← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 85

Sashe 9

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suyi musu sallama suka fito daga falon gabad'ayansu kowa ya nufi d'akunansu Dan kwanciya. Suna fita Mai martaba ya dubi Ammie yace . "Fulani! nace ba kunya waya da Afeef kuwa?..." Ya fad'a Yana kallan Ammie. Ammie ta sauke numfashi kafin tace. "Munyi waya d'azu rankai Dad'e ya k'irani yace min nan da two weeks zai dawo". Mai martaba ya jin jina kai yace. "Eh Nima haka yake fad'amin yace zaizo break koma two weeks ne to 3 ?..." Ammie tace. "Eh Allah ya kawo shi lafiya" Mai martaba ya ansa da ameen daga haka suka cigaba da hira kafin daga bisani Kuma su tashi Suma wuce d'aki Dan su kwanta Dan dare ya riga da yayi. Washe gari da safe ya kasance Ranar Monday ,wacce ko baturema Yana tsoron Monday. Huyaam ce tsaye a gaban mirrorn Dake d'akinsu wajen k'arfe 8 Saura na safe tana sanye da uniform d'inta na school tana graya zaman hijab d'in jikinta sai Wani murmushi takeyi ita kad'ai.Huda ce tashigo d'akin itama cikin shigar uniform Irin na Huyaam Sak zata dauki Wani text book d'inta data ajiye jiya a d'akin shine ta shigo zata d'auka ta tsaya kawai tana kallan Huyaam da mamakin Ganin yadda take wani murmushi ita kad'ai a d'aki.had'a idon da sukai da Huda ta cikin mirrorn Hakan yasa Huyaam ta juyo tana fuskantar Huda tai mata fari da ido tace. "Wannan kallan fa?..." Huda ta sauke numfashi tace . "Dole na kalleki ke kad'ai a d'aki ki tsaya gaban mirror kiyi ta murmushi ke kad'ai". ta fad'a tana kallan Huyaam wacce ta k'ara fad'ad'a murmushinta . Huyaam ta k'ara mata fari da ido kafin tace. "Dole ki ganni cikin farin ciki mana Huda nida zan zama graduate na shiga university kamar yadda ya Zarah takeyi yarinya". Ta fad'a tana Wani bouncing. dariya ce ta kama Huda Jin abinda Huyaam ta fad'a Amma sai batai ba tace . "Uhmm!! nidai Dan Allah yanzu ki taso muje kiyi breakfast ke kad'ai ce bakiyi ba tun d'azu ake jiranki time na tafiya kinsan fa 10 zamu shiga exam" tana fad'ar haka ta k'arasa gefen kan side drawer inda ta ajiye book D'in nata ta tafi zata d'auka.Huyaam ta bar gaban mirror tace . "Muje ai nagama Nima" ta fad'a tana d'aukar school bag d'inta.suna fita falor babu kowa a falon Dan kowa ya tafi inda zashi su su muneefa sun tafi school tun 7:30am ya Zarah Kuma tana d'aki sai anjima zata tafi school d'in itama . HUYAAM ta k'arasa dining ta fara breakfast d'in,ita kuma Huda ta shiga kitchen d'auko musu ruwa....bayan HUYAAM ta gama breakfast ta mik'e ta fito daga dining d'in zuwa nan cikin falon adai dai lokacin da Ammie ta sauko k'asa zuwa falon tana kallan Huyaam tace. "Kinci abincin ne?.." Ta fad'a tana kallanta . HUYAAM ta shafa cikinta tana k'ok'arin d'aukar school bag d'inta tace . "eh naci Ammie yanzu ma zamu tafi". ta fad'a tana rataya jakar. Ammie ta jin jina kai tana kallansu ganin sun gama shirin Suma tafiya zasuyi.HUYAAM ta k'araso har gaban Ammie tai mata side huge tace. "Mun tafi Ammie" ta fad'a tana murmushi.Ammei ta shafa kanta ganin haka yasa itama Huda ta k'araso ta rungume Ammie ta D'aya side d'in nan ma Ammie Shafa kanta itama kafin tace. "Allah ya kiyaye ya Bada sa'ar exam daughters"ta fad'a tana murmushi.duk suka ansa da Ameen daga haka Ammie ta sakesu suka fito daga falon ganin lokaci na tafiya. Tun kafin su fito tuni Aziza da su ikleema sun fito suna zaune a cikin motar suna jiransu,tun daga nesa da Aziza ta hango su ta d'auke kanta tana kallan gefe har suka k'araso suka shiga cikin motar ko zama basuyi ba Aziza taja Wani uban tsaki Kafin tace. "Aikin banza aikin wofi sai yanzu Kuka ga damar fitowa tun d'azu mu muna nan muna zaman jiranku Kun kama kun Bat'a mana time akan aikin banza,to wallahi daga Yanzu idan kuka K'ara yin let wallahi tafiya zamuyi mu barku saidai kusan ya zakuyi aimu ba bayinku bane bare mu jiraku"ta fad'a tana hararar HUYAAM.adai dai lokacin da aka rufe k'ofar motar dogarin Dake Rakasu school ne ya rufe murfin Motar sannan ya Bud'e front seat ya shiga.driver Kuma ya ta-da motar. Huda ta Kalli Aziza fuska d'aure itama tace. "Dan Allah Aziza karki fasa kisa d'in a tafi a barmun sai me idan har kinga zaki iya sawar tunda ke Neman masifa baya miki kad'an".Huda ta fad'a tana hucii ikleema ce tasa musu Baki tace. "Dan Allah kuyi hak'uri ya isa haka" , sai kuma ta Kalli Aziza tace. "kema Aziza ba'a haka Bai kamata ki fad'a musu haka ba kema yaushe kika daina yin let d'in da har zakiyi wasu cewa sunyi letting ko kin manta time d'in da muke zaman jiranki kafin ki fito mu a time d'in sai muce me? kika San Mai yasa yau d'in Basu fito da wuri ba" ta fad'a cikin ruwan sanyi... Aziza ta juya ta harari ikleema kafin tace. "Eh dole kiyi magana tunda na tab'o iyayanki, To bari Kiji in fad'a miki karki K'ara samun Baki idan Ina magana da su Bada ke nake ba"ta fad'a tana juya ido. A dai dai lokacin da suka fice daga cikin palace d'in gabad'aya za'a kaisu school d'in. Ikleema ta tab'e Baki tace. "A'a!! ni baza kiyi Dani ba sai dai ki nemi abokin Yi" tana fad'ar haka ta juyar da kanta gefe.ita dai HUYAAM dama Batai magana ba ita da safnah Dan ko kad'an Huyaam Batasan hayaniya.bugu da Karima taiwa Aziza uzuri tunda ta riga tasan halim Aziza tunda ba k'aunarta take ba. Wani malolon bakin cikine ya tsayawa Aziza A wuya tai ta masifa ganin Huyaam Bata kula taba Dan ta tsani Irin wannan halin na Huyaam na tai banza da mutum , sannan ta bawa banza ajiyar sa Aziza tafiso ace Huyaam ta tankata ita Kuma tai mata tass sai Kuma taga ko ta d'ago kai ta kalleta Huyaam batai ba bare ta Maida ta mutum,nan Aziza ta cigaba da fad'ar magan Ganu duk dan Wani ya tankata Acikinsu sai dai hak'arta Bata cimma ruwa ba Dan dukkansu babu Wanda ya kulata saima hira da suka kama yi duka ukun Amma Banda HUYAAM wacce take kallon hanya .Babu dad'ewa suka k'araso school d'in wacce take ta 'ya'yan manya Dan daga 'yay'an gomna saina sarakai irinsu Huyaam sai kuma Wanda yake da kud'i Mai suna kud'i ne kawai zai iya sa 'ya'yansa a school d'in saboda tsadarta,ga kyau da Kuma tsari uwa uba Kuma ga karatun da ake koyar musu acikinta Dan school d'in Babu k'arya tayi sosai ta ko Ina. bayan sun shiga ciki driver yay parking anan inda akeyin parking. Dogarin nan Dake gaban motar yay saurin Bud'e inda yake Zaune ya fito ya Bud'e musu k'ofar duk suka fito D'aya bayan D'aya Aziza ce ta karshe wacce ta cika tai fam k'iris ya rage ta fashe saboda haushi. Suna gama fitowa Kowa ya nufi hole d'in exam d'insu, HUYAAM da Huda da safna a hole D'aya sukeyi sai Aziza da ikleema da sukeyi a hole D'aya Suma driver ya juya suka koma palace d'in idan sun tashi kuma su zo su d'aukosu. ____________ Har ya Zarah ta dawo daga lecture su HUYAAM Basu dawo daga school ba saboda paper biyu sukai yau hadda practical sukayi basu suka tashi ba sai k'arfe biyar da Rabi na yamma suka taso ,duk agajiye suka dawo gidan da sallama suka shigo falon nasu babu kowa a falon sai k'arar AC direct sama suka haura zuwa d'akinsu nan suka tura k'ofar suka shiga suka tadda ya Zarah tana zaune gefen gadonsu tana waya sai Wani murmushi take. HUYAAM ta Bude ido ta juya suka had'a ido da Huda ganinsu yasa ya Zarah ta fita daga d'akin nasu bayan ta kullo k'ofar ta koma nata d'akin .ganin ya Zarah ta fita daga d'akin yasa huyaam tai k'asa da murya tana kallan Huda tace. "Ko waye yayan namu ne?..."ta fad'a tana gimtse dariyar ta.huda ta juya tana kallon k'ofar Ganin ya Zarah ta fita kafin ta juyo ta k'araso kusa da Huyaam Tai mata rad'a a kunne tana dariya .take itama HUYAAM tasa dariyar tana rufe Baki tace. "Dan Allah fa Huda?..."Huda tai murmushi tace. "Babu ruwana wallahi idan taji, Kinga nidai ban fad'a miki ba Dan ki fad'a mata danni ma ban tabbatar ba". HUYAAM ta rik'e baki tace. "Yo nima hau ne akaina da zan fad'a mata salon ta dokeni" Huda tace. "To dai gara kiyi shirun". daga haka ta ajiye Jakarta ta fito daga d'akin HUYAAM Kuma ta fara rage kayan jikinta zata shiga toilet Dan yin Wanka. Bayan magrib gabad'ayansu suna zaune a main falorn gidan kan babban carpet d'in Dake shimfid'e anan tsakiyar falon suna karatun Al'qur'ani Dan dama haka suke duk ranar da suke da paper wacce zata kaisu har k'arfe biyar zuwa biyar da Rabi na yamma Basu Samu damar zuwa ismaliya ba to to da daddare sai sun biya wannan Karatun Daya wuce su yadda idan sunje islamiya saidai kawai su Bada hadda kawai ,wannan tarbiyar Ammie ce.yanzu haka suna cikin karatun aka fara K'iran sallahn isha'i Hakan yasa zasu tak'aita saboda K'iran sallahn da ake Saida suka kai aya sannan suka tsaya saukai addu'o'i sannan suka mik'e zasu kabbara sallah ganin ana k'ok'arin shiga sallahn a masallacin palace d'in. Suna idarwa suka shige D'aki Dan cire hijab d'in jikinsu sannan Kuma saisu fito suyi dinner..... 07066508376_______ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *paid book *Free pages* *NA* *___(MRS SARAKIES ___* *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 8 ____________ Washe gari HUYAAM basuda paper Dan haka basuje school ba itakan batama tashi daga bacci ba sai after 10:00am sannan ta fito daga d'aki bayan tayi wanka ta sauya kaya daga na bacci zuwa na gida ta fito daga d'akinta zuwa k'asa Dan yau a d'akin da yake mazaunin nata ta Kwana ba'a na Huda ba Wanda suke kwana da Huda tare,a k'a'ida d'akin kowa daban agidan to sune dai har yau Basu Raba wajen kwana ba ita da huda kodan sun taso tare ne oho. bayan ta sauko downstairs ta k'araso dining ta zauna Bataga kowa a falon ba harta ta fara breakfast
Chapter 9 · 0% Book details