Sashe 72
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ki gabad'aya ba,yanzu dai kiyi hak'uri kiyi ki Bud'e wayar ki zai k'iraki Yanzu in Sha Allah! ,da ya ce na had'u ku a wayata Amma tunda ga wayarki bari na tafi Dan Allah ki kunna taki zance ya k'iraki ta layinki Yanzu" Huyaam ta ce tana girgiza kai "nifa Bazan tab'a picking call d'insa ba" Huda ta kamo hannunta ta ce cikin lallashi "Dan Allah Huyaam ki tausayawa bawan Allah nan tunda har kikaga ya k'irani ya fad'a min wallahi abun ya dameshi ne, ya Aziz Yana mutuwar sonki HUYAAM ke shaida ce, Dan Allah ko baza kiyi magana ba kiyi picking call d'in sa ko zaiji Dad'i Dan Allah Badan niba" huda ta fad'a da sigar rok'o. Huyaam ta girgiza mata kai ta ce "jiya ma Haka Kuka min keda siyama har Saida kuka ja min Yaya ya ganmu,to yau d'inma so kike ya kamani Ina wayar ya kasheni ko ya_ya? gaskiya Huda bazan iya ba kiyi hak'uri wannan Karan bazan tab'a iya bin maganar kiba" ta fad'a tana kauda kanta gefe.Huda dai kallan ta Kawai take sai Kuma can ta ce "Dan Allah fa nace Huyaam, kiyi hak'uri ni wallahi tausayi yake bani shiyasa har nazo nake rok'ar ki wallahi karkiga Irin damuwar D'aya shiga ko ke kikaji sai kin tausaya masa ga magiya da rok'on Daya dinga min akan nazo na Baki hak'uri na taimaka na had'u kuyi magana sannan ki Bud'e wayarki shiyasa Yanzun ma nazo" Huyaam ta kalli Huda zatai magana wayar Huda tai ringing Huda ta kalli wayar sai Kuma ta dawo da kallonta kan Huyaam ta ce cikin sanyin murya "ya Aziz ne Dan Allah ki karb'a" Bata jira cewar taba tai picking ta ce "Hello Ya chiroma gata bari na Bata" daga haka ta Karawa Huyaam wayar kunnenta.uffan Huyaam Bata ce a wayar ba duk da Irin magiyar da Aziz yay tai mata Amma Bata tanka Saba.ita dai Huda kallan HUYAAM kawai take tana mamakin wai yau ya AZIZ ne yake mata magiya tare da ban hak'uri Amma Huyaam ta had'e Rai tak'i yin magana. tana ji yace Mata Dan Allah tai hak'uri ta kunna wayarta zai K'irata anjima, da k'yar ta ansa masa shima sai da huda tai mata magiya da Hannu sannan.godiya ya hau jero Mata kafin ya ce mata zaije masallaci.d'auke kanta tai Jin ya kashe wayar Huda tai murmushi ta ce "thank you so much sisto me bari naje nai sallah Nima" daga haka ta Mik'e.ita dai HUYAAM batace mata komai ba har Huda ta bar d'akin nan itama ta mik'e ta shige toilet d'in Dake d'akin nata Dan d'auro alwala.... Wunin yau haka Huyaam tayi shi a d'aki har dare Koda wasa bata yadda ta Sauko downstairs ba, Ammie data Kasa jurewa ta shigo ta duba ta ganin Lafiyarta lau yasa ta fice daga d'akin..har washe gari Huyaam bata fito ba sai wajen k'arfe hud'u da Rabi na yamma shima ta dalilin a ranar su Anty khadija zasu koma Abuja shiyasa ta fito saboda zasu musu rakiya zuwa airport,kuma da tai Sa'a ma Afeef baya gidan tun bayan Azhar ya fita Kuma har lokacin Bai dawo ba sannan ya Haidar NEMA zai kaisu. A hankali ta sauko downstairs d'in kowa kallanta yake ta Tarar da duka 'yan gidan suna tsaye a falon suna sallama dasu.Anty Khadija na sallama da Ammie Wanda har an Kai musu a kwatunsu zuwa mota.Anty khadija tai murmushi tana kallan Huyaam ta dafa kafad'ar ta ta ce "daughter yau zamu koma gida in Sha Allah" Huyaam tai mata murmushi ta rumgumeta ta ce "we are going miss you mummy" Anty khadija ta d'ago ta ta ce "Nima haka daughter Amma Baga waya nan ba zamu dingayi in Sha Allah" sai Kuma ta Kalli Ammie ta ce "Anty fulani zamu tafi" Ammie ta ce "Allah ya Sauke ku lafiya a gaida Ambassador" Anty khadija ta ce "zaiji in Sha Allah!" daga Haka tabi bayan su HUYAAM da siyama da Huda Wanda har sun fita daga falon gabad'aya... Anty khadija na kallansu su Huyaam Wanda suka rungume siyama bayan sun isa airport d'in da k'yar suka saki juna ganin time na tafiya suka K'ara yiwa Anty khadija sallama ta ansa musu suka tabmna rik'e da Hannun Imaan suka shiga cikin airport d'in.nan suma suka juya suka nufi Wajen motarsu Haka nan suka Rabu Suna kewar Junan su k'afin su shiga mota Su koma gida...... ____________ *Bayan sati D'aya* Da daddare Afeef na zaune a falon Mai mar taba kansa a k'asa Yana yiwa Mai martaba magana cikin ladabi har ya kai k'arshen zancen sa. Mai martaba ya Sauke numfashi bayan ya gama sauraran Afeef kafin ya ce "to Alhamdulillah! yanzu dai ka gama Musu registration din Kenan? Afeef ya ce "eh Abba" Mai martaba ya ce "yaushe zasu fara zuwa Kuma? Afeef ya ce "nan da sati biyu in Sha Allah rankai Dad'e" Mai martaba ya ce "okay ai harma Za'a Kai Huyaam Egypt d'in su dawo kafin su fara zuwa ko? Afeef ya Jin Jina kai ya ce "eh in Sha Allah Abba" Mai martaba ya ce "to masha Allah! Allah yay Maka Albarka" Afeef ya ce "Ameen rankai Dad'e" Mai martaba ya ce "jibi ne tafiyar ko? Afeef ya ce "eh rankai Dad'e jibi ne" Mai martaba ya Jin Jina kai ya ce "Kai kuma yaushe zaka koma Ingiland d'in?" Afeef na Shafa kansa ya ce "nan da one weeks ne in Sha Allah!" Mai martaba ya ce "da kai za'a kai Huyaam Egypt d'in ne ko ya_ya? Afeef ya K'ara sunkuyar da kansa k'asa ya ce "eh haka nake tunani rankai Dad'e" Mai martaba ya Sauke numfashi ya ce "Allah yayi jagora yasa adace ita kuma Allah ya Bata lafiya" Afeef ya ansa da Ameen.daga nan Kuma suka koma hirar company.... Da daddare Wajen k'arfe 2 na dare cikin masarautar zazzau.Razik'a ce tsaye a cikin wannan d'akin inda suke had'uwa ita da maina a duk lokacin da zasu k'ulla duk wani makircinsu da suke k'ullawa a cikin palace d'in. Ta kalli maina Wanda yake ta kai da komowa acikin d'akin duk da duhun dake Dakin Wanda Babu haske ko kad'an, Amma Hakan Bai Hana maina safa da narwar da yake Yi ba,Dan tunda yaji abinda Razik'a ta fad'a ya kasa nutsuwa waje D'aya Sak'awa da kwancewa kawai yake Saida ya maula Dan kansa sannan ya tsaya kusa da Razik'a fuskar sa daf da tata Yana kallanta ya ce "Razik'a kika ce jibi za'a koma da gimbiya Ayush Egypt d'in? Razik'a ta ce "eh Maina jiya Dana shiga dubata naji k'anwar ta Ameenah Suna waya da 'yar uwarta tana fad'a mata" Jin jina kai maina yayi ya ce cikin wata iriyar murya "indai hakane aikinmu a daren gobe zamu aiwatar dashi kenan" Razik'a ta ce "tabbas wannan haka yake" maina yayi Wani murmushi ya ce "shikenan kije kiyi shiri Nima Zanyi nawa kamar yadda mukai wancen Karan haka zamuyi wannan, Amma karki manta da abinda na Baki waccen lokacin" Jin jina masa kai Razik'a tai.Maina ya gyad'a kai ya ce "zan sa abawa gabad'aya dogarayen da bayin Dake b'angaren ta maganin bacci Irin na mutuwar nan yadda zasu kwanta da wuri kuma baza su tab'a farkawa ba sai washe gari,ke Kuma ki biyo ta inda kike biyowa sannan ki fita ta inda kike fitowa zan tsaya a inda nake tsayuwa nake gadinki Ina fatan kin Gane" Razik'a tai Wani murmushi na Ganin burinta na gab da cika ta ce" godiya nake sarkin masarautar zazzau na gobe" wata iriyar dariya Maina ya saki Jin abinda Razik'a ta fad'a, a duk lokacin da zatai masa wannan kirarin wani Irin Dad'i yakeji kamar yayi hauka ya ce "godiya nake sarauniyar masarutar zazzzu ta gobe" itama murmushin tai daga Haka Sukayi sallama suka fito daga cikin d'akin Kowa ya nufi b'angarensa ta boyayyiyar hanyar da suke biyowa a duk lokacin da zasuyi zama Irin wannan..... HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF ABDALLAH SHATTIMA Saura 1 page mu gama free pages.kuyi Maza ku hanzarta ku biya kud'in Karatunku ta wannan account d'in Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar zenith bank Evidence of payment 07066508376 *Yan Niger _zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA 07066508376 *TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!* *Ina kuke manyan mata masu capacity ? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."* *To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* *1,Atamfofi* *2, lesses* *3, Abaya* *4, kayan kwalliya ko Wani iri ne* 5,*D'an kunnaye(jiwelleries)* *6,takalma* *7,hand bag* *8, mayafai* *9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*. *domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka +234 811 190 1302 /09020337676* *Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*