← Book details Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 85

Sashe 66

Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ne haka tun d'azu kowa ya gama Amma ke Baki taso ba?" Ta fad'a tana kallan Huyaam Dake ta faman Shan ice cream.jin muryar Ammie yasa Huyaam tai saurin d'auke robar ice cream d'in ta matsar gefe Dan tasan indai Ammie ta Gani k'wacewa zaitai tana goge bakinta tace "Gani nan fa Ammie" Ammie ta ce "meye kike Wani sid'e Baki haka? ya Zarah ta ce "Ice cream mana aikinsan sai shi tasan indai tazo nan tana Sha sai kin k'wace" Ammie ta Kalli ya Zarah da mamakin abinda ta fad'a ta ce "ice cream Kuma? wai nikan Bata sha d'azu ba?" Ya Zarah ta ce "aikinsan ita ba k'oshi take da ice cream ba saita Sha Wanda yay mata yawa tazo tana Hana mutane bacci a cikin daren nan tana cewa cikinta na ciwo" Ammie ta juya da sauri tana kallan Huyaam ta ce "kawo min nan kafin ki ta-da min da hankali a cikin daren nan" mikewa Huyaam tai tana tura Baki ta fito daga dining d'in ta k'araso har gaban Ammie ta mik'a mata" Karb'a Ammie tai gabad'aya tana kallan robar, wannan sabone ma ta Bud'e take Sha Dan ba na d'azu bane Wanda Tasha ba"da mamaki Ammei ta ce "wato Wani kika d'auko kike sha Bayan Wanda kika Sha d'azu ko?" sunkuyar da kanta k'asa tai tana sosa Kai Dan tasan bata Isa taiwa Ammie k'arya ba. Ammie ta ce "shiyasa d'azu da kowa yaci Abinci Amma ke kika k'i ci Ashe wannan abun kike so Kisha Idan kika faki idona? Huyaam ta girgiza mata kai ta ce "Ammie naci fa" Ammie ta ce "rufe min Baki" sai Kuma ta kalli ya Zarah ta ce "kinsan d'azu a dining Dana ga ta zauna ta nutsu d'auka ta fa ko abincin da Bataci d'azu bane take ci yanzu" ya Zarah ta ce "hmmm da dai ba Huyaam bace ba " Ammie ta sauke numfashi tace "Allah ya kyauta" ta k'ira hadimarta D'aya wacce ta rage Bata koma bangaren su ba tana kitchen tana gyarawa Bayan ta k'araso Ammie ta mik'a mata Ice cream d'in hannunta ta ce ta kai Mata kitchen ta ajiye"karb'a hadimar tai cikin ladabi ta juya ta wuce kitchen d'in, Huyaam ta tura Baki gaba ta zauna kusa da Ammie ta D'ora kanta saman kafadar Ammie.... Wajen k'arfe goma da rabi na dare har Huyaam ta kwanta bacci taji wayarta Dake gefenta tayi k'asa alamar shigowar message, juyawa tai daga kwancen da take ta d'auki wayar tana kallon secreen d'in wayar tare da Bud'e duka message d'in tana karanta contents d'in Bata ko kiftawa,wannan number ce da bata San ko ta waye ba har yau tai mata message d'in, Mai zazzau Maita sak'on kawai take kamar Wanda Bata fahimci Abinda aka rubuta ba "danai tozali Dake yau sai naji duk wata kewar ki da nai ta tsawan watannin da bangan kiba naji wata Irin nutsuwa ta musamman ta saukar min a tareda ni, tafiyar da nai kuwa tare da Dake daga gida har inda muka je muka dawo ji nake Ina ma ace mu Kasance tare da ke a k'ark'ashin inuwa D'aya har Abada? Amma Ina fatan zuwan wannan ranar Ina so ne ki fara arba da kalamai na kafin ki bani damar had'uwa Dake na bayyana miki da kaina ido da ido a matsayin masoya. Please heart beat ki aminta Dani Dan Allah ki soni Koda ko baza kimin Irin soyayyar da nake miki ba.bari na barki haka Karna cika ki da surutu good night bye bye I love you from AMT" iya abinda aka rubuta kenan sai emojies na love... lumshe ido Huyaam tai tana Jin Wani Irin zufa na keto Mata lokaci D'aya a duka jikinta, ita ko waye wannan wanda suka fita dashi d'in tare? Waye Shi,waye yake son K'ara tarwatsa mata zuciya Haka?Abinda ya d'arsu azuciyar ta ne yasa ta kifa kanta tana Hana zuciyar ta gaskata mata wanda take tunani, ita kan ta shiga uku yanzu su uku kenan, Yanzu idan yaya ya sani ko Ammie Mai zata ce musu wallahi babu Mai yadda da ita kome zatai kuwa har gara ma Ammie zata iya fahimtar ta Amma yayansu tasan ko boka da malami zata had'iya bazai tab'a fahimtar taba Wani Irin tashin hankali ne ya K'ara saukar mata yin wannan tunanin da tai take ta fara Jin Jikinta ya fara rawa.tana wannan halin Huda ta tai knocking tare da ta turo k'ofar ta shiga batare da Huyaam ta sani ba Dan tayi nisa a duniyar tunanin Data tafi.Mamaki ya kama Huda ganin yadda HUYAAM ta takure jikinta waje D'aya kamar wacce take Jin sanyi.k'arasawa kusa da gadon Huda tai ta kai hannu ta ta tab'a ta Tana K'iran sannan Huyaam cikin sanyin murya.a firgice Huyaam ta juyo Jin an tab'a ta, Sauke numfashi tai Ganin Huda ce,Huda dai kallan ta take sai Kuma ta sauke numfashi ganin lafiyar Huyaam d'in k'alau Dan d'aukar tama ko Bata da lafiya ne ta ce "ko kin fara bacci ne? Girgiza mata kai Huyaam tai alamar a'a,Huda ta ce tana kallanta "bani blanket d'ina da kika d'auko jiya Kinga nakin kuwa? Mik'a mata Huyaam tai ta ce "eh na gani" karb'a Huda tai kafin tace"meya sameki na ganki Wani Iri?" tun kafin Huda takai k'arshen zancen ta Huyaam ta fashe da Kuka,dan kamar dama jira take a tambayeta damuwarta.nan gaban Huda ya Fad'i ta zaune a bakin gadon ta rik'o HUYAAM tana tambayar ta da lafiya Mai ya sameta? Huyaam Bata ansa ba sai ma kukan da ta dinga rerawa,Huda dai kallan ta Kawai take tana tunanin Mai yasa sameta haka .Saida Huyaam tai Kukan ta Mai isarta sannan ta ta d'ago ta Mik'awa Huda wayarta. Karb'a Huda tai tana Karanta Sak'on Saida ta gama Karantawa tass sannan ta kalli HUYAAM ta ce "waye wannan d'in? Huyaam ta ce cikin sheshshek'ar kuka "wannan d'aya number ne da bansan ko waye ba ya tura min" huda ta k'ara kallan number sannan ta kalli HUYAAM ta ce "na kasa fahimtar inda ya dosa,wai da Kuka fita? To keda waye kuka fitan? Nidai a iya sani na yau da iya ya lamid'o kawai muka fita Bada kowa ba? Gyad'a Mata kai Huyaam tai kafin ta ce cikin rawar murya "Nima haka na gani ai".. Huda ta sauke numfashi ta ce "to iKon Allah waye wannan shi Kuma? Shiru Huyaam tai batai magana ba sai Kuma can ta k'ara fashewa da Kuka tace "na shiga uku Huda wallahi bansan Shiba bansan waye shiba wallahi so suke kawai Yaya ko Ammie wani ya kasheni indai suka sani" saurin toshe mata Baki Huda tai tana girgiza mata kai ta ce "a'a kidai na cewa haka" Huyaam ta k'wace bakinta zatai magana wayar tai k'ara alamar shigowar k'ira, a tare suka kalli wayar kafin Huda ta Mik'a mata ta ce "ana k'iranki" Huyaam ta ce "waye? Huda ta ce "number ne ki karb'a ki duba ki Gani" karb'a Huyaam tai sai Kuma taja tsaki tai rejecting call d'in,Huda tace "waye? Huyaam ta ce "ya Aziz ne mana" tana hararar wayar .sauke numfashi Huda tai tana kallan Huyaam sai Kuma can tai k'asa da murya ta ce "Huyaam kina son Yaya Aziz ne?" ta fad'a da sigar tambaya tana kallan yanayin Huyaam d'in .wata iriyar muguwar harara Huyaam tai mata na ashema bakida hankali.Huda tai murmushi ganin rin hararar da take Mata sai kuma ta ce "Abdallah fa?" Huyaam ta ce a fusace "karki K'ara yimin Irin wannan tambayoyin banaso Huda" Huda tai murmushi ta ce "seriously nake tambayarki Huyaam ta Hakane kad'ai zamu magance Abun" Huyaam ta ce "Allah ya sawak'e ni kaf cikin su Babu Wanda nake so, ke ni Soyayyar ma banji zan iya ba bare Kuma har nai musu Wani gurbi a cikin zuciyata ba.Dan Allah tashi ki tafi bacci nake ji" ta fad'a cikin b'acin Rai.mik'ewa Huda tai da bargon a hannunta tana kallan Huyaam ta ce "zan tafi Amma kafin nan Inaso kiyi nazarin tambayar da nai miki" daga haka ta fice daga d'akin gabad'aya bayan ta kullo mata k'ofar . kallon Huda kawai Huyaam take har ta kai k'arshen zancen ta tafita daga d'akin tana mamakin Mai Huda take nufi da har zata ce tai tunanin tambayar da tai mata? tsaki Huyaam tai tana Jin Wani Irin haushin maganar da Huda tai mata kafin ta d'auki wayar ta kashe gabad'aya ta kwanta tana lumshe ido tunani fal ranta da k'yar ta samu bacci ya d'auketa a haka ....... HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF ABDALLAH SHATTIMA Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar zenith bank Evidence of payment 07066508376 *Yan Niger _zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA 07066508376 *TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!* *Ina kuke manyan mata masu capacity ? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."* *To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* *1,Atamfofi* *2, lesses* *3, Abaya* *4, kayan kwalliya ko Wani iri ne* 5,*D'an kunnaye(jiwelleries)* *6,takalma* *7,hand bag* *8, mayafai* *9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa,
Chapter 66 · 0% Book details