← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 85

Sashe 11

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Afeef ya sauka akan wasu dogayen riguna guda biyu Wanda suka kasance Iri D'aya sak kalar pitch color nan yasa aka d'auko masa su Dan Yana tunanin zasu yiwa HUYAAM da Huda babu musu aka d'auko aka Mik'a masa aikuwa Yana duba size d'in sai yaga zasu musu nan ya Mik'awa worker d'in shikuma yasa cikin trolling shikuma yay gaba Saida ya d'aukowa su Huyaam dogayen riguna guda hur hud'u duk masu bala'in kyau da tsada sannan kuma ya d'aukawa ya Zarah da muneefa,sai ya'yan Fulani Salamatu suma duk ya d'auka musu kai D'aya suda 'ya'yan baba turaki su ikleema dukansu Suma sai Kuma 'ya'yan baba wambai su safnah dukansu Suma gabad'aya haka ya siya musu babu abinda ya ban banta dan haka yake baya tab'a siyawa K'annensa Abu Bai siyawa duka Yaran gidan ba. Daga wajen dogayen riguna Kuma sai ya wuce wajen kayan maza nan ya d'aukar su muneeb da duka Sauran yaran gidan Maza bayan ya gama dasu sannan ya wuce wajen hands bag da takalma nan ya siyawa su Huyaam masu bala'in kyau da tsada ko Wacce biyu biyu sai Kuma ya wuce wajen jewelleris nan ma ya d'ibar musu daham gabad'ayansu sai kuma ya d'aukowa su Ammie gold ko Wacce biyu biyu masu bala'in kyau d a tsada daga k'arshe yasa sauran ma'aikatan suka Taya wannan worker d'in na farko suka tayashi d'aukar kayan saboda yawan su daga nan Kuma sukai wajen payments akai counting din kud'in gabad'aya aka fad'a masa babu Wani musu haka ya Mik'a musu card d'insa suka cire kud'in suka Mika masa ya karb'a ya fita waje wajen mota ma'aikatan suka biyo shi da kayan Nik'i Nik'i tunda driver ya hangoshi ya fito ya Bud'e musu boots d'in haka suka zube kayan gabad'aya aciki Bayan sun gama Afeef ya biya sannu ya shiga back seat Wanda driver ya Bud'e masa ya shiga daga nan Basu zarce ko Ina ba sai gida...... 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *paid book *Free pages* *NA* *___(MRS SARAKIES )__* *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 9 ____________ Sai da su Huyaam sukai kwana biyar cif basuje school ba saboda Interval d'in exam da Suke dashi.basa zuwa ko Ina sai dai suyi karatu da yamma Kuma su tafi islamiya....Ranar Sunday da safe Huyaam tana kwance saman gado tana bacci har wajen k'arfe 11 :20am Bata tashi ba ta baje akan gadon ga gashin kanta yadda ya bar baje nan saman pillow sai sharar bacci take abinta.bud'e k'ofar d'akin akayi Huda ce ta shigo shigowarta na ukune kenan tana zuwa tana duba taga ko Huyaam ta tashi?, Amma sai dai ta tadda Bata tashi ba. yanzunma Ammie ce ta aikota akan lallai ta taso Huyaam ko Bata tashi ba, shine yasa tazo ta. Tsayawa tai kawai Daga nan Bakin k'ofar tana kallan Huyaam da mamakin yadda take sharar baccinta hankalinta kwance ,Huda ta sauke numfashi ta k'arasa shigowa har cikin d'akin zuwa gaban gadon ta kai hannu ta yaye blanket d'in da HUYAAM ta rufa dashi har saman kanta tana Kuma K'iran sunanta at the same time. Cikin bacci Huyaam taji muryar Huda tana K'iran sunan ta, nan ta Bud'e idonta kad'an Wanda suke cike da bacci tana kallan Huda dasu .Huda tana rik'e da bargon a hannunta har lokacin tace . "Kike Kallona? ki tashi baccin ai ya isa haka koh?..." ta fad'a tana Jan blanket d'in. HUYAAM ta had'e Rai ta damk'e blanket d'in da k'arfi ganin Huda na Neman yaye mata shi tace cikin shak'akk'iyar murya Irin ta Wanda bacci Bai ishe ishe Shiba. "Banaso Huda miye Hakan? banaso ki K'yaleni". ta fad'a tana tura Baki gaba. Huda tai murmushi ta k'ara Jan bargon da k'arfi tana cewa. "Wallahi sai kin tashi Ammie ce tace nazo na taso ki ai,baccin ya isa haka sai kace Mai baccin mutuwa"ta fad'a tana k'ok'arin fusge bargon daga rik'on da HUYAAM tai masa . Ganin haka yasa Huyaam ta yunk'ura da sauri ta mik'e Zaune itama ta fara jan bargon nanfa suka fara jaye jayen bargo da ko kawa. ganin da Gaske fa Huda take saita janye bargon yasa Huyaam Tai kanta da sauri cikin b'acin Rai tana yiwa Huda magana. Ganin haka yasa Huda ta saki bargon da sauri ta nufi k'ofar fita daga d'akin da gudu tana K'iran sunan Ammie .. Huyaam tai murmushi Jin abinda Huda keyi ta Maida bargon nan saman gadon sannan ta wuce toilet Dan yin brush da Kuma wanka. Sai k'arfe Sha biyu Saura Huyaam ta fito daga d'aki,ta sauko downstairs nan main falorn gidan cikin shigar atamfa D'inkin doguwar riga A shape wacce tai mata bala'in kyau sai Wani walwali take acikinta saboda d'inkin da aka zubawa rigar. haka tafito sauko daga stairs d'in.Babu kowa a falon daga Huda sai muneefa ne kawai a falon suna zazzaune kan kujera suna kallo a TV kamar ance muneefa ta juya sukai ido hud'u da Huyaam wacce ke shigowa falon cikin sand'a zatai wajen da Huda take. muneefa ta Bud'e Baki zatai wa HUYAAM magana Huyaam tai saurin d'aura Hannunta saman Bakinta tana kallan muneefa alamar kada tai magana . muneefa ta koma ta zauna a hankali Dan kada Huda ta ganta tana gimtse dariyarta Dan tasan mai Huyaam take nufi tunda sun Saba. Huyaam ta sauke numfashi a hankali ta fara takowa cikin sand'a har zuwa wajen da Huda ke zaune wacce tai backing d'inta ta Bata Baya tana zuwa tai saurin rufe mata fuskarta da tafukan Hannunta ta baya Huda.me muneefa zatai inba dariya ba nan ta saki dariyar da tai ta rik'ewa.itako Huda batai mamakin waye ba tunda ga k'amshin turaran HUYAAM nan tana shak'a nan ta Gane itace. Ta rik'e hannun Huyaam wacce ta rufe mata fuskarta K'am tak'i saki, Huda ta Bud'e Baki tace . "Huyaam miye haka ki cire Hannunki daga fuskata banaso"ta fad'a tana k'ok'arin cire Hannun HUYAAM daga fuskar tata.nan Huyaam tak'i saki saima K'ara damk'e fuskar Huda da tai, nan fa Huda ta fara k'ok'arin k'wace fuskarta Amma ta kasa ita Kuma HUYAAM sai murmushi take can Huda ta kai hannunta zata kamo rigar HUYAAM,tuni HUYAAM ta saketa tai baya da sauri Huda ta Mik'e zatai kan Huyaam tuni HUYAAM ta haye stairs tai d'akin Ammie da sauri har tana had'awa da gudu tana yiwa Huda dariya.Huda tai k'wafa ta koma ta zauna tana murtsuke idonta. Ammie na zaune bakin gadonta tana gyara wasu kayanta HUYAAM tai knocking k'ofar Had'i da turawa ta shigo tare da sallama a bakinta. Ammie ta d'ago tana kallanta ta ansa mata sallamarta. Huyaam ta k'araso d'akin tana sauke numfashi tana Kuma murmushi Had'i da juya banyanta tana tunanin ko Huda ta biyo bayan ta. Ammie tana kallan Huyaam da mamaki tace . "A'a keda waye Kuma? Kika shigo kina haki?...."ta fad'a tana kallan bayan Huyaam ko zataga me Huyaam d'in takewa waigen oho. Huyaam ta sauke numfashi tace. "Babu kowa fa Ammie". Ammie ta sauke numfashi tace. "keda Huda ne ko?..." Huyaam tai murmushi batace komai ba nan Ammie ta Gane itada da Huda ne k'ila abinda suka Saba sukayi wato tsokanar juna. Ammie tana kallan Huyaam tace. "Yanzu kika tashi daga baccin ko?...." Huyaam tai shiru tana shafa kanta . Ammie tace . "Wallahi Huyaam idan Baki daina Irin wannan baccin ba Agidan nan ki kai har wannan lokacin Baki tashi ba zansa k'afar Wando D'aya nida ke agidan nan,sai kinje ulcer ta kama ki kizo kina ciwo ciwo Allah ma ya kiyaye". Ammie ta fad'a tana kallan HUYAAM. Huyaam ta sauke idonta k'asa tana sauraran Ammie. Ammie tace . "Kinji ko Baki jiba?..."Huyaam ta d'ago kanta tana kallan Ammie da raunan nin idanuwanta Dan arayuwarta bata so taga Ammie cikin damuwa.a hankali ta k'araso kusa da Ammie ta rungumeta tace cikin sanyin murya. "Kiyi hak'uri Ammie bazan K'ara ba"ta fad'a tana K'ara shigewa jikin Ammie. Ammie tai murmushi tana shafa kan Huyaam Dan itama dolene take sawa taiwa Huyaam fad'a badan komai ba sai Dan ta gyara abinda take tunda ita macece duk mun daran dad'ewa ba'a gidan zata dauwama ba gidan Wani zata.Ammie ta sauke numfashi tace. "Naji na hak'ura. but dear kinsan banason duk abinda zai B'ata Miki Rai ko? So please ki kiyaye, ni tsorona kada ki dinga zama da yunwa har Wata cutar ta kama ki". Ta fad'a tana Shafa kan Huyaam. HUYAAM ta gyad'a mata kai tace a shagwab'e. "In Sha Allah Ammie kema kin hak'ura ko?.."Ammie ta d'agota tana kallan fuskar ta da Murmushi tace . "Na hak'ura dear dama bakimun Komai ba karki damu kinji?..." Huyaam tace "Thank u lovely mother".ta fad'a tana murmushi. Ammie itama murmushin tai ta rik'e fuskar HUYAAM da tafukan Hannunta tana kallanta tace . "Nevermind lovely daughter"ta fad'a tana fad'ad'a murmushinta .Huyaam tai murmushi tai kissing Ammie a Kumatu. Ammie ta shafa fuskarta tace. "Thanks dear fatan kinci abincin dai koh?..." Huyaam ta girgiza mata kai tace cikin k'asa da murya. "Yanzu zanje naci". Ammie ta kalli Wani Dan k'areren agogon bangon Dake d'akinta sai Kuma ta juya tana kallon Huyaam tace. " past 12 fa Huyaam, Amma kike zaune Bakije kinci abinci ba? oya wuce kije kici".ta fad'a tana nuna mata hanyar k'ofa.Babu musu HUYAAM ta juya ta fita daga d'akin bayan ta kullowa Ammie k'ofar. " LAmmie ta sauke numfashi tana girgiza kai tare da cigaba da abinda takeyi. Huyaam tana sauka k'asa tun kafin ta k'araso sukai ido hud'u da Huda wacce take Harararta. Ganin haka yasa Huyaam ta sauko downstairs d'in a hankali tana Murmushi ta had'a hannayenta biyu alamar roko tace. "Dan Allah kiyi hakuri lovely twin". Ta fad'a tana murmushi. Huda ta d'auke kai kafin tace . "Sorry for your self Yarinya ,Dan bazan tab'a hak'ura ba sai na rama ,Kuma karkiyi tunanin ma yanzu zan rama,Dan idan zan rama ma ai ba yanza ba sai kin sakan kance kamar yadda Nima kikai min". tana fad'ar haka ta Maida hankalinta kan TV ta cigaba da kallonta. Huyaam tai murmushi ta k'arasa dining d'in cikin sand'a ta zauna kan kujera har lokacin a tsorace take da Huda Dan Gani take a kowani lokaci Huda zata iya tasowa kanta .ta bubbud'e warmers d'in tana k'ok'arin d'ibar Abinda zata iya ci... _____________ Washe gari Monday Huyaam basuda paper sai washe
Chapter 11 · 0% Book details