai 65yrs cikin manyan kaya tareda wani mai kama da shi da zaiyi 60yrs a gefensa suna magana ga kayan abinci agabansu sai kaninsa Auwal dake gefen Ammi laptop kan cinyansa yana tabawa, dakatar da magana magidancin yayi murmushi ya gauraye fuskansa yace
Sojoji
cikeda girmamawa ya sunkuyar da kansa ya maida kofan yarufe yazo har gabansa yadan duka yace
Baffa barkanku da dare, ina yini Dad
mugun kallo mai kama dashi yamasa yace
kaga daman dawowa daga Chinan? Ai dakai zaman ka saika dawo rannan daurin aure
dasauri Babban yace
waikai baka gajiya da fada daga dawowan yaro?
Tabe baki yayi yadauki jarida yabude yana karantawa, Baffa ya shafa kansa yace
ka sauka lpy, barrack kaje ne hala?
Gyadamai kai yayi alamun eh batare dayayi magana ba, Baffa yace
sannu da zuwa Salim, Ya shirin bikin
anatse yace
Alhamdulillah Baffa
Ammi tace
zokaci abinci
ahankali yace
okay
saiya wuce dinning dasauri Auwal yabisa Dady yadan sauke jaridan kasa yabisa da kallo kafin ya kadakai yasake bude jaridan yana dubawa, Auwal yace
Yaya akwai kanwar wata Abokina Shamsu dazatayi IT a company mu, I know kace no yan IT but please Yaya kaga nariga nacemai yes
dan kallonsa Salim yayi fuskan nan tasa ba walwala, Ammi dake zubamai abinci tace
tundazu yaketa nanata maganan nan Son, I told him daya sanar dakai kafin ya yarda but tunda kanwar Abokinsa ce ka yarda please na san Shamsu yana zuwa gidan nan he
s a nice boy kaji Son
ta shafa kansa, sauke jaridan Dady yayi yajuyo yakallisu yace
kazo company na kayi aiki ka makale ana yayanka gashinan kullum cikin roko kake kaman me bara
dukansu kallon Dady sukayi hatta Ammi bataji dadin maganan ba Baffa zaiyi magana Auwal ya jirasa yace
common Dad sau nawa zan gayamaka company Yaya is my dream, I studied architecture a school, mexanyi in your company when my brother open my dream company and gives me to manage
yayi maganan yana murmushi yana kallon Yayansa dake juya spoon, magana Daddy zaiyi Baffa yace
kafi kowa kewan yaron nan dabaya gari yanzu yadawo zaka fara
shiru Dad yayi bai kara magana ba.
Kansa Ammi ta shafa hakan yasa yadago yakalleta murmushi ya sakan mata kadan yadan lumshe idanu yabude sai yaja bowl of soup din gabansa yasaka spoon ciki yadeba zaikai baki saiya kallesu ganin duk shi suke kallo da Ammi da Auwal yasa yace
is there something in the food
? Kwashewa da dariya Auwal yayi yace
wlh Ya Salim baka iya cracking jokes ba badadi kai sojoji babu abinda kuka iya
, murmushi Ammi tayi tace
ci abincin ka mun dena kallonka
taja kujera ta zauna kusa dashi, kaiwa bakinsa yayi anatse yaci sannan yakalli Auwal yace
she can start
dunkule hannu Auwal yayi cikeda jin dadi yace
yesssss!
Ammi tai murmushi tace
thank you Salim
gyadamata kai yayi cikin muryansa kasa kasa yace
tell him within the week zanzo for supervision idan naga anything ba daidai ba I will fire both him and Paresh and nobody will use you to beg me Ammi! It won
t work
Ammi takalli Auwal dake dariya tace
kadaijiko
? Dasauri yace
I manage everything to perfection bazaka ga komi ba sai alkhairi Yaya, wannan uban salary da kake biyaba how can I joke da wajen cin abinci na
dan hararansa kadan Salim yayi yace
silly boy
shiru yamusu bai kara tankasu ba yacigaba da cin abinci while Ammi da Auwal na hira, Dady da Baffa na nasu a falo, bai wani ci sosai ba yadauki mug na coffee yamike baice musu komiba ya wuce stairs yashiga hawa Ammi tabisa da kallo, anatse yake tafiya kaman yana inspecting ko
ina dakin dake gaban na Ammi yawuce hannunsa yadaga yayi knocking so daya dudda kannensa ne baya taba fadawa dakinsu kai tsaye he respect privacy nasu, bude kofan akayi autansu ce Lubna batai wata wata ba kawai ta rungumesa tana washe baki dan tana bala
in son yayanta tace
Yaya kadawo? Oyoyooo
Ameerah da kanta ke a tsefe gashin kam acinye tazo itama tana murmushi akunyace gabanta na faduwa tayi hugging nasa tace
Yaya sannu dazuwa, Yaya kaga gashina duk yakarene saisa nasaka
Calmly yet strictly yace
is that ur excuse na yin abinda Allah yahana
? Dasauri ta girgizamai kai, anatse yace
Allah ya tsinema mai karin gashi, get ready I will take you to supermarket gobe to get the best hair products that helps with hair growth
gyadamai kai tayi tana murmushi tace
thank you Ya Salim
suna mugun tsoron sa but again kuma suna mugun sonsa, he
s just the best and very sweet but you need to be open minded before ka fahimce sa inba hakaba zaka dauka ya tsaneka ne, kusan 1min suna ahaka yace
ku cikani
dariya dukansu sukayi suka sakeshi wucesu yayi yashigo dakin Lubna ta kulle kofa duk suka biyosa bai zauna kan gadonsu ba saiya wuce gaban dressing mirror nasu ya zauna yayi crossing leg yanashan shayin ahankali yanabin ko
ina da kallo kaman wani invigilator this is just him haka yake, akwai observing environment nasa, he
s very very security conscious, gadaje biyu ne a dakin daya na kallon daya ga bra da pants akan gadon Lubna kallo daya yamusu yadauke kai yace
wat are those underwears doing saman gadonki Lubna?
Dasauri tayi wajen ta kwashe komi tawuce wardrobe nasu tabude tana sawa ciki tace
Yaya sunmin kadan ne Ammi tace nahada nafito dasu
wayansa ne yahau ringing da sauri Ameerah tazo wajen tace
Yaya Anty Nanah ne?
Kallonta yayi saiyasa hannu yaciro wayan ga sunan Nanah a screen din dasauri Ameerah tace
can I talk to her Yaya?
Dasauri itama Lubna tace
Yaya nima I want to talk to her
wayan yaba Ameerah yamike yace
idan kun gama ina wajen Ammi
yawuce yafice daga dakin yashiga dakin Ammi, Ammi na zaune saman gado hannunta rike da wata yar takarda yawuce yazauna kan coach na dakin yace
ina yini Ammi
murmushi tamai tace
yaushe zaka gidansu Khadija?
Dan shiru yayi Ammi ta tsaresa da idanu ahankali tace
Salim
dago kansa yayi yakalleta anatse yace
zanje
Ammi tace
before this week runs out kaje, kudan tattauna kaji me da me take bukata da babu na biki, get to know her, Nanah yar mutunci ce ga hankali da kunya, this is duk abubuwan damuka duba ni da mahaifinka muka hada aurenku kajiko
gyadamata kai yayi yace
okay
zata sake magana Ameerah tashigo rikeda wayan tace
Yaya ga Anty Nana
Ammi tace
Khadijah ce bani ita
dasauri Ameerah tawuce tabama Ammi wayan, Ammi tasaka wayan a speaker tace
Yar Albarka
akunyace tana murmushi kasa kasa tace
Ammi na ina yini ya gajiya yakuma karfin jiki? Ina Daddy na
? Ammi tace
Alhamdulillah duk muna nan lpy, Dadyn ki na falo, ya su Mama?
Nanah tace
Alhamdulillah Ammi, Ammi daman gobe inaso namiki burabusko na aiko miki dashi Ameerah tacemin kina sonshi sosai da miyan hanta
murmushi sosai Ammi tayi kana gani kasan maganan yamata dadi tace
gaskiya ne inaso kam sosai amman karki wahalar da kanki
dasauri tace
duk abinda zan miki ba wahala bane Ammi in sha Allah gobe zan miki
Ammi tace
shikenan Allah yayi albarka
ahankali tace
Ameen Ameen agaida Abba, saida safe Ammi
Ammi tace
Allah tashemu lpy
tabama Ameerah wayan tace
ungo ba yayanki
karba tayi tamike ta kaimai wayan karba yayi yasa hannu ya katse wayan yamike yayi kofa Ammi tabisa da kallo, hannu yasa zai bude kofa Ammi tace
I really love this girl Salim!
Chak ya tsaya batare daya juyoba, Ammi tace
s my choice and choice na mahaifinka, yarinya yar gidan mutunci, she
s those type of girls that will keep familyn ka together, tanason kanninka da yan uwanka duka, tana son mahaifiyarka da mahaifinka, this is dream of Everyman yasami perfect wife that have no any problem or issues with his family
shiru yayi baice komiba kusan 10secs kafin ahankali yace
good night Ammi
yabude kofa yafice.
LOKACI BAI KURE BA
Chapter 10 · 0% Book details