← Book details Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 93

Sashe 44

Lokaci Bai Kure Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dina makemata kafada Waleed yayi ya manne jikin Mama yadena wasan ma dan sarai yaganesu, Momma dake kallonsa tace harka manta mu rigimamme fitowa Yasmeen tayi da drinks da snacks, Baba yakalli Safeerah yace badake nake magana ba Mamana Zainabu tace zauna Safeerah zuwa Safeerah tayi ta zauna ahankali kanta akasa. Anatse Zainabu Mom tace nasan abubuwa da dama sun faru but yanzu ba lokacin maimaita kace nace bane, mu ukun nan iyayen mu suka haifa, zumunci yawuce wasa, komunaso ko bamuso duk jini daya muke anan, komi yariga yawuce, Momma mahaifiyarki ce Safeerah ke kuma diyarta ce, an samu sabani ada kwarai but yafiya yazama dole dan haka inaso kibata hakuri sabida arufe chapter gabaki daya abude sabuwa afara shirye shiryen biki Zainabu tai shiru duk ana kallon Safeerah data haderai sosai takalli Zainabu tace ni bazan bata hakuri ba sai yarta Salma tabama Babana da Mamana hakuri! Ai iyaye basufi iyayeba, bakuma daraja tafini ko iko ba dazatai tunanin zata zagi iyayena ta gayamusu maganan banza bazata bada hakuri ba sabida sunada kudi mu bamuda shi dan haka ni nabayar, I am never going to live wannan rayuwan again, I am sorry Ummi but zumunci ba dole bane, and idan kunaso ayita daga yarta har ita Momma saisun bama iyayena hakuri ko sutashi su bar gidan nan! Kowa na dakin kallon Safeerah yake Safeerah ta bala in burge Yasmeen, Baba yace Mamana kinkosan Momma Adda na ce? Ran Safeerah abace tace Baba nikuma yarka ce! Mama ko kadan bataji zafin maganganun Safeerah ba, Ummi takalli Salma data batarai tace sauka kasa ki duka kiba Baba da Mama hakuri dan kin musu ba daidaiba saukowa Salma tayi Safeerah na kallonta sosai tai murmushi tace Baba and Mama nayi kuskuren abubuwan dana muku kuyakuri kuyafemin, bazan karaba, I am very sorry about everything saikuma tajuyo takalli Safeerah ahankali tace I am very sorry cousin forgive me okay kasa yarda Safeerah tayi Salma Salma dai data sani ke bada hakuri haka, Baba yace mun yafe miki Salma, Allah ya yafe mana gabaki daya yakalli Safeerah yace Adda na don t have to tell me sorry agabanki, tana gaba dani kuma daga gidanta muke now kibata hakuri Safeerah ko zan sabamiki hawaye cikowa idanunta sukayi ahankali tace kiyakuri Momma kiyafemin murmushi Momma tayi wanda iya lebe ya tsaya tace bakomi yawuce Allah ya yafemu gabaki daya, ga yar uwanki nan Salma sai ayi komi tareda ita, ga Yasmeen itama tazo kuhada kanku kunji, let us all close the old chapter gyadamata kai sukayi, Momma ta kalli Salma tace Feerah batace tayafe miki ba sake bata hakuri ga mamakin Safeerah sai Salma ta taso tana murmushi tazo gabanta sai kawai ta rungumeta tace m sorry Feerah! And I love you so very much, sorryyyy pleaseeeeee, I am ur big Sis fada dake is norms but baran karaba kiyakuri kinji, I love u alot wani sanyi Safeerah taji idanunta suka cicciko da hawaye tana tuna abubuwa da dama da Salma tamata takai hannu ta goge hawayen dasauri Salma ta taso takalli fuskanta takai hannunta ta share mata a fuska tace I made my sister cry kiyakuri Kinji forgive me pls muryan Safeerah nadan rawa tace yawuce nima kiyakuri duk abinda namiki Salma tace yawuce har raina takara hugging Safeerah tana shakan kamshin datake da ita kanta mace tanaji kaman ta hadiye Safeerah balle kuma namiji sannan tasaketa tace Yasmeen kutashi muje sama dakinmu mubar iyaye suyi magana Salma tasa hannu tawani kama Safeerah tana dagota sukai sama while su Baba suka cigaba da tattaunawa. Sosai Salma tadinga hira dasu tun Safeerah bata sakin jiki harta saki jikinta suna hira dan gaskiya batada riko ko bakin zuciya, idan ta yafe ta yafe. Sai yamma Momma tace tazo sutafi Salma tace ita anan zata kwana, Yasmeen daman tana nan haka ma Mom ga mai gyaran Safeerah, Salma so kawai tasan wanene me kudin daya chanza rayuwan mutanen nan haka? Who is he?. EPISODE 4 Around 6 na yamma ya sauka a lagos jirgin yan airforce yabi, wani gidansa dake Ikoyi yaje, shifa daman yanada yawan tafiye tafiye but wannan is work related, kawai he just wants to rest from all the bacinrai na this past few days sannan yayi prepping kansa for this walima and tarewan matarsa. Gidansu yacika dayawa ga gidansa na barrack ana aiki, duka duka yau is just 3days left a daura auren Auwal da Nanah, he just pray kanninsa enjoy this marriage and he wish them the best, May Allah bless union nasu, bazaije daurin auren ba cus baimaso yahadu da family ta at all yariga yabarta yabarta baiso kananun magana. While tarewan Safeerah saura 10days yau, sai ana 3days to tarewanta zai koma Abuja. Wanka yayi yaci abinci cus yanada chef yakirasa kafin yazo daman yayi shiru he s just remembering the hug he shared da Safeerah, how he felt in his body baitaba jin hakaba, yakasa mancewa cus it s such a great moment for him, this days kuma bacci na gagaransa all because of the hug, what is happening to him? What is wrong with him? Shi yasan har cikin ransa, harga Allah sabida ya taimaki Safeerah ya aureta, he deeply cares for her sabida she deeply cared for him then, she was crying for him sosai seeing him in pain mutamun dabata saniba just because tagansa in pain, is that the reason yake jinta haka in his mind har bayaso yahadata da wata? He knows this Safeerah is one big reason dayasa he couldn t go on da auren Nanah, he just wanna see her smile, and happy, idan yaga she is sad he feels sad, yanzu he thinks he feels something else especially when she hugged him, and he keeps feeling the urge to go back for the hug maybe yamayi advancing, kiss, also love making, sake lumshe idanu yayi tsigan jikinsa natashi abun is too much kaman zai haukace sabida ita, kaman yakira yasa akawomai ita Lagos right now, sai kawai yakai hannunsa yadauki wayansa yayi dialing number ta, Yasmeen tafita ta zubo musu abinci, Safeerah na bayi, while Salma na kan gado har yanzu batai isha i ba su duk sunyi ganin wayan Safeerah na ringing taga Major Salim dasauri tadauka takai wayan kunnenta tawani kashe murya kaman yar mage tace Hi Major Salim danzare wayan yayi daga kunnensa ya kalli screen sannan yamaida wayan kunnensa kawai ransa yahau baci da kyar kaman ana begging dinsa yayi magana yace where s my wife ? Yayi maganan cikeda iko, sounding brutally rude cikeda rashin mutunci fa, wani iri Salma taji jin baida kirki irin he s not even interested in knowing waye ita data dauki wayan ko? Matarsa yake tambaya baida ma interest na sannin wacece ita ta dai daure cike da duniyan ci ta sake kashe murya tace I am Salma Feerah s Cousin, she s using the restr dip ya katse wayan daidai Safeerah nafitowa daga bayi dasauri Salma taji gyara fuskanta tajuyo tana murmushi tamika mata wayan tace wai wannan miji naki kaman mai anger issue baima jira na gama gaya masa kina restroom ba, wai Allah sa dai ba mai dirkanki kika kwaso ba, dan masu kudin nan sai ahankali barinma sojoji Allah sa ba yayan Abbati bane wannan ba daidai Yasmeen na shigowa dakin tace Allah yarabata da mutane irin su Abbati kekuwa Salma kidinga fadin alkhairi, not all men are bad dasauri Salma dataji kaman ta make Yasmeen tace ke kinsan waye Soja kuwa? Me kika sani game da Soja? Lemme tell you kadan, kinga Sojoji akwai su da son mata, ga iya dukan matan kuma, ga hanasu fita wlh, ga bala in neman mata, mace daya bata isarsu that is masu tsoron Allah kenan da basabin na waje, ga uban kulle, basa barin matansu da kawaye, ga kishi maida matayensu ustazai suke wasu har nikabi sukesa matansu sawa, sannan basu da kirki ga bakin mugunta wucewa abinta Safeerah tayi tai kaman bata jinsu but gabaki daya duk maganan na kunnenta, somehow she s believes Salma cus zancen kulle da all those rules tagani, da sauransu, gabanta se faduwa yake, anytime zatai tunanin wani abu she remembers she s doing it for iyayenta da ba auren nan ba da yanzu suna gidan Momma an cigaba da wulakanta su inama ace zata sami wani aiki ko kwangila da zata sami kudi tasayama iyayenta gida dataji dadi wlh, kayan bacci tasaka tadawo ta zauna cikinsu zatai magana wayanta yafara kuka Yasmeen tace yana kira again kai wannan miji naki na sonki Feerah daukan wayan tayi ahankali saita tashi daga wajen tazauna kan gado takai wayan kunnenta tana dan satan kallon su Yasmeen da Salma daba ita suke kallo ba tace hello batare daya amsaba yace next time tell those people su dena daga miki kira ahankali tace sukai shiru kirjinta nadan bugawa gently tace ina yini ahankali yace how are you? Ya Waleed? Batasan mesa ba anytime ya tambayi Waleed wani irin sanyi takeji aranta mara misultuwa tanason aso Waleed, duk maison Waleed automatically yake stealing heart nata, ahankali tace Alhamdulillah we re fine, Waleed na wajen Baba akasa gyadamata kai yayi chan yace nayi tafiya ina Lagos shiru tayi batasan mezatace ba, ahankali yace ana biki agidan mu, Auwal is getting married rannan asabar asanyaye tace Allah sanya Alkhairi, Allah yabasu zaman lpy shiru yayi yana sauraron addu anta harta gama zuciyansa namai dadi sosai, murmushin yayi kadan da saida taji karan murmushi hakan ya mugun bata mamaki dan bata taba gani ko ji yayi murmushi ba sai yau, ahankali yace Ameen nagode, kina bukatan wani abu ? dan shiru tayi kafin tace takasa sakin jiki dashi batamasan tayaya zatayi ba, even though ta taimakesa da to ko aranan ai duka duka awa nawa sukai tare and she was small then ga yarinta, batasan ya ake mu amala da maza ba, yanaso yajata da hira taga he is not that strict or wicked datake tunani but he noticed bata iyaba, hakanan even though bawai wani maganan kirki takemai ba tana dari dari dashi but he s enjoying dan maganan dasukayi, kaman karya mata sallama but baisan mezai kara cewa ba jin shirun yayi yawa yasa yace saida safe Allah tashemu lpy
Chapter 44 · 0% Book details