Sashe 16
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fulani Salamatu ta shigo d'akin bakinta d'auke da sallama ta k'araso ta zube gaban Aziza kanta a k'asa tace . "Ranki Dad'e fulani tace idan angama miki kije tana san Ganin". Aziza ta ya Mutsa fuska tace . "Kije kice mata Ina zuwa".ta fad'a tana juyar da kanta gefe.hadimar Fulani Salamatu Mai suna Karima ta sunkuyar da kanta k'asa cikin girmamawa tace. "To ranki Dad'e afito lafiya".tana fad'ar haka ta Mik'e tabar d'akin. Babu dad'ewa Aziza ta fito zuwa d'akin ta shiga na fulani Fulani Salamatu ta sameta itama taci kwalliya tana zaune bakin gado ta k'arasa tace. "Mummy Gani". Fulani Salamatu tace . "Dama tambayar ki Zanyi zaku fita da kayan naki yanzu ne ko sai Kun gun gama parting?.."ta fad'a tana kallan Aziza....Aziza ta yamutsa fuska tace. "Mummy sai za'ayi pictures tukunna". Fulani Salamatu tace . "A to shikenan kije"Aziza ta juya ta fita daga d'akin ta sauko downstairs Dan k'awayen nata tuni sun fita compound Dan anan za'ayi partyn. Lokacin da Aziza ta fita compound ya Allah.wow haka ta Ambata ganin Yadda akai decorations d'in wajen, Dan anan compound daga jikin bango akai decorations d'in da balooms da flowers haka aka mam manna awurin, wurin yayi kyau ba kad'an ba . tsakiyar wurin kuma aka shim fid'a Wani k'aton carpet akai sai table a tsakiyar sa Wanda akai masa decorations Shima da Wani farin yadi da kuma flowers sai tun tun sarauta da aka zagaye table d'in dashi inda k'awayen Aziza zasu zauna a gaban kowa kuma and'ora masa plate na snacks wanda k'awayen zasu ci .Wuri dai yayi kyau sosai sai kace wadda zatai parting graduation na university ba SSCE ba . Aziza ta k'arasa wajen friends d'in ta Wanda suka mik'e sai zuzuta kyan da tai suke Dan yawan cin suma 'ya'yan k'awayen Fulani Salamatu masu kud'i suma sai wasu class mate d'inta su biyu.aziza sai murmushi take ganin yadda ake ta cewa tayi kyau.Adai dai lokacin da Aziza ke tare da k'awayen ta su Huyaam suka shigo gidan bayan sun k'araso Aziza ta juyo tana kallansu take annurin fuskarta ya canza daga fara'a zuwa B'acin Rai ganin yadda HUYAAM tai kyau sai taji gabad'aya kamar Huyaam ta fita kyau duk da kwalliyar da tasha itama.amma saboda Aziza ta riga da sawa kanta cewa duk lokacin da HUYAAM tayi kwalliya to Gani take sai ta fita kyau . wannan abun data sawa kanta yasa ko tayi kyau take ganin kamar batai ba Koda ko Wani ne ya fad'a mata Gani take dole sai su Huyaam sun fita.take kuma ta kauda tunaninta ta k'araso wajensu tana murmushin yak'e tace... "Sannunku da zuwa ku k'araso mana". Ta fad'a tana murmushin yak'e suka ansa mata suka bi bayanta ta k'arasa inda k'awayenta ke Zaune kan tun tun nan suma duk suka samu waje suka zauna k'awayen Aziza sai kallan Huyaam suke suna Yaba kyau da nutsuwarta. Aziza ko sai cika take tana batsewa kamar Wani ne yasa tai parting.Babu Bat'a lokaci aka fara gabatar da partyn bayan sunci sun sa sai kuma akazo za'ayi pictures Karima ta kawowa Aziza gifts d'in nata Aziza ta karb'a ta nuwa k'awayenta da cewa a school aka Bata suka Karb'a suna tayata murna ko kunya Bata jiba .bayan sun gama Gani akai musu pictures d'in tare da Aziza sai da aka gama mata da friends d'in ta Sannan ta tafi wajensu Huyaam ta nuna musu gifts d'in tace .. "Kunga d'azu uncle Samuel Jackson ya kawo min wai mantawa akayi shiyasa alokacin da za'a Baku ni ba'a bani ba".ta fad'a ko kunyar k'aryar da tai bataji jiba Mamaki ya kamasu ikleema Amma basuyi magana ba tunda sun San halin Aziza zatai yafi hakama.suka karb'a duk suka Gani Suna tayata murna ta k'ira photographer da suka d'auko na musamman yazo yay musu pictures aka had'u harda k'awayen Wannan Karan ma akai musu su sai Kuma Aziza tace photographer yazo yay musu na iya su 'Yan Cikin palace d'in suka had'u su su biyar suka tsaya safna ta tsaya kusa da Aziza Amma sai Aziza ta tureta ta jawo Huyaam kusa da ita kamar abin arzik'i Hakan sai ya bawa safnah mamaki Amma batai Magana ba ta tsaya akusa da Huyaam ita aka fara d'aukar su pictures Aziza data lura hankalin kowa Baya kanta Yana wajen photographer nan kawai tasa k'afarta wacce ke d'auke da highheel shoe ta take k'afar Huyaam da shi Babu shiri Huyaam tasa Wani ihu tana k'ok'arin janye k'afar ta jin Wani azaba ya ratsa ta har tsakiyar kanta Huyaam zata Fad'i safnah Dake gefenta ta rik'ota cikin tashin hankali.take su Huda ta iyo kan Huyaam tana tambayar ta da lafiya Maiya sameta Amma Ina Huyaam sai kuka take tana rik'e da k'afar ta wacce sai zubar da jini take sosai tana K'iran sunan Ammie k'awayen Aziza duk suma hankalinsu ya tashi Ganin wannan jini safna ta Kalli Aziza Ganin yadda ta saki wani murmushi d'aukarta Babu Wanda ya lura da ita take safnah ta gane me yake faruwa wato Aziza ita ta take k'afar Huyaam kuma tana sane tunda gashi ko ajikinta bare tazo wajen da HUYAAM take tai mata sannu Babu Bat'a lokaci su Huda suka fita da Huyaam daga b'angaren su Aziza gabad'aya sukai b'angaren su da ita tana ta ihun K'iran sunan Ammie. Ganin amfita da Huyaam ga lokacin sallahn magrib yayi tunda gashi ana k'ok'arin shiga sallahn magrib a masallaci cikin masarauta yasa duk da k'awayen Aziza sukai Mata sallama suka tafi Aziza tai musu godiya nan suka tafi shima photographer da yake dama an sallame shi shima ya tafi itama Aziza ta shige cikin gidan tunda an gama mata pictures d'in tana kuma tsaron kada Mai martaba yazo ya samesu ba'a gama ba yasa a Zane ta gefe D'aya Kuma tana farin cikin abinda taiwa Huyaam...... Alokacin da aka shiga da HUYAAM b'angarensu tana tana ta ihun kuka saukowar ya Zarah kenan downstairs bayan ta idar da sallahn magrib a a d'akinta already Dama muneefa tana zaune itama afalon tai nata sallahn cikin tashin hankali ya Zarah ta k'araso cikin falon Tana kallan Huyaam Dake zunduma ihu tana K'iran sunan Ammie da tashiga uku ga hannun ta rik'e da k'afarta .idan ya Zarah ya sauka a kan k'afar Huyaam Dake zubar da jini har lokacin take hankalinta ya K'ara tashi ta k'arasa ta karb'e Huyaam daga rik'on da su Huda sukai mata ta rungumota zuwa jikinta ta Kalli Huda da damuwa tace. "Ayina taji wannan raunin". Safna tai saurin cewa. "Ya zarah Aziza ce ta taka ta kuma tana sane wallahi ". Cikin confused ya zarah tace. "Garin Yaya?..." nan safnah ta bawa a ya Zarah labarin abinda ta sani .tuni ran ya Zarah ya gama B'aci tace . "Yanzu Azizan ce taiwa Huyaam haka? Mai tai mata daza tai mata irin wanna zalincin haka ai".ta fad'a ranta a b'ace.jin haka yasa tuni muneefa ta haura Sama da gudu wajen Ammie zata fad'a mata. Ammie tana zaune kan sallayan idar da sallahn ta kenan taji kamar kukan Huyaam da Kuma K'iran sunanta da taji Huyaam nayi tana k'ok'arin tashi ta fita ta gano meke furuwa kenan Kuma saiga muneefa ta shigo d'akin tana haki tace cikin rawar murya kamar zatai kuka. "Ammie kizo ya Huyaam ta karye a k'afa k'afar sai zubar da jini take sosai"ta fad'a tana rushewa da gunjin kuka. Jin haka yasa Take gaban Ammie ya Fad'i Jin abinda muneefa ta fad'a tace . "Muje" ta fad'a cikin far gaba.muneefa ta juya ta fita daga d'akin Ammie ta biyo bayanta hankali a Tashe. Koda Ammie ta sauka ta tarar Huyaam na Jikin ya Zarah sai kuka take tana rik'e da k'afarta wacce jini ya gama wanke ta tass gashi har lokacin jinin Bai daina zuba ba ga su safnah sun zagaye ta sai sannu suke mata.cikin Tashin hankali Ammie ta k'arasa wurin da suke ta karb'i HUYAAM daga hannun ya zarah ta rik'o ta zuwa jikin kamar zatai kuka tace. "Meyasa sameta hakane?...".ta fad'a tana duba K'afar HUYAAM . Kafin kowa yay magana ya Zarah tai saurin fad'awa Ammie kamar yadda safnah ta fad'a mata.Ammie ta Kalli ya Zarah da mamakin abinda ta fad'a.muneeb ne ya shigo falon bakinsa d'auke da sallama dawowar sa Kenan daga masallaci da sauri ya k'araso har cikin falon Dan Ganin abinda ke faruwa Ammie ta kalleshi tace. " Yauwa muneeb ina haidar?..."muneeb yace. "Yana masallaci". Ammie tace . "Yi masa ka k'ira min shi yazo mu kai HUYAAM asibiti yanzu kai sauri".ta fad'a cikin damuwa.babu musu muneeb ya fita daga falon cikin sauri Dan K'iran ya haidar.babu Dad'ewa muneeb ya shigo falon sai Mai martaba Dake biye dashi sai Kuma ya haidar Yana takewa Mai martaba Baya Dan lockan da muneeb yaje zai fad'awa ya haidar alokacin Yana tare da Mai martaba kuma agaban Mai martaba muneeb ya fad'awa ya Haidar sak'on Ammie shine Mai martaba yace suzo su Gani tare. Gabad'aya su safnah sukai baya Ganin Mai martaba ya shigo falon suna ansa Musu sallamar da Sujay kafin su tsugunna har k'asa suka shiga gaida shi,Mai martaba ya ansa musu da kulawa ya tsaya akusa da Ammie Yana kallan ta yace cikin nutsuwa. "Meya sameta?... Kafin Ammie ta bashi ansa ya Zarah tai sauri cewa . "Abba Aziza ce ta takewa Huyaam k'afa da takalminta Kuma da sanin". ta fad'a cikin Jin haushin Abinda Aziza tai.Mai martaba ya juya Yana kallan ya Zarah yace. "Wani Irin takalmine haka da zai iya Huda mata k'afa"ya Zarah tace. "highheel ne Abba".Mai martaba yace . "Garin Yaya? Nan ya Zarah ta bashi labarin kamar yadda safnah ta Bata,ran Mai martaba ya gama B'aci tuni dama su ikleema sun bar falon ganin Mai martaba ya shigo ya kalli HUYAAM yace. "sannu mamana". sai Kuma ya kalli Ammie yace. "Kiyi hak'uri fulani zan d'auki mataki in Sha Allah". Ammie dai batai magana gyad'a masa kai kawai tai .Mai martaba ya Kalli ya haidar Wanda shima jikinsa yay sanyi yace. "Haidar ku kaita asibiti bari na koma masallaci".Yana fad'ar haka ya fita daga falon gabad'aya.yana fita Ammie ta Kalli ya Zarah tace cikin Damuwa. "Zarah Mai yasa zaki fad'a masa salon ki K'ara jawomin wani bakin Jini a wajen funali".ya Zarah tace. "Ammie idan ma Ba'a fad'a masa ba dole