← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 85

Sashe 67

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*. *domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka +234 811 190 1302 /09020337676* *Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta* *Sai mun Jiku 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *__NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* My channel link https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y *Bismillahirrahmanirrahim* PAGE 3 ___________ Kwance tashi Babu wuya a wurin Allah,satika suna wucewa Kwanaki suna shud'ewa harya kasan ce yau saura kwanaki biyu kacal bikinsu su ya zulaihat.a Kuma yau da safe Anty khadija ta sauka a cikin palace nan b'angaren Ammie ita da iyalanta gabad'ayansu Wanda suka zo Dan halarta wannan bikin har siyama wacce ta shige cikin su Huyaam ana ta hada_hada tare da ita. yau alhamis da yamma za'ayi cocktail Wanda anan cikin palace d'in za'ayi.sai Kuma gobe Friday idan Allah ya kaimu za'a Yi dinner sai Kuma ranar Saturday da za'ayi d'aurin AUREN.su Huyaam ansha lalle both red and black Wanda ya d'auki fatar ta yay mata mugun kyau ba kad'an ba kamar kisace ta ki gudu haka zakiji saboda yadda lallan ya tsaru ba kad'an ba,Dan saida suka samo k'wararriya wacce ta iya sosai zatai musu Dan wacce taiwa amarya ita tai musu. D'inku nan suma tailor ya gama ya kawo musu har gida d'azu da safe. Yanzu haka k'arfe hud'u da Rabi ne na yamman ranar,Huyaam na zaune kan stol Dake gaban mirror a Wani k'aton bedroom Dake nan gefen d'akinsu anai Mata kwalliya, an gama yiwa ya Zarah da Huda da siyama yanzun ita akayiwa.kallan kayan jikin Huyaam kawai nake wanda shine ankon cocktail partyn,Wani rantsatstsan material ne kalar army green gabad'aya jikin material d'innan stones ne dan sai Wani walwali yeke yana Wani bada different hasken stones d'in,d'inkin ya zauna mata ajikinta das. ga itama kanta kwalliyar da ake mata wani Irin K'ara mata kyau takeyi,Dan Mai kwalliya Ammie ta d'auko musu ta musamman saboda a samu a tsan tsarawa 'yan matan nata kwalliya ta kece raini.kallon Huyaam kawai Mai kwalliyar take bayan ta gama Mata kwalliya da d'aurin head gabad'aya.a fili ta furta "Masha Allah! Kinyi kinyi kyau sosai gimbiya" ta fad'a tana kallan Huyaam.murmushi Huyaam tai mata kafin ta ce "thank you" cikin sanyin muryarta .Huda ce ta turo k'ofar d'akin ta shigo bayan tayi sallama tana Kallan HUYAAM ganin yadda tai kyau ba kad'an ba itama Irin kayan jikin Huyaam d'in ne ajikinta. Mik'awa Huyaam Wani D'an k'aramin box tai Dake hannun ta ce "gashi inji Ammie ta ce a kawo Miki" karb'a Huyaam tai tana kallan box d'in lokaci D'aya tana bud'ewa har ta gama bud'ewa gabad'aya taga wata sabuwar sark'ar gold ce Mai Bala'in tsada da kyau,ta d'aga manyan idanuwanta Wanda suka Sha lashes ta Kalli Huda dasu ta ce "Kinga fa ansa min wata? Huda ta ce "eh! Ammien ta ce ki ajiye agunki gobe saiki sa" Jin jina mata kai Huyaam tai tana kallon Mai kwalliyar ta ce "angama ne? Gyad'a mata kai Mai kwalliyar tai tana cewa "eh angama" tafad'a tana murmushi.mik'ewa Huyaam tai ta nufi k'ofar fi ta ganin har Huda ta fita daga d'akin Mai kwalliyar ta bita da kallo tana Yaba kyawunta bama ita kad'ai ba kusan dukansu ma kyau ne dasu Jin jina kai tai nan ta cigaba da har had'a kayanta... A can Wani k'aton fili dake tsakiyar b'angaren su Ammie da Kuma b'angaren su ikleema yazamto wurin yana tsakiyar b'angaren su Ammie kenan, to anan za'ayi cocktail partyn. anyiwa wajen decorations na musamman ga table da aka jejjera Wanda ko wanne ke d'auke da kujeru Suma duk an musu decorations wajen dai ya tsaru yayi kyau ba kad'an ba. K'arfe biyar da mintuna wurin ya fara cika da Dan dazon mutane 'yan uwa da abokan arzik'i Wanda duk yawancinsu 'yan mata ne tunda wannan partyn na iya Amarene da k'awayensu sai k'ananun su Irin su Huyaam kenan,k'awayen Amaren sun zo duk sun Sha anko anci kwalliya ba kad'an ba.su Huyaam ma sun k'araso wajen su biyar abinsu har siyama da Huda da safna sai ikleema banda Aziza wacce ta ware kanta tak'i shiga cikin su, saima ta samu wasu 'yan uwansu Sa'an ninta ta shige cikinsu. Wuri ya cika mak'il Amare kawai ake jira su Huyaam suna zaune a wurin zamansu da aka tana dar musu.suna nan Zaune babu Dad'ewa Amare suka k'araso wajen partyn take waje ya d'auki Sowa masu pictures suna yi ta ko Ina masu busa sarewa da tamburan sarauta nayi a haka har suka k'arasa wajen zamansu da aka tana da domin su tareda rakiyar k'awayensu .angwaye dai Basu zoba sai gobe idan za'a Yi dinner. Bayan sun zauna nan aka shiga fara gudanar da shagalin partyn cikin nutsuwa Babu Wani Baragada bare hayaniya Abu dai akayi na masu class saboda kowa kika gani a wurin iyayensu suna da kud'i dan kuwa dukansu 'ya'yan manya mutane ne. K'arfe takwas da mintuna aka tashi daga Taron masu tafiya gida kowa ya kama Hanya, wad'an da kuma ba'a garin suke ba sunzo ne har a gama bikin duk sun Wuce masaukinsu. Agajiye Huyaam suka koma part d'insu,cikin sauri ta cire kayan jikinta bayan ta shiga d'akinta ta d'aura towel ta Shige toilet d'in Dake d'akin . fuskarta ta fara wankewa da sabulu Saida ta wanke ta tas sannan tai wanka bayan ta gama ta d'auro alwala ta fito shaf shaf ta Saka wata doguwar riga marar nauyi ta d'auki gogoggen hijab d'inta tasaka ta k'arasa ta d'auko darduma ta shimfid'a nan tsakiyar d'akin ta fara rama sallolin da suke kanta both magrib and isha'i....da daddare wajen k'arfe 10 na dare har Huyaam ta kwanta bacci Dan yau da wuri ta kwanta saboda gajiyar shiga da ficen da Sukayi, ta baro su siyama da Huda dai afalo Dan sunce su ba yanzu zasu kwanta ba,K'ara gyara kwanciyar ta tai nan taji wayarta na ringing,jawo wayar tai tana duba Mai K'iran,tsuke fuska tai lokaci D'aya Ganin Abdallah shattima ne ke K'iranta take ta jaa D'an k'aramin tsaki tai rejecting call d'in ko ajiye wayar bata kai ga Yi ba saiga K'iran Aziz chiroma nan ya shigo wayar tata dafe kanta tai tana jin Wani Irin k'ululun Bak'in ciki Daya to kare mata k'irji lokaci d'aya taji wata zufa na keto Mata ita kan ta shiga uku yanzu ace haka zata tafiyar da rayuwar ta kullum acikin tsoro da fad'uwar gaba akan abinda zai je ya dawo akan masu K'iran nan nata duk ranar da wani ya gani tsakanin yayansu da Ammie.lokaci d'aya wasu zafafan hawayen tausayin kanta suka shiga ziraro mata a fuskarta.nan ta kifa kanta acikin filo tana rare kuka a hankali tana jin wayar nata ringing Amma Bata iya yin picking ba daga k'arshe ma ganin baza'a tab'a hak'ura da K'iran ba yasa ta kashe wayar gabad'aya a fusace ta jefar nan saman gadon ta juya baya ta kwanta tana rera kuka k'asa k'asa a haka har bacci ya d'auketa.... Washe gari da yamma wajen k'arfe biyar da Rabi ana ta shirye shiryen tafiya dinner.kowa ya ci kwalliya daga iyaye har yaran Babu Wanda aka barshi a Baya, bak'i ma da suka zo na kusa Dana nesa both 'yan uwan Hajiya Lubabatu da Hajiya Aysha sai 'yan uwansu baba turaki da Baba wambai Wanda dama su duk family D'aya ne tunda 'yan uwansu ne na jini.anyi general anko na musamman na dinner Wanda aka ware just for iya 'yan uwa da abokan arzik'i ne akayi shi,less ne kowa ya D'inka Mai bala'in tsada.sai ankon dinner Wanda aka ware na musamman na iya Yaran cikin palace d'in daga kan su ya Zarah zuwa su Huyaam iri D'aya akai musu sai sauran Yara kamar su muneefa Suma kalar nasu daban sunyi kyau ba kad'an.nikan an Kon dinner nasu na yau ne ya K'ara d'aukar hankali na Dan kuwa Wani rantsatstsan less material akai musu gabad'ayansu iri D'aya dukan su tun daga yaran har su 'Yan matan irinsu ya Zarah da Salima Dan kuwa komai iri D'aya akai musu kalar ce kawai ta banbanta. Su nasu Huyaam maroon color ne sai nasu muneefa Wanda ya kasance pitch color ne nasun,kayan sunyi musu kyau ba kad'an ba,Dan yau ma dai Mai kwalliyar ta k'ara tsantsara musu dukan su ukun har siyama,dama kwalliyar ta kwana uku Ammie ta ce zatai musu..... Motoci ne kawai ta ko Ina a Cikin harabar palace d'in nan, wasu na shiga wasu na fita,Dan yau ba'a Cikin palace d'in za'ayi dinner ba acan Wani k'aton hole ne Dake cikin government house acan za'a Yi dinner. Duk motar da kika ga dama ita zaki shiga, Dan kuwa motocine wali ishi a harabar palace d'in wasu ma Sabi ne dal aka fito dasu ba'a tab'a hawan suba sai a ranar a Kuma ciki Za'a debi mutane akai su wurin dinner Dan kuwa saboda bikin kawai aka fito dasu.motar Amare kuwa suma duka Sabi dal aka fito dasu aciki za'a kaisu.ana ta wannan had'a hadar Amma Banga su Huyaam ba Dan kuwa naga har an fara d'iban mutane ana tafiya dasu.sai da na d'aga kaina can na hango su suna tsaye daga gefe suna kallan yadda ake ta d'aukar mutane a cikin motocin sai tafiya suke Amma su sunja gefe sun tsaya siyama data gaji da tsayuwar ta Kallesu ta ce "wai mu a wacce motar zamu tafi ne da muka ja muka tsaya anan ne? Ta fad'a tana kallan su Safna ta ce "nima abinda nake tunani kenan, Amma yanzu kuzo muje mu shiga waccen Motar naga kamar Babu kowa aciki" Huda ta ce "to muje" har sun fara tafiya wayar Safna tai k'asa alamar shigowar k'ira.picking tai Ganin Mai K'iran ta ce "hello Yaya" daga D'aya bangaren akai mata magana ta ce "okay Tom muna jiranka" daga haka ta sauke wayar Bayan taji abinda aka fad'a matan tana kallan su Huyaam Wanda suma kallan nata suke tace "Ya lamid'o ne yace mu jira shi zai fito yanzu ya kaimu" ai Huyaam na Jin
Chapter 67 · 0% Book details