Sashe 68
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haka taji gabanta ya Wani Irin Fad'uwa Dan kuwa haka kawai taji Bata son ace lamid'o ne zai kaisu kwata kwata, duk da kuwa rabon da su sake had'uwa dashi tun ranar daya kaisu wurin tailor nan.suko su Huda ko ajikinsu saima murna da suke tayi Jin Lamid'o ne zai kaisu.Sauke numfashi tai Ganin siyama ta dafa ta ta ce "what happened naga mood d'inki ya sauya?" Murmushin yak'e Huyaam tai mata tace "nothing" adai dai lokacin da mota tai parking a inda suke tsaye ya sauke glass Yana kallansu idan su ya sark'e cikin na juna da Huyaam Amma sai tai saurin d'auke kanta tana mayar wa gefe gaban ta na fad'uwa.Huda tai murmushi ta Kallesu ta ce "shine kuzo mu shiga" ta fad'a tana yin gaba bin Bayan ta sukai siyama na rik'e da Hannun HUYAAM wacce jikinta yake a Sanyaye har suka k'araso wajen motar suka Shiga back seat, wannan Karan Huda ce a front seat.bayan sun shiga lamid'o Yaja Motar suka fita daga cikin palace d'in gabad'aya suka d'au titi sai government house. akan idon Aziz Dake tsaye daga can gefe a harabar gidan komai ya faru ya furzar da huci Mai zafi Yana Jin zuciyar Wani iri shida yake da niyar ya kaisu Amma Kuma sai yaga sun shiga wata motar sauke numfashi yayi nan ya juya koma b'angaren su Dan Hajiya lababatu tace shi zai kaisu........ _____________ Har suka isa government house lamid'o Yay parking a dai dai k'ofar babban hole d'in inda anan ne za'a Yi dinner Huyaam a takure take, Dan kuwa yauma dai lamid'o da Wani irin k'urullan kallo kawai yake binta dashi tunda suka taho Kuma data d'ago da kanta saita ga idonsa Yana kanta.ta ras a ya zatayi. sauke numfashin salama tai Ganin har sun iso hole d'in,ai Yana yin parking da sauri ta b'alle murfin motar ta fita taja gefe ta juya baya ta tsaya tana jiransu Dan dama itace a farko. Godiya sukai masa bayan sun fito daga cikin motar gabad'ayansu ,ansa musu yay da ka kafin ya ce "idan antashi daga dinner sumai magana shi zai Maida su, ansa masa sukai tare da k'ara Yi masa godiya daga haka suka shige cikin hole d'in gabad'aya .suna shiga nan suka tadda wurin acike mak'il da Dan dazon mutane ta ko Ina ga kid'a na tashi gefe guda kuma masu busa sarewa da tamburan sarauta nayi suna tai wa mutane da Ka'nnen amaren kirari.nan suka k'arasa suka nemi wurin zaman suka zauna. Babu dad'ewa saiga su Ammie Suma sun Shigo wurin itada Hajiya Aysha maman amarya da Anty khadija cikin shiga ta Alfarma Ammie tasha alkyabba sai Wani walwali take Yi fuskarta cike da annuri ga hadimarta Mai rik'e mata jaka tana biye da ita a abayanta gabad'aya mutanan wurin mik'ewa sukai alamar girmamawa ganin shigowar matar sarki sai kallonsu suke suna furta masha Allah,masu busa sarewa da tamburan sarauta kuwa sai suka K'ara himma wajen Yi,sai masu kirari Wanda sukai tai wa Ammie da uwar Amarya har suka k'arasa wurin da aka tanadar musu na musamman saboda su, sai sauran k'awayensu Dake biye dasu abayansu da Suma suka samu wuri kusa dana su Ammie suka Zauna.daga bayansu kuma Hajiya Lubabatu da Fulani Salamatu ne Suma suka shigo cikin shiga ta Alfarma Suma sunyi kyau ba kad'an ba nan ma dai kirarin akai tai musu har suka k'arasa wurin zamansu inda yake opposite da na su Ammie suka zauna.babu dad'ewa Amare suka k'araso tareda da angwayensu, Masha Allah haka na furta araina Dan kuwa sunyi kyau ba kad'an ba idan ka kallesu dole ka sake kallansu saboda had'uwar da Sukayi.kirari a kai Tai musu har suka isa wurin zamansu inda aka tanadar musu.nan da nan aka shiga gunadar da shagali dinner anan akai bud'ar kai kowa yazo ya Zuba kud'insa Kuma kudi ba k'ana nan kud'ad'e ba mak'u dai Ammie ma ta zuba nata million uku uku ta zuba wa duka amaren ,ganin Haka yasa da akazo kan Fulani Salamatu itama tasa 4_4 million ita adole saita fi Ammie,oho itakan Ammie Bata ma san tanayi ba domin ita zuciyar ta D'aya tasa kud'in nan. Haka har aka gama taro aka watse aka maida kowa gida kamar yadda aka kawo su, wannan Karan ma dai lamid'o ne ya Maida su Huyaam kamar yadda ya fad'a.aikuwa Yana yin parking a compound Huyaam tai saurin ficewa daga cikin motar ta shige b'angaren su da sauri Batare da ta jira kowa ba,Bata kula ma su siyama ba Dake ta K'iran sunan taba..... Tana shiga b'angaren su falon ta Bud'e ta shiga Babu kowa aciki Hakanan yasa ta K'arasa shiga ciki harta nufi stairs zata haura sama kenan kawai taga Afeef Yana zaune a dining Yana sipping drinks zaro ido tai tare da k'walla wata iriyar K'ara.Afeef da tunda yaji an Bud'e k'ofar falon ya d'aga kansa Yana kallan k'ofar har aka shigo dayaga itace ya zuba mata ido Yana kallanta baya ko kiftawa.daka matsa tsawa yayi ganin tana masa ihu Kuma yaji shi har tsakiyar kansa,Bata saurare Shiba ta cigaba da ihunta ganin yadda take ihu bilhakki da gaskiya zata juya da gudu ta fita daga falon yasa Afeef yay saurin mik'ewa tsaye ya fito daga dining d'in gabad'aya cikin few seconds ya isa gareta ya rik'o ta yana cewa "miye Hakan? kuka kawai Huyaam take tana kallan sa Dan a gaskiya bata yadda Afeef bane tunda babu Wanda ya fad'a mata cewa zai dawo ko Yana hanya Dan ko Ammie bata fad'a musu ba bare su San zai dawo d'in ,Dan ita duk d'aukarta aljanine yayi siffarsa ya bayyana a agareta bashi ba. Ganin Bata daina ihun ba yasa Afeef ya fara kalle kalle a falon Dan baya son Wani daga cikin hadiman gidan su jiyo ihun Huyaam Hakan yasa ya toshe mata Baki ta tafukan Hannunsa ya jata zuwa d'akin su Dake nan downstairs stairs ya rufe k'ofar adai dai lokacin da su Huda suka shigo falon..Yana kallan Huyaam Ganin yadda take zaro ido waje ya K'ara rufe mata Bakin ta yadda Babu damar tai ihun ya K'ara tsuke fuska tana kallan ta yay k'asa da murya yace cikin deep voice d'insa "ihun me kikeyi haka? Girgiza masa kai Huyaam tai har lokacin gaban ta Bai daina fad'uwa ba,Dan ba Bak'ara min tsoro taji ganin sa ba,yana kallan har sannan ya ce "tsoro kika ji Dan kin ganni? Gyad'a masa kai tai da sauri ya ce "relax nine ba Wani ba d'azu na dawo okay" nan ma gyad'a masa kan tai tana kallan sa ya ce "tunda yanzu kinji nine karki sake ki k'ara yimin ihu kinji na fad'a miki" ya fad'a cikin fad'a.daga haka ya sake ta zamewa tai ta zauna a k'asa dab'as shi Kuma Afeef ya Bud'e k'ofar fito daga d'akin gabad'aya bayan ya kullo K'ofar.yana zuwa falon bai Tadda kowa ba Yana dai Jin hayaniyar su Huda da siyama a saman. k'arasawa dining d'in yayi ya d'auki wayoyinsa ya bar wajen ya haura stairs zuwa b'angarensu....sai Da Huyaam tai kusan 20 minutes a inda take zaune bata iya tashi ba saboda shock d'in da ta shiga lokaci D'aya, Dan Bata tab'a tunanin yayansu na hanya ba ko kad'an, mik'ewa tsaye tai a hankali ta fita daga d'akin gabad'aya bayan ta kullo k'ofar. Falon ta fito ganin babu kowa Shi d'in ma baya nan yasa ta haura sama da sauri tana waige waige...... HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF ABDALLAH SHATTIMA Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar zenith bank Evidence of payment 07066508376 *Yan Niger _zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA 07066508376 *TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!* *Ina kuke manyan mata masu capacity ? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."* *To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* *1,Atamfofi* *2, lesses* *3, Abaya* *4, kayan kwalliya ko Wani iri ne* 5,*D'an kunnaye(jiwelleries)* *6,takalma* *7,hand bag* *8, mayafai* *9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*. *domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka +234 811 190 1302 /09020337676* *Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta* *Sai mun Jiku