Sashe 51
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku mutanan arziki. 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* PAGE 3 ____________ *Bayan kwana biyar* Da yamman Ranar Alhamis wajen k'arfe biyar da Rabi su Huyaam sun dawo daga b'angaren su safna ita da huda. tun daga nesa suka hango wata rantsatstsiyar mota ta shigo cikin palace bayan an wangale mata gate d'in.motar da danno kai ta shigo cikin harabar palace d'in.tun daga nesa su Huda ke kallan motar Dan Basu San waye aciki ba. Har motar isa tai parking a parking lot suna tafiya suna kallon motar. Aziz chiroma ne ya fito daga cikin motar sanye yake cikin k'ananun kayan da sukai masa bala'in kyau riga da Wando rigar blue black sai Wandon Daya kasance blue jeans ba k'aramin kyau kayan sukai masa ba tafiya yake cikin nutsuwa kamar ance ya d'aga kansa sukai ido hud'u da Huyaam tareda da Huda wacce tai saurin d'auke kanta Dan har ya kusan cimma masu basu farga ba,ya fara takowa zuwa harabar gidan Cikin saurin da shi kansa Bai San Yana Yi ba saboda yadda zuciyar sa ta harba da ganin Wacce idan ya kalleta a Koda yaushe ko Kuma ya tuna ta Hakan ke faruwa dashi.ganin direct gunsu yake nufowa yasa Huyaam ta damk'e hannun Huda da k'arfi tana K'ara saurin tafiyar ta itama .Huda na Jin yadda HUYAAM ke janta yasa ta kalleta da mamakin Irin wannan saurin da takeyi tace. "Ke saurin me kike haka ne? ki tsaya mugaisa da ya chiroma shine fa yazo kinganshi can". Ta fad'a tana juyawa tana K'ara kallan Aziz chiroma Wanda har ya kusan cimmasu . batareda da Huyaam ta kalleta ba tace suna cigaba da tafiya. "Kinga fa dare nayi kuma kinsan fa Ammie tace mudawo da wuri fa". Huda ta ja burki ta tsaya ta rik'o hannun Huyaam da k'arfi tace. "Dan Allah ki tsaya Kinga fa magana yake mana fa wai Dan Allah Huyaam Mai yasa kike yiwa ya chiroma haka ne ke kwata kwata bakya son sakewa dashi sai kace Wanda ya tab'a miki Wani abun". ta fad'a tana kallan Huyaam.Tsayawa Huyaam tai batareda tasan tayi Hakan ba tana kallan Huda da Mamakin abunda ta fad'a .Batasan Mai yasa ba kwata kwata Batasan taga ta tsaya inuwa D'aya da Aziz chiroma ba, Kuma bawai Wani abun ya tab'a mata ba Amma kuma ko kad'an Bata k'aunar Hakan .zatai wa Huda magana kenan Aziz chiroma ya iso Wajen su ya tsaya Yana murmushi tareda kallansu kafin ya tsaida idonuwansa a kan HUYAAM data Wani tura Baki gaba tana tana sunkuyar da kanta k'asa tana rik'e da Hannun Huda har lokacin...Huda na murmushi tace. "Ya Aziz dama Kaine cikin motar can mukai ta kallo muna tunanin waye Saida ka fito sannan muka ga ashe Kaine". Ta fad'a tana murmushi.Aziz chiroma na murmushi yana Shafa kansa yace. "Nine mana da Baku Gane Motar ba?..." Huda ta D'an Bud'e ido tana kallansa ta girgiza kai tace. "Ko kad'an danni banma tab'a Ganin motar nan agidan nan ba". Yana kad'a key d'in motar Dake hannunsa yace. "Oh! gaskiya ne na tuna baku sanni da motar ba Agidan nan dan yau na fara zuwa da ita da naje bichi na d'auko". Huda na kallonsa tace. "Shiyasa kan Bamu sani ba". Huyaam ce ta D'an kalleshi tace. "Ina wuni". Ta fad'a kamar wacce Batasan yin magana. Aziz na murmushi ya langwab'ar da kansa yana kallanta ya kwai kwayi irin muryarta yace. "Lafiya lau". Mai Huda zatai inba dariya ba itama kanta Huyaam d'in Saida ta D'an murmusa saboda yadda yay maganar. Yace. "Wai Huda Mai naiwa HUYAAM ne da Batasan sakewa Dani ne yanzu?. Ya fad'a Yana kallan Huda Dan jiran ansarta. Huda ta Kalli HUYAAM sannan ta Kalli Aziz tace. "Wallahi ya chiroma Nima bansani ba gata nan ka tambayaeta.." ta fad'a tana kallan Huyaam.Aziz chiroma ya kalli HUYAAM ya D'an duk'o kad'an Yana kallanta kafin yace. "Mai yasa bakyason sakewa dani ne ko dai Wani Abun nai miki?" Huyaam ta girgiza masa kai tana K'ara Damk'e hannun Huda Dake cikin nata.Aziz.ya d'ago Yana sauke ajiyar zuciyar salama yace. "Okay,so please nidai Abinda zan rok'a shine Dan Allah kidaina yimin abinda Kike mun idan kinganni kinji my sister?Dan bana jin dad'in yadda kike min, ko bakya Ganin yadda muke da huda brother and sister ne? Huyaam tai shiru batace komai ba.ya cigaba yace. "Kinyi shiru ko Baki d'auke ni kamar su yarima bane ba? HUYAAM ta girgiza masa kai yace. "So please idan har kin d'auke ni kamar su haidar Dan Allah ki daina guduna kinji?" Nan ma kai kawai Huyaam ta gyad'a masa batai magana ba.Huda ta d'auke kanta daga kallan Huyaam ta Mada kan Aziz chiroma tace. "Kar ka damu Ya chiroma in Sha Allah zata sakene kasan Huyaam d'ince dole Saida lallab'awa". ta fad'a tana kallan Huyaam tareda murmushi.Huyaam ta d'ago ta kalleta tana Maka mata harara.Aziz yay murmushi yace. "Thank You so much sisters". Ya fad'a Yana kallansu.Huda tana murmushi itama tace. "U are welcome".Ganin ana K'iran sallahn magrib yasa yay musu sallama ya juya zai nufi b'angarensu a dai dai lokacin da ya Afeef ya fito daga nasu b'angaren kenan zai tafi masallaci. bayan AZIZ kawai Afeef ya kalla Amma harya ganeshi Ido hud'u sukai dasu HUYAAM yay musu Wani kallo ya k'araso zai wuce su sukai k'asa da kansu suna masa Allah ya kiyaye Amma ko juyowa Baiyi ya kalasu. HUYAAM ta juya tana kallon Huda tace kamar zatai kuka. "kinga abinda kika jawo Mana ko?.." Huda da itama jikinta yay sanyi ganin Irin kallon da Afeef yay musu tace. "Ke naga yasan Yaya Aziz ne babu abinda zai mana fa".. Huyaam ta k'wace hannunta tai saurin shiga b'angaren nasu da sauri Bata kula huda ba Dake tai mata magana akan ta a tsaya ta ba Dan ita hankalinta ya tashi tun gargaad'in da yay musu na kwanaki yana rik'e akanta.huda ta bita Abaya itama jiki babu k'wari Amma Kuma deep down tasan Babu abinda zai musun tunda tasan ai Aziz ne ba Wani ba... K'arfe goma da Rabi na daren ranar ,Mai martaba ne zaune a k'aton falonsa yana kishin gid'e jikin tun tun sarautan Dake jera a k'asan carpet d'in falon.Ammie Kuma tana daga Zaune a gefensa yay shiru Yana sauraranta har ta gama kafin can Kuma ya Sauke numfashi yace. "Tom Babu laifi naji abinda kika fad'a fulani Amma bawai zank'i bane ba Ina tsoron kada suje can ciwon nata ya sake tashi a gidan Khadija ne bawai fata muke ba Amma duba da yadda yake yawan tashin ne nake dubawa". Ammie ta sunkuyar da kanta k'asa tana Jin abinda Mai martaba ya fad'a Dan itama tabbas tayi wannan tunanin duk da tasan Anty khadija zata kula da ita Amma Kuma tana tsoron ace ciwon ya tashi acan duba da yadda anan suke Shan wahala idan suka tasan mata anan d'in.sauke numfashi Ammie tai k'asa da murya tace. "Gaskiya ne ranki Dad'e Nima abinda nake ta tunani kenan tun lokacin da Khadija tai min maganar". Mai martaba ya Sauke numfashi yace. "Bazan iya hanasu zuwa ba Fulani Allah shine Mai iko akan komai idan muka bita da addu'a shikenan sai kigama har suje su dawo baba abinda zai faru". Ammie tace. "Wannan gaskiya ne rankai Dad'e". Mai martaba ya Jin Jina kai yace. "Yaushe zasu tafin?.." Ammie tace. Da nayi tunanin su tafi tareda da Afeef tunda kaga ta Abuja Jirgin nasu zai tashi.." Mai martaba yace. "Okay Babu laifi ranar Monday kenan?.." Ammie tace. "Eh". Yace "Tom Allah ya kaimu" Ammie ta ansa masa da Ameen. Hira suka ci gaba Dayi akan yadda dai idan su Huyaam d'in sun dawo daga Abujan idan komai ya zamana ready kamar yadda suke fata akaita Egypt d'in.... ___________ Ranar Saturday da dayay dai dai da saura wata D'aya da sati D'aya bikin su ya Bahijja aka tashi da shirye shiryen tarb'an Bak'in da zasu kawo kayan lefen ya zulaihat. Kamar dai yadda akai na ya Bahijja to wannan Karan ma dai haka akayi.Dan masu girki aka d'auko na musamman sukai duk Wani nau'i na abinci da snacks kala kala wanda za'a tarb'i Bak'in dashi kusan store guda aka cika da ruwa da drink's kala kala sai kayan snacks d'in Wanda akai raping d'insu da poel paper.komai dai anyi shi yadda ya dace Irin dai na masu dashi kundai Gane ai mutanan arzik'i .bayan sun gama aka sallamesu da kayan abun arzik'i Bandama kud'in aikinsu da aka biya su tun tuni.da farin ciki suka tafi ba kamar yadda suka tafi lokacin da sukai na bahijja ba Dan wannan kulawa aka Basu na musamman.komai ya kammala zuwan Bak'i ne kawai ya rage... K'arfe hud'u da mintuna main falon b'angaren ummi ya cika mak'il da 'yan uwanta da k'awayenta harma da abokan arzik'i haka aka cika falon nan ana zaman jiran zuwan Bak'i kowa kika gani yana cikin shiga ta Alfarma sai Wani walwali sukeyi .wuyansu kuwa sanye yake da gwala gwali wasu kuwa daham ce Wanda kud'i sukai kuka a wajen siyan su.su Hajiya Lubabatu da k'awar ta Fulani Salamatu wacce ke zaune akan kujerar kusa da Ammie wacce aka tana deta saboda su tunda matan sarkie ne dole a Basu wannan girman. itama cikin shiga ta Alfarma take sai Wani walwali kawai takeyi tana wani Shan k'amshi ita a dole matar sarki (uhmm! kodan matar sarkin ce mana ai ba k'arya tai ba).sauran matan Dake falon kuwa duk suna Zaune saman carper ne wasu Kuma saman kujerun... Hud'u da Rabi dai dai Bak'in suka iso gidan bayan an wangale musu gate.haka motocin nan suka danno kai zuwa harabar gidan alaye kusan guda shida kamar Wanda akazo d'aukar Amarya. Bayan sunyi parking a harabar gidan driver's d'in sukai saurin fitowa daga cikin motar suka k'araso suka bud'ewa wad'an da ke bayan motar kafin su matsa baya da sauri cikin girmamawa.. D'aya bayan D'aya haka manyan matan Dake bayan motocin suka shiga fitowa cikin shiga ta Alfarma kowacce Tasha sutura Mai tsadar gaske.tsayawa sukai bayan duk sun gama fitowa Daga cikin motocin.Dana k'irgasu su shida ne Basu da yawa Dan Amota biyu kawai suke. sauran motocin hud'un Kuma kayan lefen