Sashe 32
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
welcome". Aziz yace. "Thank you good night". Afeef yace. "Alright thank". Daga haka Aziz ya bar wajen Yana zuwa falo yay wa Ammie sallama Ammie tace masa ya gaida gida bayan ta k'ara Yi masa godiya.. AZIZ CHIROMA na barin falon kamar jira Huda take ta taso daga Inda take da sauri ta dira akan kayan.ta fara bud'ewa D'aya Bayan D'aya Ammie dai sai kallanta take hakama su ya Zarah itadai Huyaam tana zaune daga nan inda take zaune take kallanta.har Huda ta fiddo da wasu dogaraye riguna iri D'aya masu bala'in kyau.rike Baki tai tana kallan kayan da mamaki sai Kuma ta mik'e ta Kara D'aya ajikinta taga tayi mata dai dai nan ta Kalli HUYAAM tace. "Ki taso kiga kayan mana kika Wani zauna kina kallo na?...." Ta fad'a tana Wani zare ido.Huyaam tai murmushi ganin yadda Huda ta Wani susuce akan kayan sai Kuma tace. "Ki dai gama Gani ni idan kika waremun nawa na Gani daga baya". Tana fad'ar haka tana dariya lokaci D'aya..Huda ta tab'e Baki tace. "Ai shikenan". Nan ta cigaba da fiddo da kayan Saida ta gama fiddo su gabad'aya sannan Kuma ta kalli Ammie tace. "Ammie Kinga kayan Daya siyo manan". Ta fad'a cikin farin ciki.itama Ammie tai mamakin wannan uban kayan da aziz ya kawo musu tace. "Masha Allah kungode".ya Zarah ma tace". Masha Allah gaskiya kayan sunyi kyau yayi k'ok'ari sosai" Huda na murmushi tace. "Kinga ya zarah gashi ma harda rings". Jin haka yasa Huyaam tai saurin juyowa Dan tana bala'in son rings sosai tuni ta sauko daga saman kujerar tayo wajen da Huda take tsaye tana kallanta tace. "Muga". Ta fad'a tana Mik'a hannunta. Huda ta Mik'a mata nan HUYAAM ta karb'a tasa a hannunta tace. Wow wallahi yayi kyau sai kace yasan size d'inmu kema Saka muga nakin".ta fad'a tana kallan Huda.Huda ta d'auki nata itama tasa Huy aam tace. "Wallahi kema yayi Miki dai dai size d'inmu yasiyo Kuma yayi Miki kyau wallahi, i like it so much inason ring". ta fad'a da Wani sautin Dayasa Afeef Saida ya juyo ya Kallesu take ya hango ring d'in Dake Hannun HUYAAM Wanda sai jujjuya hannun take Yi ga yadda hasken wutar ya haske shi ya fito sosai yana Wani fidda hasken stone"Muneefa data ke ganin kayan tace "ai Ga Wani ma anan". ta fad'a tana Mik'o musu take Huyaam tai saurin Karb'a tace . "Wow! wannan ai gold ne ya Allah! Gaskiya ya chiroma mun gode Sosai we really appreciate it". Ta fad'a kamar Yana wajen.sai Kuma ta Mik'awa Huda d'ayan bayan ta d'auki nata tace "kema ga naki".Huda ta karb'a tana murmushi tace. "Wallahi ya Aziz Yana da kirki sosai gaskiya mun gode komai yayi kyau". Huyaam na kallan hannunta ganin yadda zoben ya hau hannunta tace. "Kedai bari ai nasamu nayin Gayu kuma". ta fad'a da Wani Irin farin ciki. Afeef ne ya taso daga dining d'in yazo zai wuce zuwa b'angaren su Huyaam na kallansa ta k'arasa gabansa da sauri ta tsaya tana murmushi ta kalleshi tace. "Yaya kaga zoben da ya chiroma ya kawo mana".ta fad'a tana Mik'a masa Hannun nata Wanda ke d'auke da 2 rings.. kallan yatsun nata Afeef yayi na Wani lokaci sai Kuma ya d'ago ya kalleta Ganin yadda take masa murmushi alamun taji dad'i.ya d'auke kansa yace. "Okay na gani bani hanya na wuce".ya fad'a a maganarsa Babu alamun wasa .Huyaam ta Wani tura Baki gaba tana kallansa tace. "Yaya baka Kalli sauran kayan ba kuma Zaka tafi". Ya d'ago ya mata Wani kallo tun kafin yayi magana ta matsa daga gabansa tana murmushi. ya kalli Ammie yace. "Saida safe". Ammie tace . "To Allah ya tashe mu lafiya".ya ansa da ameen Yana yin gaba.huyaam ta koma kusa da ya Zarah tace. "Ya Zarah Kinga zoben Aiya min kyau koh? Tunda yaya Bai fad'a ba". Ya zarah ta Kalli hannun Huyaam taga rings d'in sun K'arawa yatsun nata kyau tace. "Masha Allah yayi kyau sosai akashe lafiya". Tai murmushi tace. "Thanks". Sai kuma ta bar wajen muneefa ta taso tace "muga hannun ya HUYAAM?.." Huyaam na murmushi ta nuna mata hannunta Saida ta kalla sannan ta d'ago ta Kalli HUYAAM da murmushi tace. "Yayi kyau". Huyaam na Maida mata da Martanin murmushin cikin Jin Dad'i tace. "Thank you Auta". Ya Haidar ne yashigo bakinsa d'auke da sallama duka suka ansa masa har ya k'arasa shigowa falon ya Gaida Ammie.Ammie ta ansa masa gabad'ayansu suka shiga Yi Mai Sannu da zuwa Yana kallansu ya ansa musu sai Kuma yaga yadda suka baje kaya anan falon Yana kallansu yace. "Wannan Baja kolin kayan da akai fa".kafin kowa ya bashi ansa Huyaam tazo gabansa da sauri ta tsaya tana murmushi tace. "Kaga Ya chiroma ne ya kawo mana". ta fad'a tana nuna masa Hannunta alamar Yaga zoben.ya haidar ya Kalli hannun Nata ganin yadda rings din sukai mata kyau.yana kallanta yace. "Rings ya kawo muku?...." HUYAAM na murmushi tace. "Ba iya shine ba duka wannan kayan da kake gani shiya kawo mana". Ya haidar ya Jin Jina kai yace. "To Masha Allah". Ya fad'a yana rab'awa ta gefenta ya wuce . Huyaam tace da D'an k'arfi. "bakace yayi min kyau ba". Batare da ya juyo ba yana hayewa stairs yace.." yayi kyau shikenan". Huyaam Ta kad'a kai tana murmushi tace. "Nagode".sai Kuma ta juyo ta k'arasa gaban Ammie tace. "Ammie Yamin kyau ko?...".ta fad'a tana juya hannun Ammie ta kalli hannun tace". Oh ni Maryam yanzu kowa ma sai annunawa wannan zoben?..". Ya zarah tace. "Hmmm HUYAAM ce fa ai har Abba sai ta nunawa da Yana nan.Huyaam ta tura Baki gaba tace. "Ammie kyau fa Yamun". Ammie ta Jin jina kai tace . "To ko Allah ya kyauta". Huyaam tai murmushi tace. "To kuma Bakice Yamin kyau ba". Ta fad'a tana Wani tura baki.Ammie ta sauke numfashi ganin bama ta maganarta take ba ta gyada mata kai tace."to yayi Kyau shikenan". Huyaam tai murmushi tace. " Eh". Ammie tace. "to ku kwashe komai kukai d'aki sai Kuma kuje ku kwanta". Ta fad'a tana mik'ewa suka ansa mata da to" ta kama hannun muneefa suka haura sama ya Zarah ma ta tashi tabi bayan Ammie rik'e da wayarta aka bar su Huyaam da kwashe kayan.... ____________ Bayan fitar Aziz chiroma daga b'angaren Ammie direct Wajen Motar sa ya nufa ya dauk'o sauran kayan Daya siyawa su ikleema da safna da Aziza yayi b'angaren su dashi, anufinsa tunda dare yayi idan ya bawa ikleema nata kayan sai ya Bata nasu Aziza ta kai musu da safe. Da sallama a bakinsa ya shiga falon nasu . Hajiya Lubabatu ya Gani zauna akan kujera da Salima Wacce ke Zaune kusa da Hajiya Lubabatu da dukan alamu shi Suke jira.sauran yaran duk sun shiga d'akinsu sun kwanta bacci ya Bahijja ma tana d'akinta.da k'yar Hajiya Lubabatu ta iya ansa masa sallamar tasa tana juyar da kanta gefe ranta a b'ace .Aziz ya K'arasa shiga cikin falon ya ajiye kayan hannunsa nan tsakiyar falon Yana kallan maman nasu yace. "Ina ikleema?...".ya fad'a Yana zama kan kujerar dake kusa da shi... Hajiya Lubabatu ta juyo tai masa Wani kallo tace. "meye wannan d'in ka Wani ajiye anan". Aziz na sauke numfashi yace". Gifts d'in graduation d'insu ne na Siyo masu sai yau na samu time"..ya fad'a Yana jinginar da kansa Jikin kujerar.... Hajiya Lubabatu tai masa Wani kallo tace.... " To Yanzun Daga Ina kake? nasan ba direct daga wajen siyayyar kake ba". Aziz ya d'ago ya kalleta da mamaki Jin abinda ta fad'a.sai kuma yace "eh saida na fara zuwa wajen Jafar sannan na dawo gidan".... Hajiya Lubabatu tace a fusace. Ba haka nake son jiba daka dawo gidan ina ka fara zuwa kafin kazo nan?..."Aziz ya Kalli maman nasu da mamakin Irin tambayar da take masa kamar Wanda yay mata Wani mugun abun sai kuma ya Sauke idansa k'asa yace. "Eh naje b'angaren Ammie na kaiwa su Huda nasu kayan kafin nazo nan". Hajiya Lubabatu tai masa Wani kallon takaici tace . "Hmm! ai dama na sani daga wajen k'anwar uwar take kake,kaje ka kaso musu mak'udan kud'ad'e ka d'auko saura ka kawo nan ,bama wannan ba shi kuma wannan kayan na nasuwaye da waye?..."Aziz ya sauke numfashi yace. Nasu Ikleema da safna da Aziza". Hajiya Lubabatu tai masa Wani kallo kafin tace. "Me yasa Su d'in Baka kai musu nasun yanzu ba?..." AZIZ yace . Saboda dare yayi shiyasa gobe sai ikleema ta kai musu nasun."Hajiya Lubabatu tace. "Oh! mai zaisa suma Wad'anda ka kaiwan ka bari duk ka had'a ikleema takai musun da safen ko sun fisu Wani matsayi ne a gunka da ka tafi ka kai musun Yanzu da kanka". ta fad'a cikin b'acin Rai.Aziza yace cikin k'osawa da tambayar da maman nasu ke masa "Haba Mama wai Dan Allah Mai kike tunanine akaina? yanzu Dan na Siya musu Abu na kai musu shine abin yimin wannan tambayoyin haba Dan Allah! Yanzu shi Afeef da yake musu siyayyar wacce ta linka tawa sau Dubu Ammie batai k'orafi fa sai ke ko shi kyauta ake basa haba Dan Allah!".ya fad'a k'irjinsa na sama da k'asa Saboda b'acin Rai". Hajiya Lubabatu ta saki Baki da hanci tana kallan Aziz da mamakin abinda yake fad'a mata sai kuma can tace. "Wato ni kake yiwa wannan shouting d'in ko Aziz? To kaje ka tattare dukiyar ma gabad'aya ka kai musu shine zansan Maryam tafini matsayi awurinka".shidai AZIZ huci kawai yakeyi.hajiya Lubabatu tai tsaki ta cigaba tace. "Ya bazan bazan Maka fad'a ba kana can kana almobazzaranci da kud'inka akan Wand'anda Basu ma damu da kai ba". Aziz ya kalleta yace. "Waya fad'a miki wannan maganar na tabbatar baki sani ba zuwa akai aka fad'a miki" Hajiya Lubabatu tai masa Wani kallo tace. "Ni Babu Wanda ya fad'amin kawai jiki nane ya bani".shidai Aziz kallanta kawai yake". Hajiya Lubabatu tace ai kaima kasan Dole zan sani". Aziz yace. Amma mama kema Kinsan ko Mai naiwa 'ya'yan Ammei da Mai martaba kinsan ban biya suba ko? Kiduba kiga Irin wahalar da sukai Dani ko ko Mai martaba,aini d'aukata kece ta kan gaba wajen cewa nai musu Abun duniya Koda ko banyi niyyar yin hakan ba , Amma yau kece kike ganin nayi asara idan nai musu Abu ".