Sashe 26
Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kinada yancin zaban miji dakanki bata fuska tayi tace Mama ni bazan kara aure ba harna mutu zanyi tunani nasan inda zamuje idan an sallami Baba Mama tadade tana kallonta sai bata kara cewa komiba. EPISODE 2 Waleed shima bacci yayi dan yayi ciye ciyen nan Mama ta kwantar dashi kan lafiyayyen couch na dakin. Motsi Baba yayi hakan yasa daga Safeerah har Mama suka taso da sauri Safeerah tai wajen muryanta yayi rauni sosai tace Baba Baba kanajina gani nan bude idanunsa Baba yayi ahankali yadan gani dishi dishi but he was able to know Safeerah ce murya chan kasa yace Mamana kin dawo? Ina Waleed? Fashewa da kuka Safeerah tayi kawai ta rungume Baba sosai tace Baba kayakuri dan Allah, Baba baran karaba kayakuri I m sorry kaji Baba, sabida nine rashin lafiyanka yatashi ko, baram kara tadamaka da hankaliba kaji Baba hannunsa yadaga ahankali taredayin murmushi dan gaskiya yasami sauki yace ai kaganta ga kiriniya ga iya kuwa, Feerah rigima, ya isa toh bar kukan haka ya shafa bayanta Mama ta tsaya tana kallonsu kai Baba na son Safeerah bana wasaba to ko don ita kadaice yarsa oho amman baya wasa da Safeerah dagosa Safeerah tayi tana dago gadon ya zauna tace meke maka ciwo yanzu Baba? Girgiza kai yayi yace ba abinda ke min ciwo Alhamdulillah inama dan gani baga Waleed chan ga kujera ba yanuna Waleed dake bacci, Mama ya kalla yace waya kawoni asibiti ? Yayi tambayan sabida yasan ba Mama Kubra bace wannan dake fushi dasu ahankali tace Salim ne yakawo ka shiru Baba yayi yana tunani yatuna sanda yazo yana masa maganan Safeerah daidai nan Dr Isa yazo Baba yaduba tsaf sannan yayi murmushi yace bansan ko Major Salim ya gayamuku ba, inhar kanaso zaka bamu yardan ka muna kyautata zato zamu iya maka aiki a idanunka da sababbin technology mu dasuka shigo tsaf zaka iya gani, Major Salim yariga yabiya kudin aikin consent naka kawai mukeso dazaran BP ka yasauka sai ayi fixing time ashiga surgery Baba tunda Dr Isa yafara magana kowa na dakin kallonsa yake especially Safeerah da kirjinta yahau bugawa batada burin da ganin Baba ya dawo, wayan nan idanuwan sune suka tankwafar da Baba yakasa samin sana a muguwar yayarsa na yanda taga dama dashi, Baba yaje school yayi FCE he s such a good teacher idanunsa suka dawo he can look for teaching job again har ranta taji dadi, Baba yadan kalli Mama sabida shi kudin ne aransa sai cin kudin Ogan yarsa suke but saiyaga Mama ta gyadamasa kai hakan yasa yace to likita kunada consent dina a ina zanyi signing? Wata takarda yasan karba daga hannun nurse ya matso yasa a hannun Baba yasamasa biro Baba yayi signing, Dr Isa ya karba yace I will monitor you zuwa gobe idan BP ka yazama stable za asa lokaci na aikin gyadamai kai yayi yace an gode likita, Allah saka da alkhairi juyawa yayi yafice, Mama takalli Safeerah tace kinyi salla wai ke yarinyar nan girgizama Mama kai tayi, Mama tace tashi kitafi masallaci kiyi salla tashi tayi ba musu tawuce tabude kofa tafita ta rufo zata wuce saitaki ta tsaya dan yanda Mama ta korata when she can simply pray adaki is somehow kunnenta tasa jikin kofan muryan Mama taji cikeda damuwa tace Yayarka nata kiran wayanka Malam nasaka wayan silent banso yarka maraji tagane, sakon ta ya shigo ta aiko maka da sako a message wayan Baba ya kalla cikeda damuwa yace mita fada a sakon? Shiru Safeerah taji Mama tayi sai chan tace waya baka izinin shigomin dawani kato gida? Gidanka ne ko gidan ubanka ne? Gidana ake shigomin da wasu batare da izinina ba to bari kaji zumunci yaci uwarsa da ubansa tunda baku da godiyan Allah dakai da matarka kuma ku kama sahu kubi yarku ko kofar gidana kada ka kara zuwa inba hakaba saina maka wulakanci wanda harka mutu bazaka mantaba munafuki shashasha Mama ta sauke ijiyan zuciya ta kalli Baba tace yanzu ina zamu Malam? Ta ina zamu fara gamu da y a, gamu da jika? Kano zamu koma da ake nemanmu akashe? Inamu ina zaman Abuja? Ko an maka aikin ma a ido kafin kasami aiki it takes time a zamanin nan damuke, bazan maka karyaba nadamu Malam murmushi Baba yayi saiya rungumo Mama yanada danne damuwa yace kidena damuwa ni nasan Allah bazai barmu ahaka ba, ya isa dan Allah karki kuka yarinyar nan tazo ta gane wani kalan nauyi Safeerah taji zuciyanta yamata sai kawai ta tashi wajen kofan tawuce masallaci salla tayi tasa goshinta akasa takuma yi shiru kunya takeji tamayima kanta maganan aure after abinda tagani a auren, saita kasa rokon Allah komi ta taso kawai ta zauna har akai asir tayi sannan tadawo, tana bude dakin taga wani soja aciki yakawo basket dake dauke da manya manyan kulan abinci ga gwangwanin cerelac da madara a gefe aikin Salim ne, why is he so good to her? Meya yakemata alkhairi haka for mutumin da sau biyu sika hadu on Monday and Tuesday what is happening? Godiya Mama tama sojan yajuya yafita tabude kulan dan wlh yunwa takeji, tuwon shinkafa ne da miyan kuka mai kifi da kaza da man shanu, sai jellof rice da chicken tace mezan sama ka Malam ahankali Baba yace tuwon yabani sha samai tayi ya karba yafara ci sai kallonsa Safeerah take Mama ta kalleta tace ke bazaki ci ba ahankali tace anjima zanci duk son abincinta dakuwa yamata yawa she loose apatite. EPISODE 2 Shi daman iyayensa sun sani ko yana gari baiwani cika zama gidansu ba sai idan yaga dama ko Ammi na kewansa he s always fighting da Daddy so he s avoiding him, gidansa na barrack yawuce bayan yatashi daga office, wanka yayi yasaka simple yadi brown jumper ce dinkin, Hermes slippers yasaka na maza yafito yana zuba uban kamshi, wata envelope dake kan table na falon yadauka yabude yaciro takardan yakalla sai kawai yamaida cikin envelope din yarike yafito yashiga mota, super market yabiya yayi sayyaya mostly for Waleed ne da irin kayan tea yasaka a booth yakoma gaba yawuce hospital wasu soja yabama kayan akai dakin ya tsaya yayi isha i a mosque yayi magana da Dr Isa yana basa update kan lafiyan Baba. Duk suna dakin Mama na goye da Waleed da akeso yayi bacci dan rigima yake saiya fita waje wasa yamafara gyangyadi while Safeerah na magana da Baba akai knocking Mama tawuce tabude kofa soja ne yashigo da uniform da leda yace good evening Oga yace na kawo he s coming ya ijiye yajuya yafita Safeerah tai shiru tana kallon kayan kaman yanda su Baba keyi tace zan maidamai abun yayi yawa Baba ahankali yace ke kul babu kyau maida kyauta bata sake magana ba almost 20mins akai knocking tareda sallama gabanta kawai yafadi jin muryansa, Mama tace shigo Salim bude kofan yayi yashigo Safeerah takasa kallonsa ya gaisa da Mama yama Baba yajiki, Baba yace Salim dawainiyan nan batai yawa ba? Toh mungode Allah amfana, nagode kwarai Allah ya saka da mafificin alkhairi kansa yasauke kasa yace Allah kara lafiya Baba, kadinga cin abinci akai akai sannan karage damuwa Baba, duk batada amfani Baba kadakai yana yabawa da natsuwan Salim da hankalinsa yace ba shakka haka maganan ka take Salim, Allah yayi albarka anatse Salim yace tom Allah saida safen ku Allah baka lafiya Baba sosai Baba yaji dadin addu an yace Ameen Ameen Salim nagode sosai juyawa yayi yasaci kallon Waleed dake bayan Mama karaf Mama ta lura murmushi tayi tace abokinka yayi bacci da yanzu yafara binka sunnar dakai kasa yayi yace saida safen Mama, zanzo gobe da yamman In sha Allah Mama da Baba sukamai godiya, Baba shi kawai yanason yaron wlh hakan yasa yakalli Safeerah yace baki iya gaisuwa bako, anyways ke jeki masa godiya ita sai yanzu tasan bamatayi gaisuwa ba, mikewa tayi tawuce tana bude kofan tagansa tsaye gefen kofan saida gabanta yafadi, kaman daman ita yake jira yayi gaba abinsa tabisa abaya dudda bataso taje har waje ya shige mota kin shiga motan tayi hakan yasa yasauke glass yamata wani kallo dasauri tashigo tamaida kofan tarufe, Envelope yadauka yamika mata yace take this dago kanta tayi takalli abinda yake bata but kallon dayake mata yasa tasaka hannu ta amsa ahankali gabanta na faduwa yadauke kansa yakalli kofa yace that is the house papers! Dasauri ta kalleshi shima juyowa ya kalleta da kyau wani irin kwarjini yamata dasauri ta sauke kanta kasa chan yace remember i made this offer since naga baki son kyauta it hurts your ego yasake shiru chan for the second time today yace marry me Safeerah! Wlh gabanta faduwa yayi da karfi akwai yanda kalman ke fita daga bakinsa yake shiga kunnenta, why is he so adamant about ya aureta, yanda kirjinta ke bugawa saitaji gumi yasoma keto mata, he sees and noticed yanda take tsoronsa if he wants zai iya tsoratata now and hear ta yarda da zancen auren but baison haka, shi ko bata auresa ba yariga yabata gidan har ransa, he s just using the gidan ne as excuse he really wants to marry her, dudda baida tsoro but deep deep chan chan kasan zuciyansa baisan mesa ba he s scared kartace bazata auresa ba, kotace ta yarda ta karbi kyauta basai sunyi aure ba, he s just praying kar her little brain dinta yayi wayon gayamai haka, shi kansa baisan mesa he just wanna make her his ba, baitaba feeling haka for Nana ba, but look at the way yakeso wata tace ta yarda zata auresa. Calmly yace I told you nabaki zuwa dare for final decision naki, here are the papers kirike gidan nan amatsayin sadakin ki dasauri tadago kanta takalleshi gabanta na faduwa batason aure, dan rage muryansa yayi yace a musulunci mace can decide to collect anything as sadaki, zaman n Annabi akwai wacce aka bawa takalmi a matsayin sadaki, akwai wacce aka koyama suratul Fatiha a matsayin sadakinta! Baki Safeerah tabude dake rawa sosai zatai magana hannu yadaga mata hakan yasa maganan ta makale a wuyanta yace I am not forcing you, aurena is your decision! I just wants to help you! I don t need anything from you kome azuciyanki, kome