Sashe 7
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fusace yace. "Ke bansani ba"Karaf a kunnan Huda wacce take k'ok'arin saukowa downstairs d'in tace . "lahh yaudai na ganku a Rana Ashe bani kad'ai ake hanawa wayarba harda ke"ta fad'a tana yiwa HUYAAM gwalo. Huyaam ta harareta sai Kuma ta kalli ya haidar ta k'ara marai raicecewa tace. "Ya haidar kagafa dariya take min fa?ta fad'a kamar zatai kuka..."ya haidar ya juya Yana yiwa Huda Wani kallo sai Kuma ya juya ya Mik'awa HUYAAM wayar yace. "Ungo"Huyaam ta karb'i wayar da sauri tana murmushi tace. "Thank you ya Haidar"sai kuma ta juya ta rama gwalan da Huda tai mata tace. "Indai nida ya haidar ne ya rinya bazaki tab'a Ganinin mu arana ba koh ya haidar?....". Ta fad'a tana kallan ya haidar Wanda Bai kalleta ba.baiyi magana ba gyad'a mata kai kawai yayi. Huda ta tura Baki gaba tace kamar zatai kuka. "Allah sarkie ni wato Dan Kunga Yaya baya nan shiyasa duk kuke min haka". Ta fad'a tana tura Baki gaba. Ya haidar ya juya Yana kallanta da mamakinta jin abinda ta fad'a. Ganin Irin kallon da ya haidar yake mata yasa Huda ta juya Dama a stairs ta tsaya ta koma zuwa d'akinsu .Huyaam da itama tabi Huda da kallo Jin abinda ta fad'a ta Kalli ya haidar tai k'asa da murya tace. "Yaya bari naje muyi tare kagafa taji haushi". ta fad'a cikin marai rai cewa.ya haidar yace. "Ke Babu inda zaki ta fashe ma ba haushi ba". Huyaam ta marai raice tace. "Dan Allah Yaya kayi hak'uri "ta fad'a kamar zatai kuka. yay shiru baiyi magana .tace . "Dan Allah ya haidar nanma dai baiyi magana ba Hakan yasa ta Gane ya amince ta mik'e da sauri tabi bayan Huda wacce har takai d'akinsu. ___________ Da yamma wajen k'arfe 4:30pm na yamma su Huyaam suka fito Daga part d'insu zasuje su gaida mutanan Dake cikin palace d'in gabad'aya Dan dama haka suke duk ranar Friday sai sunje sun gaida Matan Dake gidan ,kuma wannan ba tarbiyar kowa bace saita Ammie. Dukkansu sanci kwalliya cikin shigar less d'inkin doguwar riga Huda da Huyaam iri d'ayane nasu Dan komai nasu iri d'ayane, indai za'ai musu D'inki to iri D'aya ake musu ba'a tab'a ban banta musu.less d'in kalar green ratsin golding mayafin shima kalar kayan jikinsu.kalar nasu ya Zarah daban itada muneefa. B'angaren Dake jikin nasu suka fara zuwa wato bangaren uwar gidan mai Martaba Fulani Salamatu. Wanda Designed sin ginin da komai Irin na part d'insu ne komai Babu abinda ya ban banta.suna zuwa k'ofar part d'in sukai knocking kofar tare da sallama Abakinsu .Saida sukai knocking sau biyu sannan aka Bud'e musu k'ofar .haka suka shiga bakinsu d'auke da sallama. Sun tadda Aziza da K'annanta gabad'aya Zaune a falon Ramla ce kawai Batanan mummynsu ta aiketa part d'in su ikleema.dama su ukune ya'yan Fulani Salamatu Aziza itace Babbar 'yarta wacce take sa'arsu Huyaam sai Mai bi mata Ramla sai walida itace Autar Fulani Salamatu. Fulani Salamatu itace uwar gidan mai Martaba Allah ne Bai Bata haihuba da wuriba Saida aka auro Ammie ta haifi 'ya'ya uku sannan ita da Ammie suka samu cikin Aziza tare dasu Huda Wanda yanzu haka suna Shrekara 17 to 18 ne,Ramla kuma sa'ar muneeb ce sai walida kuma sa'ar muneefa.to daga nan kuma haihuwar saita tsaya musu duka su biyun.ita Fulani Salamatu Bata da d'a namiji ko D'aya.'ya'yanta duka matane. Tun kafin su k'araso cikin falon Aziza take kallansu bayama HUYAAM ganin Irin yadda tai kyau ba kad'an ba arayuwar Aziza ta tsani taga Wani yafita , Ina anata burin saidai tafi Wani ,saidai Kuma Hakan Bai yuba saboda gabad'aya 'ya'yan Ammei kyawawane .haka ta K'ara had'e Rai bayan Sun had'a Ido da Huyaam ta harareta sai Kuma ta juya tana kallon ya Zarah kamar wacce aka matsewa Baki tace. "sannunku da zuwa ya Zarah" ta fad'a tana sakin murmushin yak'e. Ya zarah tace Batare da ta kalleta ba. "yauwa, Ina mummy?..."sunan da 'ya'yan fulani Salamatu suke K'iranra dashi kenan. Aziza ta mik'e tace. "sallah takeyi bari nai mata magana".tana fad'ar haka ta nufi stairs tai hanyar d'akin Fulani Salamatu. suka k'arasa falon suka samu waje suka zauna waleeda ta k'arasa wajen su HUYAAM inda suke Zaune ita da Huda tana kallan Huyaam tace . Ya HUYAAM kinyi kyau Sosai". ta fad'a tana murmushi. HUYAAM ta Maida mata da Martanin murmushin tace . "Nagode sosai walida" Huda ta Kalli Walida tace . "Wato iya Huyaam kika gani ko Walida?..." Tafad'a tana yiwa walida Hararar Wasa . Walida ta rufe fuskarta da tafukan Hannunta tace. "A'a ya Huda kema kinyi kyau keda ya Zarah da muneefa".ta fad'a tana murmushi.huda ta d'auke kanta daga kallan ta. Aziza ce ta dawo falon tace . "Ya zarah mummyn Tana zuwa "ta fad'a tana zama kan kujerar data tashi.bahu dad'ewa Fulani Salamatu ta sauka k'asa sanye da jihab alamar dai da Gaske sallahn tai ba fad'ar Aziza bace . Fulani Salamatu ta sauko tana kallansu har ta k'araso cikin falon ta zauna kan kujera one seater cikin tak'ama Fuskarta Babu yabo babu fallasa. Tare suka gaida ta tana kallansu ta ansa kadaran mahadan. daga nan Bata k'ara cewa komai ba suma sukai shiru inda sabo sun Saba idan sukazo b'angaren fulani Salamatu tai banza ta k'yalesu Dan Suma ba'a San ransu suke zuwa b'angaren ba tunda suma sun San ba k'aunar take ba bayama HUYAAM Dan ita har Bataso ace yau Friday Dan kada ace suzo part d'in d'in falani salamatu saboda ita Kanta tasan ba k'aunar ta take ba daga ita har 'yarta Aziza.haka kowa yay shiru a falon sunkai kusan 2 minutes ahaka Babu Wanda ya K'ara magana.sai can fulani Salamatu ta kalli Aziza tace . "Aziza kawo musu mana". Ya fad'a tana kallan Aziza. ya zarah ta mik'e tace . "A'a mommy munsha ruwa a gida tafiya ma zamauyi" ganin haka yasa suma su Huyaam duk suka mik'e Wanda kamar suna kan k'aya .fulani Salamatu tace. "Tafiya Kuma? To nagode ku gaida gida"daga haka Bata k'ara cewa komai ba.walida tace. "ya HUYAAM ya Zarah,ya Huda muneefa bye bye" ta fad'a tana murmushi.suka ansa mata suna Fita daga falon . Suna fita Aziza ta mik'e tana kallan walida tace. "Kedai wallahi ba akwai marar zuciya ba banza kawai suna Wani shash shareki Amma kina Wani cusa kai". Ta fad'a tana hararar walida kamar idanuwanta zasu zazzago k'asa Saboda masifa. Walida ta tura Baki gaba tace . "Kai ya Aziza Mai nai kuma?..."ta fad'a tana juya kanta gefe. Aziza da haushi ya gama cikata idan ta tuno da yadda gabad'aya su Huyaam sukai mugun Kyau tace . "Ni kike fad'awa me kikayi Dan Bakida mutunci eh!!..."ta fad'a kamar zata doki Waleeda. walida tai saurin Matsawa baya tana tura Baki gaba ganin Aziza zata doketa. Bak'in ciki yasa Aziza tai k'wafa ta bar wajen ta haye sama zuwa d'akinsu tana ta masifa ita kad'ai .itadai Fulani Salamatu batai magana tabi Aziza da kallo kafin ta tab'e Baki itama ta mik'e ta wuce zuwa d'akinta tana Jin Wani Irin tsanar yaran na yad'uwa azuciyarta barin ma babban yayansu ta tsaneshi shida HUYAAM tsana mafi Muni ma kuwa. 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *Paid book *Free pages* *NA* *___(MRS SARAKIES ___* *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 6 ___________ Daga b'angaren fulani Salamatu ,b'angaren Dake yamma da part d'insu suka nufa wato b'angaren sauran matan Dake gidan. b'angaren farko na baba turaki ne wato k'anin Mai martaba shima dai matansa biyu Kuma ko Wacce bangaren ta daban. part d'in farko shine na uwar gidansa Mai suna Hajiya Lubabatu . Hajiya Lubabatu 'ya'yanta s hida hud'u mata biyu maza .acikin matan biyun farko sune manya bahijja wacce a shekaru zatai 25 itace babba sai Mai bi mata Salima ita Kuma shekararta 22 itace sa'ar ya Zarah sai ikleema wacce itace sa'ar su Huyaam Mai shekaru 17 sai maza biyu Sai kuma autarsu Ameera . Tunda suka baro part d'insu Aziza gaban HUYAAM fad'uwa kawai yake har suka k'araso part d'in kwata kwata Bata son zuwa b'angaren nan guda biyu.wato b'angaren su Aziza da b'angaren su ikleema saboda duk gidan babu Wanda yake k'aunarta musamman ma wad'annan matan guda biyu wato fulani Salamatu da Hajiya Lubabatu wato babarsu ikleema ,Basa k'aunar HUYAAM ko kad'an iya mamansu safna ce kawai take Santa sai kishiyar hajiya Lubabatu wato antynsu su ikleema, ita Irin matan nan ne Irin 'yan I don't care d'in nan ce, ita baka Gane inda ta dosa shiyasa kwata kwata babu part d'in da HUYAAM take zuwa ta zauna ta sake sainasu safnah. Suka isa part d'in Saida sukai knocking bayan an Basu iznin shiga sannan suka shiga. sun tadda ikleema dasu ya bahijja wacce take zauna kan kujera tana danna wayarta, ita kan ma ansa musu ranar AURE itada yayarsu safnah Mai suna zulaihat nan da 2 month ne bikin nasu idan Allah ya kaimu Dan an kawo kud'i anyi komai kawo legefe ne kawai ya rage yanzu.sai K'annan ikleema mazan sai autarsu Ameera.suna zaune a falon suna kallo . ikleema ta mik'e da murmushi a fuskarta ganin su Huyaam tana kallansu ta ce. "sannunku da zuwa ya Zarah" .ta fad'a tana murmushi Ya zarah ta ansa mata suka k'arasa har cikin falon suka zauna na kan kujera suna gaida ya bahijja ta ansa musu tana barin falon da wayarta a hannunta ikleema tace. "Bari na k'ira mama tana d'aki"daga haka tabar falon .Babu dad'ewa ikleema suka dawo falon tare da Hajiya Lubabatu cikin shiga ta Alfarma sai wal walwali take ta k'araso har cikin falon ta zauna a nan kan kujera tana kallansu . Gabad'aya Suka had'a Baki wajen gaidata.ta ansa musu tana murmushin da Bai kai zuciyarta ba .kafin kice me ikleema ta kawo musu ruwa da drink's ta ajiye agabansu tana kallansu tace. "kusa ruwa ya Zarah tana fad'ar haka ta koma kan kujerar da take Zaune ta zauna. Nan ma dai shiru falon yayi sai ikleema ma ce kawai da take Jan su Huyaam da hira,sukan bama Wani sakewa sukai ba kawai dai suna Zauna ne .Basu Dad'e a falon ba, Dan babu Abinda suka tab'a na D'aya daga cikin abinda aka kawo musun suka mik'e sukace tafiya zasuyi.hajiya Lubabatu tana kallansu tace . "Tafiya kuma zakuyi Zarah?...."ta fad'a tana kallan