Sashe 3
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta D'aya a duniya.haka aka dinga NEMA Amma ba'a ganta ba zuwa lokacin har gimbiya Aysha ta sare sai kuka take Dak'yar goggoninsu suka kamota suka shigarta d'akinta sai kuka take gwanin ban tausayi suna Bata Baki,gimbiya Bilkisu kuwa zamu iya cewa tafi Mai jegon ma shiga tashin hankali tunda ita ce sanadin komai har Mai martaba yaji shima take ya shiga cikin Tashin hankali Amma Bai nuna ba saiya D'an Dake yana Basu hak'uri da kwantar musu da hankali da cewa yasa ayi bincike in Sha na za'a ga baby Zainab. Anan wannan rugun tsumin a cikin palace anan kuma su safara har sunbar gari tareda baby Zainab sai Wani dogari haladu Wanda sukeyiwa shakundum aiki da yake driving.tafiya sukai ta kusan two hours Dan su kansu basusan Ina suke nufa kawai su burinsu suyi nesa da masarautar sannu su aikata Abinda aka umarcesu Dashi. Basu Tsaya a ko Ina ba sai a jejin can wajen gaba da Abuja iyaka Abuja da minna anan suka tsaya sukai parking motarsu Nan wajen Bakin titi inda babu motsin Wani mahaluk'i ko motoci babu a Hanyar ko tsoro basaji saboda zuciyar su ta riga da ta tsike da Rashin imani.haladu ya juya Yana kallan safara wacce ke rik'e da baby Zainab wacce ke sharar bacci abinta Bai war Allah da Batasan komai ba yace. "Safara gashi munzo saiki cika aiki tunda ni kin hanani Yi ga kwalin nan sai ki jefata aciki mu wullarta cikin dajin nan tun kafin a farga bama cikin masarauta"ya Fad'a Yana kallan safara data k'urawa baby Zainab ido tana kallan ta. Safara Ta d'ago tana sauke numfashi kafin tace . "Ni ansawa ganin haladu gara mu jefata cikin kwalin kawai da ranta basai mun kashe taba. ,Dan na tabbata kafin safiya ta mutu tunda ko sanyin nan da ake na gari zaisa ta mutu banaso mu kasheta ne kar zunubin yayi mana yawa"ta fad'a tana kallan haladu da tun lokacin data fara magana yake kallanta. Haladu yace . "A'a safara yanzu idan aka ga yarinyar kinsan Wallahi hukuncin kisa ne namu". ya fad'a a tsorace. Safara tace . "babu Wanda zai ganta ma haladu kagafa a inda muke jejine iya jeji kana fa ganin ko motoci babu a Hanyar".ta fada tana kallan wajen. Haladu yace. "Shikenan safara tunda kinci haka jefata a kwalin kije ki jefarta".Babu musu safara ta Bud'e kyakkyawan towel d'in da baby Zainab wacce alokacin ta fara mutsu mutsu Amma Hakanan safara rufeta cikin towel d'in ta jefata ta rufeta a cikin kwalin ta fita daga motar . ta fara shiga jejin harta fara nisa ta juya taga haladu na waya ta ajiye baby Zainab ta Bud'e kwalin ta lek'ata Taga ta Bud'e ido tasa hannu abakinta nan da nan tausayinta ya d'arsu azuciyar safara da har zata rufe kwalin sai Kuma ta Bud'e kad'an kafin ta juya tafi tabar wajen tana Jin yadda baby Zainab ta fara k'ananun kuka Amma Bata juyoba ta koma motar. Tana zuwa bayan ta shiga haladu yace. "Ya! kin ajiyetan?..". Safara tace a Sanyaye. "Eh mutafi". Haladu yace. "Anya ko safara shawarar nan taki tayi kuwa? gaskiya nake ganin kamar akwai matsala". Safara tace. "Babu wata matsala haladu mu tafi kawai haladu ya ta-da motar suka bar wajen suka bar baby Zainab daga ita sai ya ubangiji..... __________ Acikin palace kuwa Har k'arfe biyun dare ba'a ga baby Zainab ba nanfa gimbiya Aysha ta sare take ta yanke jiki ta fad'i nan su goggo sukai kanta suna K'iran sunanta, Amma babu inda ya motsi ajikinta take aka k'ira Mai martaba aka fad'a masa.yace za'a turo mota a d'auke ta akaita asibiti. ganin wannan halin da gimbiya Aysha ta shiga yasa itama gimbiya Bilkisu itama ke Neman fad'uwa take itama aka tarota suka zaunar ta a kan sofan Dake d'akin suna Bata hak'uri.gimbiya Bilkisu kuka kawai take kamar ranta zai fita haka takeji Dan Gani take itace silar faruwar komai.Aranar dai mutanan palace sunga tashin hankali ba kad'an ba,Dan sun shiga Irin tashin hankalin da Basu tab'a shiga bane tun atarihin masarautar. Shiyasa a ranar kuwa palace Shiru tai kamar Babu mutane acikinta daga cikin gidan har su kansu masu gidan. 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM (The love story) *Paid book *Free pages* *NA* *___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___* *___(MRS SARAKIES ___* *Bismillahirrahmanirrahim* Page 3 ___________ Washe gari da safe har k'arfe bakwai Saura gimbiya Aysha Bata farka daga doguwar Sumar da tai ba, gabad'aya hankalin su goggo ya gama tashi dashi kansa Mai martaba,iya da bugun zuciyarta ne kawai doctors d'in suka Gane cewa tana a yare .da k'yar da k'yar dai likitocin suka samu nasarar dai dai tuwar numfashinta kafin su d'auki mataki ja gaba .ganin numfashin nata ya dawo normal tana kuma buk'atar hutu yasa sukai mata allurar bacci kafin su fito suna sharce gumin wahala. Gabad'aya daga kan gimbiya Bilkisu zuwa kan su goggoninsu suna nan Cikin asibitin suna zaune a k'ofar d'akin da aka kai gimbiya Aysha kafin daga baya akaisu Wani d'aki Dake cikin asibitin na musamman Dan su huta dan har K'arfe ukun dare a tsaye suke sun kasa sama saboda tashin hankali Dan Suma dai basuyi baccin ba yadda sukaga dare haka sukaga rana a wannan dare. Wajen k'arfe takwas da Rabi Mai martaba yazo asibitin direct d'akin da gimbiya Aysha take ciki akai mishi rakiya .Yana zuwa Yana Bud'e k'ofar d'akin bak'insa d'auke da sallama zuciyarsa na bugawa da halin da zaizo ya tadda matarsa aciki idonsa ya sauka akan gadon adai dai lokacin da gimbiya Aysha ta Bud'e idonta Dan da kuka ma ta farka tana daga kwancen da take.k'arar Bud'e k'ofar da kamashin turaran da taji yasata juyo tana kallon Bakin k'ofar Dak'yar ,ido hud'un da sukai da Mai martaba yasa Bata d'auke idonta akansaba Dan gani take kamar zata ga babyn ta a hannunsa ya kawo mata ita ,tana kallansa harya k'araso cikin d'akin ya zauna nan kan kujerar Dake gaban gadon Yana kallan gimbiya Aysha har lokacin. Gimbiya Aysha ta motsa lips d'inta kad'an tana k'ok'arin dai dai ta kanta tace. "Rankai Dad'e ba'a ga baby naba ko?,ta fad'a tana kallansa .Mai martaba yay jimmm yana kauda kansa daga kallanta Dan Wani Irin rauni yakeji idan yaga matar sa Abar alfaharinsa tana wannan kukan ya Dake ya juyo Yana kallan ta yace cikin nutsuwarsa. "Kiyi hak'uri da abinda zan fad'a Maki fulani!, hak'ik'a wannan abun daya faru muk'addarine daga ubangijinmu ,kiyi hak'urin sanar mikin da Zanyi cewar har yanzu ba'a ga Mai sunan Daada ba , Amma Kuma muna nan muna binciken yadda za'a sameta, yanzu haka kafin na taho saida natara zama na gaggawa a cikin masarautar nan tundaga kan ma'aikata har masu sarauta Dake cikin gidan nan ,nai tambaya ga duk Wanda yasan yaga zuwan matar da akace ta d'auki Mai sunan Daada da kuma fitar da ita daga cikin masarautar nan, Amma kowa yace shi bai ganta ba, sannan nasa a ciki tamin duk Wanda yazo taron sunan nan tun daga kan 'yan gidan nan Wanda suke AURE a waje har Wad'anda ke wajen masarautar nan duk nasa ayi bin cike yanzu haka ana kan binciken so Dan Allah Ina rok'anki da kiyi hak'uri Dan Allah Fulani"ya fad'a cikin lallashi. Tunda ya fara magana gimbiya Aysha take kuka marar sauti tana kallan Mai martaba cikin rawar murya tace. "Yanzu shikenan rankai Dad'e na na rasa baby nah jaririyace fa yaushe aka haifeta yaufa satin ta D'aya a duniya meyasa za'a rabani da ita? Metai musu ko kuma ni Mai nai musu Dana can cancin wannan sakayyar daga wajen su ,Ni Yanzu babbar damuwata shine bansan a Wani Hali take ciki ba zuciyata zafi take mun kamar ta fashe haka nakeji rankai Dad'e"ta fad'a cikin gunjin kuka . Mai martaba ya mik'e daga zaunan da yake cikin nutsuwa ya Tako har zuwa gaban gadon ya d'ago gimbiya Aysha zuwa jikinsa Ya zauna nan akusa da ita tana jikinsa har lokacin. Yay k'asa da murya yace. "Na sani Fulani Amma kiyi hak'uri Wallahi Nima Ina cikin damuwa Amma in Sha Allah za'a ganta"ya fad'a cikin damuwa. Gimbiya Aysha ta d'ago tana kallansa kafin tace cikin Damuwa. "Yanzu Ina sultan yake?Dan Allah ka kula min dashi shima karsu rabani dashi".ta fad'a fuskarta na bayyanar da tsoro. Mai martaba ya shafa kanta yace .. Babu Wanda zai rabaki da sultan Yana tare dasu goggo, please ummu sultan kiyi hak'uri"ya fad'a shima cikin rauni. Gimbiya Aysha kasa shiru tai Dan gabad'aya jinta take kamar ba itaba yanzu Shikenan anrabata da 'yarta wacce take mutuwar so da k'auna, tunda tai ido hud'u da babyn bayan haihuwar ta datai lokaci D'aya taji babyn gama tashiga ranta ashe bama zata rayu da itaba yanzu ko a wani Hali take oho. idan ta tuno da wannan Abu shike sawa taji Wani kunci ya mamaye mata zuciya.knocking k'ofar d'akin da akai yasa Mai martaba matsawa daga kusa da gimbiya Aysha ya koma kan kujerar ya zauna kafin ya Bada iznin shigowa.daya daga cikin doc din suke kula da gimbiya Aysha ce tashigo da sallama abakinta ta gaida Mai martaba cikin ladabi ,Mai martaba ya ansa mata Batare da ya kalleta ba ta sanar dashi tazo duba Jikin gimbiya Aysha ne, take mai marataba ya Bata iznin ,ta tafi ta k'arasa gaban gadon gimbiya Aysha ke zaune akai har lokacin tana sunkuye da kanta k'asa tana share hawayen dayak'i tsaya mata doc tai mata magana cikin ladabi akan tazo duba tane,Da ka gimbiya Aysha ta ansa mata nan doc ta fara duba gimbiya Aysha cikin nutsuwa ganin jinin natama ya sauka yasa ta rubutu Mata sallama tareda prescription d'in da zata siya bayan ta gama ta Kalli Mai martaba da Ladabi tace. "Rankai Dad'e za'a iya sallamarta, yanzu haka ma na rubuta sallamar".ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa. Mai martaba ya jinjina kai kafin yace cikin nutsuwa. "Ok doc bari naje yanzu sai su Bilkisu su shigo su taimaka mata" Yana fadar haka ya Maida dubansa kan gimbiya Aysha, tuni doc d'in ta fice daga d'akinta Mai martaba Yana kallan gimbiya Aysha yace . "Allah ya K'ara lafiya Fulani Dan Allah kada ki k'ara sawa kanki Wata Damuwar please kinsan bazan iya d'auka ba koh?...."ya fad'a Yana mata