Sashe 21
Huyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke *Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka *Atamfofi da lesses* *Abaya* *Shadda* *Hand bag* *Shoe* *Veil na manya Dana Yara* *Socks rin hands made d'in nan masu net*. *Hula ta 'yan Gayu* *Siyan D'aya ko sari* *Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki* *Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka* 08135305790 *Sai mun jiku *Bismillahirrahmanirrahim* __________ Haka Huyaam ta dinga fama da k'afarta har bayan kwana biyu. A wannan lokacin ne Kuma ta samu sauk'i daga zugin da k'afar take mata, duk da tana Shan magun gunan da akai mata prescription Amma sauk'i na Allah ne saboda ba k'aramin rauni Aziza ta ji mata ba a k'afar nan wai a Hakan ma Dan tana samun kulawa sosai..yau Laraba yanzu haka tana zaune a falon downstairs wajen k'arfe biyar da Rabi na yamman Ranar tana Zaune tana Shan iska a nan falon,zaman d'akin ne ta gaji dashi shiyasa tasa Ammie ta kawota ta zaunar da ita. k'afar ma da sauk'i tunda gashi har bandage d'in ya fara d'agowa sama da Kansa alamar dai zai iya fita da kansa tana zaune tana kallo hankalinta gabad'aya Yana kan TV tana kallan Indian series d'in da ake a tashar Bo llywood.knocking d'in k'ofar falon da akai tare da sallama yasa ta d'aga kai tana kallon k'ofar harya Bud'e ya shigo ta Bud'e ido da mamaki take kallansa harya k'araso tsakiyar falon kafin Huyaam ta sauko idonta k'asa daga kallonsa da takeyi ta Dan motsa lips d'inta kad'an tace. "Sannu da zuwa ya chiroma".ta fad'a tana k'ara sunkuyar da kanta k'asa".Aziz chiroma da tun shigowarsa falon da Yay tozali da Huyaam yake murmushi ya zauna nan saman kujerar falon idonsa na kanta har lokacin yace cikin k'asa da murya. "Lafiya lau Huyaam ya kike?..."ya fad'a Yana murmushi. HUYAAM tana wasa da yatsun hannunta tace. "lafiya lau". Yace " Ina Ammie take ? ke bakije islamiyar ba yau?...." Ya fad'a Yana kallanta kamar zai cinye ta . Huyaam tai shiru batai magana ba Yana kallan k'afar ta_ta yace . "Subhanallah"! Meyasa sameki? Dan Daya shigo Bai kula da k'afar ta_taba.."ya fad'a Yana kallan k'afar Huyaam da tausayawa. Kamar Huyaam baza tai magana ba sai Kuma tace. "Ciwo naji". ta fad'a a tak'aice.Aziz chiroma yace. "Garin Yaya Hakan ta faru?..." Ya fad'a da tausayawa.huyaam zatai magana Ammie ta shigo falon, take HUYAAM ta Sauke ajiyar zuciyar salama Dan taji Dad'i da Ammie tazo da Batasan ya zatai ba dama ,duk a takure take jinta zaman nan a Aziz yayi, da zata iya tashi ma da tuni ta tashi ta Bar falon... da murmushi a fuskar Ammie ta k'arasa saukowa stairs d'in tana kallan Aziz tace . "A'ah! WA nake Gani agidan kamar Aziz chiroma". Ammie ta fad'a tana murmushi ta k'arasa shigowa cikin falon ta Zauna nan saman kujera. Aziz Chiroma na murmushi ya zamo daga saman kujerar da yake kai ya gaida Ammie. Ammie na murmushi ta ansa masa tace. "Lafiya lau Alhamdulillah Ya bichin chiroma?..." Aziz Chiroma yay murmushi yace. "lafiya lau Alhamdulillah Ammie ". Ammie tai murmushi tace. "yaushe kazo ka?...." Ya koma kan kujerar ya zauna yace . "Ban Dad'e da zuwa ba d'azu nazo". Ammie tace. "Masha Allah sannu da zuwa,Amma ai zaka mana kwana biyu kafin ka koma ko kuma ma dai ka dawo Kenan?...." Ta fad'a tana kallansa ". Aziz Chiroma ya shafa kansa Yana murmushi yace. "Ai Ammie tunda aka had'ani da wahalar nan kuma shikenan zaman gidan nan yamin wahala kwata kwata bana samun zama". Ammie tace . "Gaskiya ne to Allah ya taimaka yasu fulani Asiya?..." yace. "Lafiyansu lau suna gaida ku...." Ammie tace. "Muna ansawa".Baba magajiya ce ta shigo falon bakinta d'auke da sallama Hannunta rik'e da tray Wanda ta d'orowa Aziz chiroma ruwa da drink's akai ta k'arasa har gabansa ta aje tray d'in nan saman center table d'in sannan ta tsugunna har k'asa ta gaidashi. chiroma ya ansa mata da kulawa baba magajiya ta mik'e ta bar falon. Ammie tana kallan Aziz chiroma tace. "Kasha ruwa chiroma". Aziz chiroma yay murmushi baice komai ba. ita dai HUYAAM tunda ta samu Ammie ta shigo falon idonta Yana kan TV tana kallanta Amma Kuma tana Jin idon Aziz chiroma akanta lokaci lokaci Yana Kallanta. *Waye Aziz chiroma?* A tak'aice. Ai nihin sunansa Abdul Aziz ne shine ake ce masa Aziz. Aziz Chiroma D'a ne ga Hajiya Lubabatu shine D'an ta na fari yayan su bahijja ne Amma ba ubansun D'aya ba uwa kawai suka had'a.ma'ana dai ba baba turaki bane babansa ba kamar yadda yake mahaifin su bahijja.shi Aziz chiroma D'an gidan sarkin bici ne Wanda ya rasu. Dan baba turaki ba'a budurwa ya AURI Hajiya Lubabatu ba,matar sa ta farko rasuwa tai kusan shekararsu biyar da ita to Basu ta'ba haihuwa da ita ba har Allah ya karb'i Ranta bayan gajeriyar jinyan data Sha. to shine bayan kamar shekara Uku da rasuwarta baba turaki ya auri Hajiya Lubabatu sakamakon itama da mijinta sarkin bici na farko daya rasu alokacin shekarar Aziz Wanda ake ce masa chiroma ayanzu D'aya a duniya, to shine bayan tayi idda da kusan shekara D'aya aka had'asu da baba turaki har suka amince da juna sukai AURE. data tare kuma tace zatazo da Aziz chiroma baba turaki Bai Hana taba ya amince mata. da k'yar ma Dangin babansa suka yarda ta taho tashi gidan acewarsu d'ansu bazai zauna zaman agolanci awani gidan ba. A tak'aice dai Saida aka kai ruwa Rana sannan Dangin mijinta suka yarda ta taho da Aziz masarautar kano.anan yay Karatunsa tunda ga nursery, primary,har secondary zuwa tertiary institutions.saida ya girma Kuma sannan suke so su janyeshi ta hanyar bashi sarautar da yake kai ayanzu wacce ba'a Dad'e da yin bikin bashi sarautar ba Amma sarautar an Dad'e da Yi mishi ita tunda dad'ewa bikin nad'a shinne dai ba'ai ba sai kwanan nan wato chiroman bici itace sunan sarautar da aka bashi .tunda aka bashi kuma sai nauyi Yay masa yawa Dan sai yayi wata D'aya baizo kano ba. da baya wuce 2 weeks Baizo ba Amma yanzu sai ya kai wata D'aya Bai zo ba .wannan kenan Ina fatan Mai karatu ya Gane. Aziz chiroma ya mik'e Yana kallan Ammie yace. "Bari naje Ammie". Ammie ta d'aga kai ta kalleshi tace. "tafiya zakai Aziz?..." Aziz yay murmushi yace. "eh Ammie ai Ina nan zan D'anyi kwana biyu kafin na koma in Sha Allah ". Ammie tace. "To shikenan Aziz mungode sosai kahuta gajiya". Yace. "in Sha Allah Ammie". Yana kallan Huyaam yace. "Allah ya K'ara lafiya HUYAAM. HUYAAM ta D'anyi masa murmushi Wanda iya karsa saman lab'b'anta tace cikin zazzak'ar muryarta. "Ameen nagode". ta fad'a a saman lab'b'anta.Aziz ya fita daga falon gabad'aya". Ammie juya tana kallan Huyaam Ganin Yadda mood d'inta ya canza lokaci D'aya tace . "Kina Jin Wani ciwo Yanzu ne Huyaam?..." HUYAAM ta juyo tana kallon Ammie sai Kuma ta girgiza mata kai tace.. "Babu komai Ammie kawai dai k'afar ce take min nauyi". Ammie tace. "Itama Zata daina in Sha Allah indai Kina takawa da kad'an kad'an zata saki gabad'aya". Huyaam ta gyad'a mata kai ta juya ta cigaba da kallanta.Ammie tai Shiru tana kallan Huyaam tunani fall ranta.lokaci D'aya taji Wani Abu ya soki zuciyar ta Mai kama da rauni take ta runtse idonta tana ambatan sunan Allah.takaf cikin yaran nan HUYAAM itace raunin ta itace wacce take jinta aduka sassan jinkinta tana matuk'ar k'aunar Huyaam so bana wasa ba ko kad'an Bata tab'a k'aunar Wani Abu da zai B'ata mata rai ko Kuma ya tab'a lafiyarta wannan ciwon Dake jikinta ma ji take dama ya dawo kanta hawaye ne ya kawo idonta tai saurin gogewa tana dai dai ta fuskarta.... Aziz chiroma na koma b'angarensu ya zauna nan kan D'aya daga cikin kujerun falon ya d'auko wayarsa Yana latsawa the falor was so silent for some minutes.can Hajiya Lubabatu tashigo falon tana kallan Aziz da mamaki tace. "A'ah! kai kuma Ina kaje tun d'azu daga zuwanka harka fita ko zaman kirki bakai ba".ta fad'a tana zama kan kujerar kusa dashi. Aziz ya d'ago da kansa daga latsa wayarsa da yakeyi Yana kallan Hajiya Lubabatu yace. "Daga b'angaren Ammie nake naje gaisheta ne". Take ran Hajiya Lubabatu ya B'aci nan da nan annurin fuskarta ya gushe tana kallan Aziz tace . "B'angaren fulani kuma? Yanzu kai daga zuwan naka har ka kwashi k'afa ka tafi b'angarenta Dan Rashin hankali to uwarke ma ya kaika tukunna". ta fad'a ranta a b'ace. Da mamaki Aziz chiroma ya ajiye wayar Hannunsa Yana kallan maman nasu Jin abinda ta fad'a yay k'asa da murya yace. "Haba mamah?yanzu Dan naje b'angaren Ammie na gaisheta shine zakice Rashin hankali?..."Hajiya Lubabatu tace . "To ai Gani nai ko ni uwarka gaisawa kawai mukai ka fita daga nan kitchen fa na shiga zan kawo Maka abinci shine na dawo na Tarar ka fita kabar falon ko gaisuwar kirki bamu yiba kawai sai dawowa nai naga baka nan". Aziz yay k'asa da murya yace . "To ai gashi Yanzu na dawo Mama". Hajiya Lubabatu tace. "To ga abinci can a dining na kawo Maka kaje kaci". Aziz Chiroma Yace . "Zanci idan nai sallahn magrib".Hajiya Lubabatu tai shiru tana kallan TV ranta a had'e Jin abinda Aziz ya fad'a.shiko Aziz ganin haka yasa ya d'auki wayarsa ya cigaba da abinda yakeyi can Hajiya Lubabatu ta mik'e tace. "Ina zuwa". daga haka ta shige D'aki Aziz ya bita da kallo kafin ya d'auke kansa ya dawo dashi kan screen d'in wayar tasa can Kuma sai ya mik'e Yana zura wayar a aljihunsa ganin time d'in sallah ya kawo kai harma ana K'iran sallahn ya fice daga falon gabad'aya ya nufi masallacin cikin palace