← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 85

Sashe 23

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

05:50pm Dawarsa kenan daga wajen aiki ko zama baiyi ba bare ya huta Yana shiga d'akin ya ajiye brave case d'insa wacce ke d'auke da laptop d'inshi ya zare agogon hannunsa sannan ya fara rage kayan jikinsa. bayan ya gama ya k'arasa cikin toilet d'in ya shiga Dan yin wanka.babu dad'ewa ya fito d'aure da towel a k'ugunsa kansa sai d'igar ruwa yakeyi hannunsa kuma rik'e da k'aramin towel Daya d'aura akansa Yana tsane gashinta kansa dashi shaf shaf yake shirinsa nasa saboda tafiya ce dashi zuwa k'asar china nan da awa biyu jirgin nasu zai tashi wato k'arfe 8 na dare.so yake aya Dad'e acan yayi one to two days Dan a San samunsa yanaso ya tafi Nigeria ne a ranar Friday or Saturday a San samunsa fa kenan idan har ya gama abinda ya kaishi akan lokaci kenan. Amma ita tafiya itace da kai ba Kaine da itaba sai yadda ta yiyuwa tukunna.sauke numfashi yayi ya Ajiye towel d'in hannunsa yayi ya k'arasa gaban mirror Dake shak'e da kayan shafe shafe sai kace mace saboda Afeef Dan Gayu ne na ajin k'arshe Yana da tsafta ta kin K'arawa ga baya San k'azanta ko kad'an komai nasa na musamman ne shiyasa zakiga baya tab'a shiri da k'azami bare ya zauna kusa da shi ma .bayan ya gama tsane kan nashi ya ajiye towel d'in nan inda yiwa Ajiyewa sannan ya d'auki Wani lotion mai kyau da dad'in k'amshi ya fara shafawa ajikinsa bayan ya gama ya k'arasa wajen drowersa ya Bud'e Dan d'auko kayan da zaisa .wasu K'ana nun kaya ya d'auko ya ajiye agefe dan su zaisa idan zai tafi sannan ya d'auko gogeggiyar jallabiyarsa ash color yasa ajikinsa dama already yayi alwalarsa kafin ya fito daga toilet d'in ya d'auki turarukansa masu k'amshi ya feshe duka jikinsa dasu bayan ya gama ya maida ya ajiye sannan ya nufi k'ofar fita daga falon ganin lokacin sallah na k'ok'arin wucewa ya nufi wani masallaci Wanda ke a jikin gidansu K'arfe bakwai da Rabi ya fito daga masallacin bayan ya Zauna anyi sallahn isha'i dashi ya shigo falon ya k'arasa har d'akinsa sannan ya zare jallabiyar jikinsa ya d'auki wannan kayan Daya d'auko d'azu yasa ya k'arasa gaban mirror Yana fesa turare Aduka Jikinsa bayan ya gama ya d'auki pacing cap dinsa yasa. ya Allah haka na ambata araina ba k'aramin kyau kayan sukai masa ba ya k'arasa ya d'auki box d'insa Daya had'a kayansa aciki tunda Safe Wanda kafin ya fita aikin ya had'a kayan nasa ya d'auka ya kai falo ya ajiye sannan ya dawo d'akin ya kashe duka kayan wutar d'akin harda switch d'in sannan ya rufo k'ofar bayan ya danna Wani D'an Abu take k'ofar ta rufe Yana shigowa falon adai dai lokacin da driversa yake shigowa shima ya k'arasa ya d'auki box d'in Yana kallan Afeef ya sunkuyar da kansa kasa yace cikin girmamawa. "good evening sir". Batare da Afeef kalleshi ba Yana kallan disigner watch d'in hannunsa Yana kallan time yace. "Let's go".ya fad'a Yana nufar k'ofar fita daga falon cikin sauri ganin k'arfe 8 Saura.driver Mai suna John ya d'auki box d'in yabi bayan Afeef da sauri ,kafin Afeef ya k'arasa wajen motar har John ya k'arasa ya Bud'e masa back seat da sauri sannan ya tafi ya zaga ya Bud'e boots d'in motar ya ajiye box d'in aciki ya rufe Afeef kuma Daya tsaya Yana magana da ma'aikatan gidan ya k'araso Motar da sauri ya shiga bayan motar yana picking call d'in Daya shigo wayarsa Yanzu. John ya zaga driver seat cikin sauri ya shiga ya ta-da motar suka bar gidan bayan Mai gadi ya wangale musu gate d'in suka dinga d'aga musu hannu har suka bar gidan gabad'aya. K'arfe 8 Saura mintuna biyar motarsu ta Isa air port. John ya fito cikin sauri ya bud'ewa Afeef bayan motar ya koma baya da sauri ya tsaya Yana duk'ar da kansa k'asa.Afeef ya fito cikin nutsuwa yana k'arewa harabar air port d'in kallo ganin har anfara boarding classes John ya zaga boots ya Bud'e ya fito da box d'in yabi bayan Afeef da ita Wanda har yay gaba zuwa cikin air port Afeef ya juyo ya karb'i box d'in a Hannun John Yana kallansa yace. "Thanks". John yay murmushi yace. "Safe trip sir". Afeef ya gyad'a masa kai kafin yay gaba.john ya koma inda motar take ya shiga yay reverse ya fita daga airport d'in ya koma gida ... k'arfe 8 da Minti goma jirginsu Afeef ya d'aga zuwa kasar china... HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __* *__(MRS SARAKIES )__* *PAGE 1 *Tallah! Tallah!! Tallah!!!* *Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke *Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka *Atamfofi da lesses* *Abaya* *Shadda* *Hand bag* *Shoe* *Veil na manya Dana Yara* *Socks rin hands made d'in nan masu net*. *Hula ta 'yan Gayu* *Siyan D'aya ko sari* *Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki* *Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka* 08135305790 *Sai mun jiku *Bismillahirrahmanirrahim* ____________ Washe gari Ranar Alhamis da yamma Ya zarah tana zauna a falon downstairs bayan sallahn ASR tunda yau Babu islamiya tana karatun test d'in da zasuyi ranar Monday. huyaam Kuma tana zauna daga gefenta a saman kujera tana game da wayar ya Zarah data bata aro tayi nisa cikin yin game d'in da take Huda ta shigo falon da sauri rik'e da wayar Ammie Tayo wajen HUYAAM da ita ta karawa Huyaam wayar a kunnenta,Huyaam ta d'ago ta kalleta da alamar tambaya sai Kuma tai k'asa da murya tace. "waye?.." Huda tai k'asa da murya tace. "Anty Khadija ce zatai miki ya jiki".take Huyaam ta saki murmushi ta ajiye wayar ya Zarah nan gefenta cikin D'oki ta rik'e wayar Ammie tace. "Hello Anty Ina yini".ta fad'a tana K'ara fad'ad'a murmushinta.daga D'aya b'angaren Anty khadija Dake zaune a tamgamemen falonta Dake nan garin Abuja tace itama tana sakin murmushi. "Lafiya lau Huyaam ya gida ya jiki Kuma Ashe abinda ya faru kenan?... Huyaam tace. "Eh Alhamdulillah anty". Anty Khadija tace . "Allah ya sawak'e fatan dai yanzu k'afar ta warke ko". Huyaam ta Kalli k'afarta wacce har bandage d'in ya cire jiya da daddare da tana bacci kawai sai tashi tai taga babu komai sai tabon ciwon kuma cikin iKon Allah tana tashi taji ta take k'afar sai taji Bata jin ciwon komai awurin tace. "Eh anty naji sauk'i". Anty khadija tace . "Masha Allah daughter Allah ya K'ara lafiya Nima bana k'asar ne bamu Dad'e da sauka ba shiyasa tun tuni banzo ba Amma tunda mun dawo soon zaki gammu a kano in Sha Allah". Huyaam tai murmushi tace. "Allah yasa anty sannunku da dawowa". Anty Khadija tace. "Yauwa ashe anyi graduation Kuma?..." Huyaam tace . "Eh munyi". Anty khadija Tace. "Congratulations my dears Wishing you good results". Huyaam tace. "Thank you so much anty inasu siyama?..."anty khadija tace. "yanzun nan ta haura sama". Huyaam tace. "A gaida su".anty khadija tace. "Zasuji in Sha Allah bawa Ammie wayar Huyaam ta Mik'awa Huda wayar tai k'asa da murya tace. "ki kaiwa Ammie". Ta fad'a a hankali.huda ta karb'i wayar ta haura sama da sauri zuwa d'akin Ammie.bayan tafiyar Huda Huyaam ta d'auki wayar ta cigaba da game d'inta...... Sallama akai daga nan kofar falon aka turo k'ofar aka shigo Huyaam ta d'aga kai ta kalli k'ofar har suna had'a Baki wajen ansawa ita da ya Zarah.ikleema da safna ne suka shigo suna murmushi suka k'araso falon kafin su zauna kan kujera tare suka gaida ya zarah.ya Zarah ta Kallesu ta ansa musu sallamar su kafin ta mik'e ta haura sama zuwa d'akinta Dan tasan tunda sukazo Kuma takura Mata zasuyi ba barinta zasuyi tayi karatun ba.huyaam ta ajiye wayar nan gefenta ta Kallesu tana murmushi tace . "Sannunku da zuwa wato sai yau ake Ganinku ko?..."ta fad'a tana hararsu.safna tai murmushi tace . "Kiji fa naga ko washe garin ranar ma munzo duba ki kuma jiya munzo da safe Ammie tace kina bacci". Huyaam ta tab'e Baki tace. "Aishikenan". ikleema ta kalli k'afar ganin Babu bandage d'in tace. "Ikon Allah Kinga Yama cire". Ta fad'a da Mamaki.safna ta kalla itama tace . "Ai kuwa dai Kinga Allah Mai iko wallahi k'afar ta warke Kai Masha Allah Allah ya K'ara lafiya". HUYAAM na murmushi tace. "Ameen" ita da ikleema.huda ce ta sauko falon ganin su safnah ta rik'e hab'a tace . "Kune a gidan yau d'in to sannunku da zuwa". ta fad'a tana k'arasowa falon ta zauna kusa da Huyaam.ikleema tace. "Da Suwa zaki Gani mune mana". Huda ta harareta tace . "Dallah rufe min Baki yaushe kika fara ziyarar da har saki Fad'i haka". Safna tace. "Fad'a mata dai candy da taine yasa ta fara ziyarar.ikleema ta harari safna Huda tai murmushi ta Kalli HUYAAM tace . "Ya zarah tace. "Ki kai mata wayarta zatai Abu da ita".Babu musu HUYAAM ta Mik'e tace musu. "Ina zuwa".daga haka ta nufi sama da sauri.Huda ta Maida hankalinta kansu tace. "Ke Yanaga duk kunyi Wani haske kunyi k'iba " tana kallansu . ikleema tace. "A'a Dama da haskenmu karatu ne yasa kika ga da d'inma munyi duhu. Safna tace . "Fad'a mata ikey hutun Candy ne ya dawo mana da hasken mu Kuma dama can muna dashi yo keko mun samu hutu babu inda muke zuwa daga gida sai islamiya Babu Wani tention na karatu ai dole kiga mun koma haka". Huda ta hararesu ta mike tace. "Ina zuwa bari na kawo muku tunda yau dai kun zama Bak'i agidan".tana fad'ar haka tai hanyar kitchen ikleema ta d'aga murya tace. "In zaki dawo gara ki dawo Dan mun Sha
Chapter 23 · 0% Book details