← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 85

Sashe 19

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ansa mata da Ameen sai Kuma tai saurin cewa. " Zarah ko zaki tafi da muneefa ta kwana agunki ni zan Kwana da Huyaam saboda bazan bari ta kwana ita kad'ai ba".babu musu ya zarah ta ansawa Ammie ta kama hannun muneefa suka fito daga d'akin. muneeb shima Yay wa Ammie sallama ya fita Huda ma taiwa Ammie bayan ta k'ara yiwa HUYAAM ya jiki har ta kai bakin k'ofa Kuma ta dawo tace. "Laa! Ammie na manta d'azu Yaya yak'ira a wayarki yace idan Kun dawo na k'irashi".ta fad'a tana duba wayar Ammie. Ammie tace . "barshi kawai mayi waya da safe idan Allah ya kaimu".har Huda zata aje wayar sai Kuma taga Yana k'ira tace. "Ammie gashi ma yana k'ira".ta fad'a tana mik'awa Ammie wayar Ammie ta karb'a ta kai kunne bayan tayi picking nan Huda ta fita daga d'akin bayan ta kullo Musu k'ofar.... Ammie tai sallama. daga D'aya bangaren Afeef Dake zaune a falonsa yana kallo ya ansa tare da gaida Ammie.. Ammie ta ansa masa nan yake tambayarta jikin Huyaam.ammie batai mamaki ba Dan tasan tunda Huda tace ya k'ira d'azu tofa itace ta fad'a masa nan Ammie ta ansa masa da da sauk'i. Afeef yace. "Allah ya K'ara lafiya".Basu Dad'e suna waya ba ganin yanzu a Nigeria dare yayi yasa yay mata sallama Ammie ta ajiye wayar tana kallon Huyaam Dake Sauke numfashi alamar har tayi bacci ta tashi ta d'auko bargo ta tufa mata ...Babu dad'ewa bayan Ammie ta zauna akai knocking k'ofar ta Bada iznin shigowa .Mai martaba taga ya shigo d'akin bak'insa d'auke da sallama.Ammie ta ansa masa har ya k'arasa shigowa cikin d'akin ya zauna kan sofan Dake d'akin Ammie ta gaidashi ya Ansa idansa yana kan k'afar Huyaam Dake nannad'e da bandage ya sauke numfashi yace. D'azu haidar yace min Kun dawo ya Mai jiki?.."Ammie ta sauke numfashi tace. da sauk'i rankai Dad'e". Mai martaba ya Jin Jina kai yace. "Allah ya K'ara lafiya". Ammie ta ansa da ameen. Ya juyo Yana kallan Ammie yace. "Yau kenan anan mamana zata kwana ko?"ya fad'a Yana yiwa Ammie Wani Irin kallo.Ammie tai murmushi saboda tagane kallan me yake mata kafin tace. "Eh rankai Dad'e saboda ciwon nata banason na barta ita kad'ai ko Kuma ta kwana da Wani kar su fame mata ciwon". Mai martaba ya Jin Jina kai yace. "Hakan ma yayi Allah ya K'ara lafiya". Ammie ta ansa da Ameen Mai martaba Bai Dad'e a d'akin ba yay wa Ammie sallama ya fita daga d'akin gabad'aya .Ammie ta mik'e ganin Mai martaba ya fita ta sauke numfashi ta k'arasa wajen da HUYAAM ke kwance ta gyara mata k'afarta Mai ciwon wacce harta kumbura tai sun tumm ta girgiza kai cikin tausayawa sannan ta shiga toilet danyin wanka Dan Wani Irin zafi take ji......... 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* *Page 1 *Tallah! Tallah!! Tallah!!!* *Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke *Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka *Atamfofi da lesses* *Abaya* *Shadda* *Hand bag* *Shoe* *Veil na manya Dana Yara* *Socks rin hands made d'in nan masu net*. *Hula ta 'yan Gayu* *Siyan D'aya ko sari* *Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki* *Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka* 08135305790 *Sai mun jiku *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 1 __________ Washe gari da safe Huyaam na kwance saman gadon Ammie har wajen k'arfe 9 Bata tashi ba saboda sai bayan sallahn ASuba ma ta samu baccin ya d'auketa Dan daga ita har Ammie Basu Samu sunyi baccin kirki ba a daren jiya, saboda zugin da k'afar Huyaam take mata haka ta farka tsakar dare babu shiri tai ta kuka dole itama Ammie ta tashi take lallashin ta duk da dama bawai baccin take a lokacin sosai ba a lokacin .yanzu haka tana kwancen ta Bud'e idonta ta yunk'ura ta tashe zaune ta Jin jinar da jikinta a fuskar gadon ta lumshe idonta kamar Mai bacci Amma kuma ba baccin take ba.... Ammie ce tashigo d'akin rik'e da mug na tea sai turiri yake sai Huda data ke bayanta rik'e da tray Wanda ke d'auke da breakfast na huyaam.sanye take cikin shigar uniform na islamiya Dan Yanzu suke shirin tafiya.huda ta k'arasa har wajen table d'in Dake tsakiyar d'akin ta ajiye tray d'in kafin ta jawo shi zuwa gaban gadon inda Ammie ta zauna nan gefen gadon.Ammie ta ajiye cup d'in tea d'in tana kallan Huyaam data Bud'e ido tana kallanta kamo hannunta Ammei tai tace . "Kin tashi?..." Huyaam ta gyad'a mata kai Amma batai magana.huda tai murmushi magana ce a Bakinta Amma tai shiru.ita abinda ya Bata mamaki ace yau Huyaam ce ta tashi i wannan lokacin ah lallai yau Babu lafiya sai Kumata furta a fili . "sannu HUYAAM ya jikin?..." Huyaam ta kalleta ta motsa bakinta kad'an tace. "Da sauki...." Huda tace. "Allah ya K'ara lafiya". gyad'a mata kai kawai Huyaam tai. Ammie tace. "Bari na kaiki kiyi brush ko?sai mu dawo kiyi breakfast d'in". HUYAAM ta gyad'a mata kai Huda ta k'araso ta Taya Ammie suka tai makawa Huyaam suka kaita har toilet d'in d'akin Huda ta tatsa mata maclean kan Wani sabon brush dake toilet d'in Ammie ta Mik'a mata Huyaam ta karb'a ta wanke bakinta bayan ta gama suka dawo da ita d'akin. Ammie ta tai Maka mata ta zauna kan gadon itama Ammien ta zauna Bakin gadon kafin ta Kalli Huda tace. "Huda Mik'o tea d'in na Bata Tasha". Babu Musu Huda tai abinda Ammie tace mata ,Ammie ta matsa kusa da Huyaam sannan ta karb'i cup d'in tea d'in da Huda ke Mik'a mata ta kaiwa Huyaam bakinta, sipping hud'u Kawai tai tace ta k'oshi Ammie ta kalli cup d'in tea d'in sannan ta kalli HUYAAM tace cikin lallashi. "Haba Huyaam please ki Bud'e bakin Kisha mana Kinga magani zaki Sha saboda k'afar nan taki tai saurin warkewa uhmm...." Ammie ta fad'a tana kallanta.huyaam ta ya Mutsa fuska kamar zatai kuka tace . "Ammie I have no test in my mouth at All"ta fad'a cikin rawar murya. Ammie ta kwantar da murya tace. "Am sorry dear dama dole Kiji haka da kad'an kad'an bakin zai dawo normal okay please daure Kisha".ta fad'a tana kaiwa cup d'in bakinta da k'yar da k'yar Huyaam ta Bud'e bakin tasha tea d'in nan D'an kad'an ta rage nan Ammie tasa Huda ta zuba mata fargesun kayan ciki sai I Irish da suka soya iya farfesun kawai Ta iya ci shima ba sosai ba Ammie ta Maida plate d'in nan saman tray d'in tana kallan Huda tace. "Mik'o min ledar maganin Huda". Babu musu Huda ta d'auko ledar maganin Dake nan saman drower ta Mik'awa mata.Ammie ta karb'a ta Bud'e ta b'alla ta bawa Huyaam da k'yar Huyaam ta iya had'iye maganin nan tana Yi tana ya Mutsa fuska kamar zatai amai . Ammie tace . "Daurewa zakiyi Huyaam in Sha Allah soon zaki samu lafiya okay". Ya zarah ce tashigo d'akin Bakinta d'auke da sallama tana sanye cikin babban hijab har k'asa na islamiyar sune Hannunta Kuma rik'e Dana muneefa wacce ke sanye cikin shigar uniform na islamiya itama da dukan alamu islamiyar zasu tafi muneefa tace tana kallan Huyaam. "Sannu ya Huyaam".ta fad'a tana zagawa ta D'aya side d'in da HUYAAM take zata haura saman gadon Ammie ta kalleta tace. "A'a Ina zaki muneefa?..."muneefa ta tsaya daga hawa gadon tana Kallan Ammie tace cikin shagwab'a. " zanje naga k'afar ne fa Ammie?.._ Ammie tace. "A'ah! kuma baza ki iya Gani ahaka ba dole sai kin hau gadon salon ki fama mata ciwon oya dawo nan". Ammie Ta fad'a tana nuna mata kusa da ita . Muneefa tai narai narai da ido kamar zatai kuka tace . "Ammie bazan iya Gani a Hakan bafa?..." Ta fad'a tana tura Baki gaba . Ammie ta saki Baki tana kallanta tace. "muneefa ke makauniya ce da zakice bakya Gani ahakan?..." Muneefa ta gyad'a mata kai kamar zatai kuka. ba Ammie hatta Huyaam Saida tai dariya duk da yadda take d'in nan Huda tana dariya ta rik'o muneefa zuwa jikinta tace . "Sorry Auta Ammie ce? Kiyi hak'uri kina gani a haka Aikoh?... muneefa ta gyad'a mata kai idonta sun ciko da k'walla.ya Zarah ta daina murmushin da take tana Kallan HUYAAM tace. "Ya jiki Huyaam?..."Huyaam da itama ta daina dariyar da take Yi ta kalle ya Zarah tace ." Ina Kwana ya Zarah?".ya Zarah tai Murmushi tace. "Lafiya lau Alhamdulillah ya Jikin?...". Huyaam tace. "Da sauk'i Alhamdulillah".ya Zarah ta Jin jina kai kafin tace. "Allah ya sawak'e". Sai Kuma ta Kalli Ammie tace . "Ammie zamu tafi?". Ammie ta kalleta tace. "Allah ya kiyaye?.sai Kuma ta kalli Huda ganin daga ita sai uniform ko hijab d'in ita Bata Saba. "Huda itama ta Kalli jikinta ganin Irin kallon da Ammie take mata taga daga ita sai uniform ko hijab d'in Bata Saba Dan tama manta ma tace . "Laa ya Zarah Dan Allah kijirani nima na Sako hijab D'ina".ta fad'a tana nufar Hanyar k'ofar fita daga d'akin Ammie tace. "Huda" . huda ta ansawa Ammie tana juyo.Ammie tace. " idan kunje ki fad'awa ya USTAZ d'in naku HUYAAM Batada lafiya baza ta samu damar zuwa ba har sai ta samu lafiya". Huda tace . "Eh In Sha Allah zan fad'a". Ammie ta Jin jina kai tace. "kuje Allah ya kiyaye". Huda ta ansa da Ameen ta fita daga d'akin ya Zarah Kuma ta rik'o hannun muneefa suka fita daga d'akin...... Wajen k'arfe goma Saura akai knocking k'ofar d'akin Ammie lokacin har Huyaam ta koma bacci .Ammie data fito daga toilet ta Bada iznin shigowa. Mai martaba ne ya shigo bakinsa d'auke da sallama
Chapter 19 · 0% Book details