Sashe 58
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shiga motar sukai shiru Babu Wanda yayi magana acikinsu kowa da tunanin da yake.driver ne ya katse musu shirun ta hanyar cewa "Ina zamu yanzu? Duk suka juya suna kallan Huyaam sai Kuma suka ce "mu koma gida kawai"Huyaam ta juya tana kallan su ta ce "Akan Wani dalili zamu koma gida? Huda ta ce "to munga kinyi Shiru ne gabad'aya" HUYAAM ta kalli driver ta ce "Malam ka zagaya Damu gari kafin dare yayi" Babu musu driver ya ansa musu daga haka suka sauya hanya.. _____________ Shiko tunda su Huyaam suka bar wajen ya bisu da kallo baya ko kiftawa har Saida yaga sun shiga motar Sanan ya farga Ganin tafiya zasuyi. juyawa yayi zuwa inda yayi parking motar sa, ya shiga cikin sauri ya ta-da motar yayi reverse yabi bayansu..tafiya kawai yaga sunayi kamar basu san inda zasu Suba, Amma duk da haka baiji ya sareba ko kuma gajiya haka nan yadinga bin bayansu ,daga yaga sunbi ta wannan titin saidai yaga sun b'ulle ta Wani titin abindai ya d'aure masa kai ganin sunyi tafiya ta kusan mintuna 40 gashi har ankusa sallahn magrib Amma Basu je inda zasun ba,Shima Kuma Bai canza ra'ayi akan binsu da yake Yi ba Haka nan ya daure yake bin bayansu...suko su Huyaam suna cikin motar sai zance suke suna tambayar duk inda basu sani ba Wani siyama ta Basu ansa wani Kuma driver ya Basu Dan wannan nishad'in da suka shiga har sun manta da sun Had'u da Wani a wannan wurin. ganin time d'in magrib is approaching yasa suka cewa driver ya juya ya kaisu gida kawai .Babu musu driver ya ansa musu.har lokacin Basu kula da motar Dake bin bayansu ba... tunda yaga sun shigo wannan layin ya daina binsu yayi parking daga gefe yadda baza su tab'a ganin Saba bare har su fahimci Yana binsu. A kofar gidan dayaga motar ta karya Kwana ta tsaya anbud'e mata gate ta Shiga yasa ya Sauke numfashi ganin komai zaizo masa da sauk'i tunda dai har ya Gane inda suke.yay zooming up sannan ya ja motar yay gaba.... Agajiye suka k'arasa shiga cikin falon Imaan ta taho ta rumgume su tanai musu oyoyo Anty khadija Dake zaune falon ta sauke ajiyar zuciyar salama tana kallan su ta ce."Yanzu nake tunanin ku ganin har ana K'iran sallah Baku dawo ba"Huyaam tai murmushi ta ce "mummy ai gashi mun dawo" Anty khadija ta ce "to sannunku da dawowa" k'arasowa sukai har gaban ta sukai hugging d'inta tare da mata barka da gida.ansa musu tai tanai musu barka da zuwa Suma sannan ta ce "zata je tai sallah ne suma su wuce d'aki suje suyi" ansa mata sukai da to sannan suka haura sama... k'arfe 10 da mintuna na dare suna kwance a d'aki hirar inda suka je d'azu da abuwan da suka Gani kawai suketayi Wani suyi dariya Wani Kuma suyi murmushi "Huda Dake rik'e da wayarta tana kallan status ta d'ago ta Kalli HUYAAM ta ce "wai har kinyi status? Huyaam ta ce Tana kallan ta "eh mana ai saima gobe wannan na good night ne kawai nasa ki jira zuwa gobe kiga" Huda ta ce "ah Nima to bari nayi" siyama ta ce "aini tun d'azu Data turamin na D'ora" HUYAAM ta ce "ai Irin wannan ba'a jira da zafi zafi ake dukan k'arfe"siyama tai dariya ta ce "Sosai fa" Huda dai murmushi kawai tai tana latsa wayarta zata D'ora status diny itama ta ce "aiku Baku da dama". Huyaam ta ce "ai Babu d'aga k'afa" siyama ta tab'o Hayaam ta ce "ke mu cigaba da zancenmu" Huyaam ta gyara zamanta nan Suka cigaba da hirar da sukeyi Wanda duk akan inda suka je d'azu..... HUYAAM LAMID'O AZIZ CHIROMA AFEEF Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in 2270127432 Naja'atu umar zenith bank Evidence of payment 07066508376 *Yan Niger _zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA 07066508376 *TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!* *Assalamualaikum warahmatullah* *Ina kuke manyan mata masu capacity ? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."* *To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* *1,Atamfofi* *2, lesses* *3, Abaya* *4, kayan kwalliya ko Wani iri ne* 5,*D'an kunnaye(jiwelleries)* *6,takalma* *7,hand bag* *8, mayafai* *9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*. *domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka +234 811 190 1302 /09020337676* *Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta* *Sai mun Jiku 07066508376________ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD HUYAAM *NA* *__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__* *__(MRS SARAKIES )__* My channel link https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y PAGE 3 ___________ Washe gari da safe wajen k'arfe 10 Saura na safe,fitowar Huyaam daga wanka kenan tana zaune saman stool d'in Dake gaban mirror tana parking gashinta bayan ta gama shafe shafenta ita kad'ai ce a d'akin Dan tashinta daga bacci kenan ta shige toilet tai wanka,su Huda Kuma tun d'azu suka tashi har suka shirya suka fita can main falor suka barta a d'akin.wayar tace dake kan side drawer tai K'ara Alamar shigowar message juya tai ta jawota ta duba, tsaki taja da d'an k'arfi ganin number Da tun washe garin da suka sauka a Abuja kullum da safe sai number tai mata text message na barka da safiya da Kuma kalaman soyayya ,zata aje wayar kenan Wani sak'on ya K'ara shigowa da wata number a again, Bud'e ido tai da mamaki bayan taga different number ne da Wanda yake mata wannan text message d'in karanta contents d'in ta farayi kamar haka "Assalamualaikum warahmatullah. Good morning my princess how are you wake up today.from your lovely, and I love you from all my heart princess.can I call you to introduce my self if you are ready? Am waiting for your answer, till I hear you good bye". iya abinda ya rubuta kenan sai emojies na love Daya tura daga k'arshe,tunani HUYAAM ta farayi na waye yake mata wannan sms d'in Kuma gashi ba mutum D'aya bane bare ta tsaida tunaninta waje D'aya, different number ne kawai ke mata sms d'in,tayi deleting Irin wannan messages d'in sunfi a k'irga tun zuwansu Abuja kullum sai an mata message Irin wannan Tarasa waye yake k'ok'arin sata Adamuwa haka tana zaman_zamanta tsaki taja da k'arfi sannan tai deleting message d'in ta ajiye wayar a nan Saman Gadon tana tura Baki gaba, K'arawa tai gaban wardrobe inda suka jera kayansu aciki ta d'auko riga da Wando na jeans tasa bayan ta saka hula a kanta sannan ta feshe jikinta da turaruka ta d'auki wayarta ta fita daga d'akin zuwa falorn inda su Huda suke bayan ta jawo k'ofar.ta samu su Huda a falon har sun gama breakfast suna ta hira ita da siyama Suna dariya, kallanta sukai ganin sai yanzu ta fito nan suka tsokanar ta, Harar su tai ta kau da kanta tana kallan Anty khadija Data fito daga kitchen ta Kalli HUYAAM ta ce "yanzu na fito nake cewa zan sa siyama taje ta_ta tasoki kiyi breakfast naga Baki fito ba Ashe kin ma tashi" Huyaam ta sunkuyar da kanta k'asa tana murmushi ta risina ta ce "mummy Ina Kwana" Anty khadija ta ce "lafiya lau oya Maza ki k'arasa kiyi breakfast kafin Anty Fulani ta k'ira Dan Kinsan tamin worning akan indinga sa Miki ido kina cin abincin akan time" Huyaam tai murmushi ta Jin jina mata kai sannan ta k'arasa dining d'in.Anty Khadija Kuma ta k'arasa shiga cikin falon tana kallan imaan ta ce ta biyo ta daga haka ta haura sama....Huda ta Kalli HUYAAM Dake zaune saman kujera a falon tana koyawa imaan Wani assignment ta ce "Ana K'iran wayarki fa tun d'azu" d'ago da kanta Huyaam tai daga zaunan da take tana kallan Huda kafin ta ce "waye? Huda ta Kalli wayar sai Kuma ta ce "I don't know" Huyaam ta ce "okay Mik'o min" Mik'a mata wayar Huda tai ta karb'a sai taga number ne ke K'iranta tun bayan data gama breakfast ta dawo falon ta zauna tana gwadawa imaan yadda zatai assignment wannan number ke doka mata k'ira a Kuma time d'in tai picking sai taji muryar namiji ne shiyasa tai saurin kashewa tana mamakin waye?shine Kuma Ba'a fasa kirinta taba haryanzu.harta ta gama ringing ta katse Wani K'iran ya Kara shigowa batai picking ba ta zubawa wayar ido kawai ne tana kallo. Huda dake kallanta ta ce "ba k'iraki ake ba,kiyi picking mana?" Kamar Huyaam baza tai ba sai kuma tai takai kunne tai shiru.daga D'aya bangaren taji wata sassan murya Mai Dad'i da d'aukar Hankali tai mata sallama.nan da nan taji gabanta ya yanke ya Fad'i jin muryar mutumin, ciki sanyin murya ta ansa masa sai Kuma tai saurin cewa "please waye? gyaran murya yayi ya ce cikin nutsuwa "baza ki