Sashe 20
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammie ta ansa masa tana sunkuyar da kanta k'asa har Mai martaba ya k'arasa shigowa cikin d'akin ya zauna nan kan sofan Dake d'akin Ammie ta zauna bakin gadon ta gaida shi duk da sun gaisa da ASuba Mai martaba ya ansa mata Yana kallan Ammie yace . "Ya jikin maman nawa?..."Ammie tace . "da sauk'i Alhamdulillah Bata Dad'e bama da yin breakfast ta kwanta". Huyaam Da har bacci ya fara d'aukarta taji kamar Muryar Abban nasu ta juya Ganin shine da Gaske ta mik'e zaune Dak'yar ta Jin Gina jikin gadon tana murmushi tace. "Sannu da zuwa Abba Ina kwana". Mai martaba yana kallanta yace. "Yauwa mamana kin tashi Lafiya ya jikin naki". Huyaam tana Murmushi tace . "Da Sauk'i Abba".Mai martaba ya Jin Jina kai yace. "Allah ya K'ara lafiya". Huyaam tana Murmushi tace. "Ameen". Sai Kuma yace. "yanzu babu inda yake Miki ciwo?..." Huyaam ta gyad'a masa ka tace. "Eh Babu komai Abba". Mai martaba ya Jin Jina kai yace . "Allah ya K'ara lafiya ". Huyaam ta ansa da Ameen. Sai Kuma ya Kalli Ammie yace. "Babu kumburun yanzu ne?..." Ammie ta kalli k'afar tace. "Eh ba kamar jiya ba dai da sauk'i Yanzun". Mai martaba ya Jin Jina kai yace. " in Sha Allah shima kumburin zai sab'e aide tana Shan magun gunan koh?...." Ammie tace. "Eh tana Sha".Mai martaba yace. "Allah ya sawak'e". Ammie ta ansa da Ameen.babu dad'ewa Mai martaba yay wa Ammie sallama ya nufi k'ofa Ammie tabi bayansa suka fita daga d'akin gabad'aya HUYAAM Kuma ta koma ta kwanta. bayan Ammie ta raka Mai martaba nan Bakin k'ofar falon ta dawo cikin falon baba magajiya ta fito daga cikin din Dake downstairs ta k'araso falon da sauri. "ta zugunna har k'asa ta gaida Ammie.Ammie ta ansa mata da kulawa.baba magajiya tana murmushi tace . "Dama ranki Dad'e nazo ne naji ya Jikin Huyaam d'in?..."Ammie ta tace. "da sauk'i magajiya Alhamdulillah". Baba magajiya tace. "Allah ya Kara lafiya". Ammie ta ansa da Ameen tace.. "Bari naje magajiya kije bari na koma d'akin". Baba magajiya tace. "To shikenan ranki Dad'e afito lafiya". Ammie ta ansa mata daga haka ta haura sama itama Baba magajiya ta mik'e ta shige kitchen d'in tana addu'ar Allah ya bawa Huyaam lafiya..... ____________ Da yamma wajen k'arfe 4:30pm na yamman Ranar fulani Salamatu ta shigo b'angaren Ammie tareda rakiyar hadimanta Wanda suka tsaya Daga nan Bakin k'ofar falon Amma Basu shigo ba suka tsaya suna zaman jiranta. Da sallama fulani Salamatu ta shigo main falorn bata k'arasa shigowa cikin ciki ba sai ta tsaya daga nan k'ofar falon tana sallama cikin shiga ta Alfarma sai Wani walwali takeyi.baba magajiya Dake kitchen ta fito da sauri jin sallama ganin Fulani Salamatu ce yasa ta k'araso falon cikin sauri ta duk'a a gabanta ta sunkuyar da kanta cikin girmamawa tace . "Barka da Zuwa ranki Dad'e". fulani Salamatu ta kalleta da k'yar ta iya ansawa tace. "Kije ki fad'awa uwar d'akin ki Isowa ta".tana fad'ar haka taja bakinta tai shiru.baba magajiya ta k'ara sunkuyar da kanta k'asa tace. "An gama ranki Dad'e".daga haka ta Mik'e ta haura sama zuwa d'akin Ammie Dan sanar mata .babu dad'ewa Ammie ta sauko itama cikin shiga ta Alfarma ta k'araso saukowa daga stairs d'in ta shigo falon tana kallon fulani Salamatu da mamakin Mai ya hanata zama tace. "Sannu da zuwa fulani ki zauna mana".ta fad'a tana murmushi Fulani Salamatu ta k'arasa ta zauna kan kujera tana kallan Ammie .Ammie ta Kara fad'ad'a murmushinta tace. "Barkanmu da yamma Fulani fatan mun yini lafiya?..."babu yabo babu fallasa Fulani Salamatu ta ansawa Ammie kafin tace. "Ya mai Jiki Kuma?..."Ammie tai murmushi tace. "Jiki da sauk'i Alhamdulillah yasu Waleeda?..." Fulani Salamatu tace. "Lafiyansu lau". Ammie tace. "Masha Allah".shiru ne ya biyo Baya harna tsawan 2 minutes Babu Wanda ya K'ara magana acikinsu har baba magajiya ta cikawa Fulani Salamatu gabanta da ruwa fa drink's sai fruits sannan tabar wajen kallo D'aya taiwa kayan ta kauda kanta sai can fulani Salamatu ta mik'e tace. "Bari na tafi ". Ammie ta mik'e tace. " tafiya kuma Fulani ko ruwa fa Baki shaba?..."Fulani Salamatu tace. "Eh Alhamdulillah Nasha ruwa sai anjima". daga haka tai hanyar k'ofar fita".Ammie ta bita da kallo tana mamakin Irin halin fulani Salamatu yadda ta d'auke take mata kallan kishiya har yau Dan ita in ta itane wallahi ba zaman kishi take da Fulani Salamatu ba Amma fulani Salamatu ita ta d'auki zamansu matsayin kishi har ma abun yake damunta Amma ita ko kad'an ba zama kishi take da ita ba.Ammei ta kau da tunaninta ta koma sama wajen HUYAAM...... Wajen k'arfe biyar da Rabi Fulani Salamatu ce zaune acikin Wani d'akinta na musamman Dake nan samanta tana zaune kan kujera ita da Hajiya Lubabatu.hajiya Lubabatu ta numfasa tace. "Ai ni ban d'auka raunin ya kai har haka ba Saida naje na gani yanzu?...." Fulani Salamatu ta tab'e Baki tace. "To ke kin Gani ma ni ko zuwa gun yarinyar banyi ba iya kacina falon uwarta".. Hajiya Lubabatu ta sauke numfashi tace. "Nima abinda yasa naje Dan kada ace agaban 'ya'yan ka akayi kuma sunje sun fad'a Maka Amma banjeba shiyasa najeni". Fulani Salamatu tace. "Kema kenan aini wallahi banyi niyyar zuwa ba Mai martaba ne kawai ya tilasta min zuwa Amma wallahi da Dan kaina ne ni kan banyi niyyar zuwa ba in yaso k'afar ta rub'e". Hajiya Lubabatu tace . "Aikuwa dai k'afa tayi sun tum Baki Gani ba Anya mako k'afar nan zata warke kuwa?...." Fulani Salamatu gyara zama tace. "Dan Allah fa k'awata? Allah yasa ma karta warke ta zauna Ahaka".ta fad'a tana Wani murmushi. Hajiya Lubabatu tai dariya ta Bata hannu suka tafa tace . "Dad'i na Dake k'awata bakida dama". Fulani Salamatu tace . "Dakinsa yadda na tsani yarinyar nan itada da Afeef ke duka yaran ma da bakiyi wannan maganar ba k'awata".Hajiya Lubabatu tace. "yauwa ni kin ma tuna min k'awata" saikuma ta fara kalle kallen d'akin kafin Kuma tai k'asa da murya tace. "Ina fatan dai kin kora wad'an nan munafukan hadiman Baki waje dai ko?..." Fulani Salamatu tace. "Tun yaushe Ai yanzu idan sunga nayi Bak'i ma basa zaman nan can compound suke tafiya". Hajiya Lubabatu tace. "yauwa,to Kinma tuna min Ashe Afeef d'in ya kusan dawowa k'asar nan?..." Tafad'a tana kallan fulani Salamatu. Fulani Salamatu tace with compused. "Afeef d'in?..."Hajiya Lubabatu tace . "Shidai Nima haka naji zancen Yana yawo agidan nan Dan ban tabbatar ba". Fulani Salamatu tace. "Hmm Babu batun Wani tabbatar wa Tunda kika ji ana zancen ai ya tabbata kenan zai dawo d'in,Amma aini ko ubansa Bai fad'a min ba kodan ni bama ya sakoni cikin harkar yaransa yanzu". Hajiya Lubabatu tace. "Aikuwa dai haka naji".. Fulani Salamatu tace. "Aini d'aukata sai bikinsu bahijja zaizo ai". Hajiya Lubabatu tace . "To dai gashi nan idan ma yazo d'in yanzu ya koma ai zai iya dawowar lokacin bikin. nifa k'awata so nake da angama bikin su bahijja so nake afara zancen nasu bikin shida salimata tunda ban samu za'ayi dashi da bahijja ba ai sai ayi dashi da saliman ko?..." Ta fad'a tana kallan fulani Salamatu. Funali Salamatu da tunda ta fara magana take mata Wani kallo sai kuma tai saurin dai dai fuskarta tace. "Indai wannan ne karki damu k'awata wai sau nawa zan fad'a miki aini nai miki ALK'awari Nima indai zaki tayani cikar burina ai Babu damuwa kamar Afeef ya AURI Salima ne". Hajiya Lubabatu tace. "Mai zaina Hana kuwa k'awata Babu abinda zai Hana in Allah ya yarda yanzu dai yaushe ya kamata mu koma gunnan?..." Fulani Salamatu tace. "yanzu baya nan yayi tafiya Amma da Zarar ya dawo zamuje d'in". Hajiya Lubabatu tace. "To shikenan Allah ya kaimu lokacin".sai Kuma ta kalli agogon bangon Dake manne a bangon d'akin Ganin shida na yamman Ranar Saura yasa tace. "Laa!! bari na tafi tun kafin yaran nan su dawo su Tarar mu".ta fad'a tana mik'ewa tsaye itama Fulani Salamatu mik'ewar tai tana cewa. "tafiya Kuma?.." Hajiya Lubabatu tace. "Wallahi sai dai Gani na biyu kuma". Fulani Salamatu ta rakota har k'ofar falon sannan ta koma ciki tana cewa azuciyarta lallai ma matar nan Kina ganin zan bari 'yarki ta AURI Afeef batareda da ni nawa burin ya cikaba ai ko ya cikama bazan tab'a bari 'yarki ta AURI Afeef ba tana fad'ar haka ta shige d'akinta.... Bayan magrib gabad'ayansu su Huda suna zaune a falon k'asa har Ammie Aziza ta shigo falon bakinta d'auke da sallama Ammie ce ta ansa mata Amma su Huda suna kallan itace suka d'auke kansu har ta k'araso cikin falon ta zauna kasan carpet tana gaida Ammie kamar wata miutuniyar kirki. Ammie ta ansa mata da kulawa tace. "Ina su Ramla?.."Aziza tace lafiya lau Ammie sai Kuma tace. "Dama nazo duba Huyaam ne?..." Ta fad'a itama kanta tana Jin nauyin maganar.Ammie ta Kalli Huda tace. "Huda raka Aziza d'aki tazo duba Huyaam ne.". Babu musu Huda ta Mik'e daga zaunan da take Aziza tabi bayanta suka haura sama har zuwa d'akin Ammie suka Tarar da HUYAAM na bacci Aziza ta Kalli k'afar ganin yadda ta kumbura . Amma ko d'ar Bata jiba bare taiwa Huyaam d'in sannu haka nan ta juya ta fita daga d'akin.huda ta kasa hak'uri tabi bayanta a fusace tace. "Aziza Yanzu ko sannu baza kicewa HUYAAM d'inba bayan ke kika ji mata ciwon?...".Batare da Aziza ta juyo ba tace. "Ai na mata".Huda tace. "Haka zakice? to bari Kiji Aiko kinyi na farko kinyi na k'arshe Aziza Dan idan ika K'ara yiwa HUYAAM Irin wannan muguntar wallahi ni da kaina zan rama mata". Aziza batace komai ba ganin sun Sakko kasa tana kallan Ammie tace. "Sai anjima Ammie". Ammie tace . "To sai anjima". Aziza tana fita daga falon Ammie ta juyo tana kallon huda tace. "Mai yasa baza ku ansa mata ba sallamar taba?..."Huda tace. "Ammie dafa muka shiga d'akin ko sannu bataiwa HUYAAM d'in bafa ". Ammie tace. "Da tayi ta kartayi babu abinda zai Sauya 'yar uwarkuce dai bana son Haka".Huda tai shiru batace komai ba Ammie ta mik'e ta haura sama....... 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* *PAGE 1 *Tallah! Tallah!! Tallah!!!* *Ina kuke hajiyoyin gidan