← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 85

Sashe 38

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ubangiji ya Bata lafiya har yau mudai bazamu gushe ba muna nan mun duk'ufa a kan addu'a da iznin Allah yaya gimbiya zata warke Allah zai tashi kafad'unta Hajiya inna in Sha Allah". Hajiya inna ta rausayar da kai tana tab'e Baki tace. "Ameen Allah yasa Amina ai mu haka mukeso Dan so nake mu koma Egypt d'in nan ma kwana nan Dan baza mu gaji ba" anty Amina tace. "Nima dai da Hakan nace ko Allah zaisa wata Rana a dace"? Hajiya inna tace. " sosai kuwa dan komai sai anayi ana Raba k'afa". Anty Amina tai murmushi tace. "To Allah dai yasa mudace" . Hajiya inna akace . "Ameen dai". knocking d'in k'ofar d'akin akayi Hajiya inna ta Kalli k'ofar kafin tace. "waye Kuma? sultan ne ya shigo cikin shigar shadda fara k'al Wacce tai masa bala'in kyau sai Wani k'amshi yakeyi gashin kannan nasa ya kwanta luf luf akansa . Hajiya inna ta bishi da kallo harya k'arasa shigowa d'akin ganin yadda yayi sallama k'asa k'asa gaida Hajiya inna yayi da anty Amina batare daya Kalli D'aya daga cikin su ba.duk suka ansa masa da kulawa.suna kallansa har lokacin. duk'awa yayi bakin gadon dai dai saitin kan gimbiya Aysha ya kamo hannunta ta kalleshi da kumburun idanuwanta ya sumnaci hannunta idansa Yana kan ta yace cikin yanayin muryarsa. "Mami Ina kwana ya jiki Allah ya K'ara lafiya" haka duk ya jero mata wannan gaisuwar. lumshe idonta tai sai Kuma ta Bud'e lokaci D'aya tana kallansa. Mik'ewa yayi anty Amina na kallansa tace. "Kayi breakfast d'in ne sultan?. batareda ya kallate ba ya gyad'a mata kai". Anty Amina Bata damu ba Dan Bai ansa mata ba tace. "Yanzu Kuma ina zaka?." Nan ma Bai jiyo ba yace. "School". Atak'aice. Hajiya inna ta zaro ido tana kallansa Jin abinda yace tace tana kallansa da mamaki. "Makaranta Kuma sultan? Wani Irin makaranta kaida baka da lafiya ko ka manta yadda aka dawo da kai gidannan shekaranjiya ne?...".ta fad'a tana sare ido.Batareda da ya juyo ba yay hanyar k'ofar fita daga d'akin yace. "Ni Babu wata jinya danai". Yana fad'ar haka ya Bud'e k'ofar ya fita daga d'akin.hajiya inna ta mik'e tsaye tana kallan anty Amina tace. "Kinji abinda yace ba? nifa Ina tsoron wannan al'amari Irin na sultan Abu kamar sihiri yau lafiya gobe Kuma akasin haka ,yo miye ma ai dama Shima sihirin ne akai masa". Sai Kuma ta d'aga hannayenta sama tace. "Allah mun gode Maka Allah mun tuba idan Wani babban Laifi muka aikata Allah ka yafe mana idan kuma Wani ne yake nufar wad'an nan Bayin naka da sharri ya Allah ka Mai da masa ya koma kansa". Ta fad'a tana Shafa addu'ar jiki a Sanyaye. Sai kuma ta kalli anty Amina tace. "Amina kina fa jin abinda yace wai a hakan zaije makaranta salon yau d'inma yaje adawomana dashi rai a hannun Allah kamar ranar, gaskiya bazan bari ya tafi ba zuwa Zanyi na fad'awa Abdallah ya hanashi tafiya danni tun ba yanzu ba nake tsoron fitar sultan daga cikin masarautar nan". Ta fad'a cikin damuwa. Anty Amina ta sauke numfashi tana kallan Hajiya inna tai k'asa da murya tace. "Tunda kika ji yace shi baiyi jinyar ba Inaga Babu abinda yaje ji ayanzu kawai kiyi hak'uri mu k'yaleshi tunda Yanzu mun samu lafiyar ta fara samuwa sai mu godewa Allah,barema ai ba shi kad'ai yake tafiya ba akwai masu masa rakiyar". Hajiya inna tace. "A'a ke yarinya ce Amina Baza ki gane bane bakisan Irin wannan ciwon yadda yake ba dole sai anayi ana kula da taka tsan tsan dashi Dan Koda yaushe yakan iya tashin masa bari dai naje kawai". Daga haka ta nufi k'ofar fita daga d'akin .anty Amina ta bita da kallo tana girgiza kai dan tasan indai sultan ne ba lallai ya hanuba sai dai idan Mai martaba ne da Kansa yay Masa magana tukunna.... ____________ *Masarutar Kano* Afeef ne zaune k'asan carfet a babban falon Mai martaba kansa a k'asa ya tank'washe K'afarsa yana sauraran abinda Mai martaba yake fad'a masa harya Kai k'arshen zancen na sa.Afeef ya gyara zaman sa yace cikin nutsuwa. "Eh Abba Babu damuwa Allah Ya kaimu ranar Monday d'in zanje in Sha Allah". Mai martaba ya Sauke numfashi yace."yauwa! am sannan ba komai ne yasa zan tura ka Lagos d'in ba sai Dan inaso ne kaje ka Gano min yadda suke tafiyar da harkokin nasu Duk da nasan Babu wata matsala suna aikinsu yadda ya kamata domin babu abinda lamid'o bayayi dama sauran ma'aikatan.Amma Kuma Muhammad komai sai anayi Ana samun sabbin abubuwan cigaba". Afeef yace. "Hakane rankai Dad'e kuma in Sha Allah zanje d'in". Mai martaba ya cigaba Yace. Sai Kuma zancen school d'in su Huyaam dama inaso muyi magana da kai wacce school kake ganin ya kamata akaisu ne dan da a San samu nane inasone akaisu k'asar waje idan results d'in nasu ya fito Amma kai ya kake ganin za'ayi?". Afeef yay shuri Yana Jin abinda Mai martaba yake fad'a sai Kuma can yay k'asa da murya cikin girmamawa yace. "Ai Abba duk yadda kace ayi haka za'a Yi". Mai martaba yace "A'a ni Ina tambayar taka shawarar ne amatsayinka na babban yayansu". Ya fad'a Yana kallan yanayin Afeef. Afeef ya K'ara gyara zaman sa yace. "Abba ni atawa shawarar kawai da a barsu a Nigeria kamar yadda su Zarah sukeyi sai Yafi ni bazanso akaisu out side of the Nigeria karatu ba, tunda akwai masu rawar kai acikinsu Amma agafarceni idan ban Fad'i dai dai ba".Afeef ya fad'a Yana K'ara duk'ar da kansa k'asa.Mai martaba yay shiru na Wani lokaci sai Kuma can yace. "Bakai laifi ba dama shawara na nema a wurinka Kuma naji opinion d'inka akan hakan so Nima abinda nai tunani kenan, but Any way dai bari mu jira har results d'in ya fito sai Muji Ina ya kamata akai sun". Afeef yace. "Hakanma yayi Allah ya taimakeka". Mai martaba yace "yauwa! Nace yaushe ne hutun naka zai k'are?.. Afeef yace. "Saura sati biyu Rankai Dad'e". Mai martaba yace. "Ok! da sauran kwanaki kenan har ka gama duk ayyukan Dana Saka kama". Afeef yace. "Eh in Sha Allah" Mai martaba yace. "Daga nan kuma sai bikin su zulaihat zakazo ko?..." Afeef yace. "Eh! In Sha Allah". Mai martaba yace "Shikenan Allah ya Taimaka". sai kuma ya cigaba Yace "sai Abu na k'arshe tunda sun gama school har suna shirin shiga jami'a Mai zai Hana a Siya musu phones before dai su shiga jami'ar ya kamata ace an siya musu waya koh ya ka Gani?. Afeef yay murmushi Jin abinda Mai martaba ya fad'a wai Asiya musu waya shifa har yanzu gabad'ayansu kallan marasa hankali yake yiwa su Huyaam yaran da har yanzu basu gama sanin ciwon kansu ba Amma ace a Wani siya musu waya". Mai martaba yace. "Ya kake murmushi Muhammad ko Bai yi bane ba?" Afeef na kallan Mai martaba yace. "A'a Abba yayi yaushe za'a siya musun?" Mai martaba yace. ."ko yaushe ma before dai ka koma". Afeef yace. "To rankai Dad'e in Sha Allah gobe zan fita zai na taho musu da ita". Mai martaba yace. "Shikenan Allah yasa". Afeef ya ansa da Ameen". Sai Kuma suka koma tattaunawa akan kamannin Mai martaba take can Ingiland da tsare tsaren da zasuyi sai wajen k'arfe shabiyu sannan Afeef yayi WA Mai martaba sallama ya fita daga falon gabad'aya....... HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF *mutanan MRS SARAKIES Kuna Ina ne? ana ta payments na book d'in Huyaam ku an barku a Baya to Maza ku garzayo yanzu kar wannan garab'asar ta wuce ku*. *ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar Zenith bank Evidence of payment (shaidar biya )via 07066508376 Domun yin magana Da marubuciyar Kai tsaye 07066508376 only chart Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku mutanan arziki. 07066598376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* PAGE 2 *TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!* *Ina kuke manyan mata masu capacity ? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."* *To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* *1,Atamfofi* *2, lesses* *3, Abaya* *4, kayan kwalliya ko Wani iri ne* 5,*D 'an kunnaye(jiwelleries)* *6,takalma* *7,hand bag* *8, mayafai* *9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*. *domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka +234 811 190 1302 /09020337676* *Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta* *Sai mun Jiku
Chapter 38 · 0% Book details